Shin za a ci gaba da tsare El-Rufai har watan Afrilu, me doka ta ce?

Asalin hoton, Kaduna State Government
- Marubuci, Ibrahim Yusuf Mohammed
- Aiko rahoto daga, BBC Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya shafe sama da kwana 10 a hannun hukumomin Najeriya.
A ranar 16 ga watan Fabarairu ne El-Rufai, bisa raɗin kansa ya je ofishin hukumar yaƙi da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), domin amsa gayyatar da hukumar ta yi masa.
Tun a farko hukumar EFCC ta tsare shi har zuwa daren Laraba 18 ga watan Fabrairu kafin daga baya aka miƙa shi hannun hukumar yaƙi da almundahana da dukiyar al'umma ta Najeriya (ICPC), inda tun daga wancan lokaci har yanzu ba a ƙara jin ɗuriyarsa ba.
Ko a ranar Laraba da hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya DSS ta gurfanar da tsohon gwamnan a kotu, ba a ga Malam El-Rufain ba, kasancewar hukumar ICPC ba ta kai shi kotun ba.
A ranar Laraba babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage ci gaba da sauraron karar da hukumar tsaron ta DSS ta shigar da El-Rufai game da zargin satar sauraron wayar mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Nuhu Ribadu.
Kotun ta ki duba bukatar bayar da belin tsohon gwamnan duk da bukatar hakan daga lauyansa Oluwole Iyamu. Lauyan hukumar tsaro ta DSS Oluwole Aladedoye ne ya ce bai kamata a duba batun beli ba kasancewar ba a riga an fara sauraron karar gadan-gadan ba, inda kuma mai shari’a Joyce Abdulmalik ta amince da hakan.
Ya zuwa ranar Litinin 23 ga watan Fabarairu, mai magana da yawun tsohon gwamnan Muyiwa Adekeye ya wallafa wani bayani a shafinsa na X, inda yake cewa "hukumar ICPC ba ta ce wa lauyoyinsa uffan ba game da batun neman beli, sannan hukumar ba ta nuna wa lauyoyin wata takardar neman ci gaba da tsare shi fiye da awa 48 da doka ta amince ba".
Baya ga haka, mashahuran mutane, kamar tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar sun tsoma baki, inda suka buƙaci gwamnati ta yi bayani game da halin da El-Rufai ke ciki, yayin da wasu kuma suka buƙaci a bi doka a batun na tsohon gwamnan.
Me dokar Najeriya ta ce kan wa'adin da hukumomi za su iya tsare mutumin da ake bincike ba tare da gurfanar da shi ko kuma an bayar da belinsa ba?
Matsayar kundin tsarin mulki kan tsare wanda ake binicike
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowane ɗan ƙasa ƴancin rayuwa da walwala ba tare da wani tarnaƙi ba, kamar yadda masanin shari'a a Najeriya Yusuf Adamu Kaile ya shaida wa BBC.
Lauyan mai zaman kansa ya ce idan har aka keta wannan ƴanci da ɗan kasa ke da su, za a iya kai wa wani mataki da za a iya yin watsi da batun laifin da ake tuhumarsa da shi a koma kan batun take haƙƙinsa.
''Duk wanda ake zargi da aikata wani laifi, da zaran an kama shi, aka tsare shi a ƙarkashin sashe na 31, da kuma sashe na 35(4) na kundin tsarin mulkin Najeriya an ce a kai mutum kotu cikin sa'o'i 24 ko kuma awa 48 idan babu kotu a kusa, idan har aka tsare mutum ya wuce wannan wa'adin an riga an take masa haƙƙinsa na samun ingantaciyar shari'a,'' in ji shi.
Masanin ya ƙara da cewa idan har daga baya aka samu cewa wannan mutumin ba shi da laifi, dole a fara batun yadda za a yi saka masa ko kuma a biya shi diyya. Saboda a cewarsa duk wanda aka tsare ba bisa ƙa'ida ba, ya cancanci a biya shi diyyar tsare shi da aka yi.
Barista Yusuf ya bayyana cewa babu wata hujja da hukuma za ta iya bayarwa na riƙe mutum ya wuce wa'adin da doka ta tanada inda ya ce : ''babu wani dalilin riƙe mutum ba bisa ƙa'ida ba, domin idan ma ba a gama bincike ba ne, sai an kai mutum kotu wadda ita ce za ta iya bayar da damar a ci gaba da riƙe mutum abin da ake kira 'remand order'".
Masanin shari'ar ya bayyana cewa duk wani abu da ba haka, to ya saɓa wa doka, kuma tsawaita tsare mutum fiye da lokacin da kundin tsarin mulki ya gindaya shi ne a turance ake kira "unlawful detention".
Me zai faru idan aka tsare mutum fiye da ƙa'ida?
Yusuf Kaile ya bayyana cewa duk wani lamari da aka samu da ya kai ga keta haƙƙin duk wani ɗan ƙasa, akwai dama da yake da ita ta ƙalubalantar hukumomin da suka yi sanadiyyar "take haƙƙin nasa da aka yi". Inda ya ƙara da cewa "za a kai matakin da za a daina maganar laifin da ake tuhumarsa da aikatawa a koma kan batun take masa haƙƙi da aka yi".
Amma masanin ya jaddada cewa a gaban kotu ne kaɗai mutum zai iya zuwa domin a ƙwato masa ƴancinsa.
''Kotu ce kaɗai ke da hurumin da za ta saurare ka idan aka yi maka irin wannan laifin, saboda haka ita ce kaɗai za a iya tunkara domin ta ƙwato wa duk wanda aka zalunta ƴancinsa.
Waɗanne laifuka ake tuhumar El-rufa'i da aikatawa?
Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya, DSS ce ta kai ƙarar Nasir El-Rufai a gaban kotu, bayan wata tattaunawa da ya yi da kafar talabijin ta Arise, inda a ciki ya ambaci cewar an saurari wayar da mai bai wa shugaban ƙasa shawara ke yi, inda a ciki ya bayar da izinin kama shi.
Tuhuma ta farko: "Malam Nasir El Rufa'i, a ranar 13 ga Fabrairu, 2026, a matsayin bako a shirin gidan talabijin na Arise TV da ke Abuja, ka yi iƙirarin cewa ce da kai da wasu abokan tarayyarka, kun yi kutse ba bisa ƙa'ida ba, a layin wayar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, inda ku ka aikata laifi da ya saɓawa sashe na 12 (1) na dokokin da suka shafi laifukan Intanet, da aka yi wa gyran fuska a 2024.''
Tuhuma ta biyu: "Kai, Malam Nasir El Rufa'i, a ranar 13 ga Fabrairu, 2026, a matsayin bako a shirin gidan talbijin na Arise TV a Abuja, ka ce akwai sanayya da kuma alaƙa tsakaninka da wani mutum, wanda ya yi kutse a layin wayar tarho na Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Nuhu Ribadu, wanda hakan kke nufin ka aikata laifi a ƙarƙashin sashe na 27 (b) na laifukan da suka shafi Intanet wadda aka yi wa gyaran fuska a 2024.''
Tuhuma ta uku: "Kai, Mallam Nasir El Rufa'i da waɗansu mutane da har yanzuu ba a san inda suke ba, a cikin shekarar 2026 a Abuja, kun yi amfani da na'urorin da ke yin illa ga lafiyar jama'a da tsaron ƙasa da kuma sanya fargabar rashin tsaro a zukatan ƴan Najeriya ta hanyar yin kutse a layin wayar tarho na mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkaokin tsaro, Nuhu Ribadu, kuma ka amsa cewa ka yi hakan a shirin gidan talabijin na Arise TV a Abuja a ranar 13 ga watan fabrairu 2026, kuma hakan na nufin kun aikata laifi a ƙarƙashin sashe na 131 (2) Dokar Sadarwa ta Najeriya 2003."











