Abin da muka sani kan jagororin adawa da ke ƙoƙarin haɗakar kayar da Tinubu

Asalin hoton, Social Media
Wasu jiga-jigan 'yan hamayya a Najeriya, ƙarƙashin inuwar ƙungiyar hadaƙa ta Nigeria National Coalition Group (NNCG), na ƙoƙarin tabbatar da wata haɗaka mai ƙarfi da nufin kawar da gwamnatin APC ƙarƙashin Bola Tinubu.
Tun a farkon shekarar nan ne ƴan mahayyar suka fara tunanin kafa wata haɗaka domin cimma wannan ƙudiri nasu.
Ƴan hamayyar sun samar da wata ƙungiyar haɗaƙa da aka yi wa suna ''All Democratic Alliance'' (ADA), wadda suka aike wa hukumar zaɓen ƙasar da nufin yi mata rajista don zama jam'iyyar siyasa.
Wasiƙar wadda suka aika zuwa ga shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a ranar 19 ga watan Yuni, shugaban ADA na ƙasa Cif Akin Ricketts da sakataren riƙo Abdullahi Musa Elayo ne suka sanya mata hannu, sannan INEC ta karɓa a ranar 20 ga Yunin.
Ƙawancen haɗakar na ƙunshe da jiga-jigan hamayya a fagen siyasar ƙasar, da suka fito daga ɓangarorin ƙasar daban-daban daga mabambantan addinai.
Wannan ne ma dalilin da ya sa wasu ke ganin haɗakar za ta yi ƙarfi, kasancewar tana da wakilci a sassan daban-daban na ƙasar.
Ƴansiyasa ne da a baya suka riƙe manyan muƙamai a baya, kuma har yanzu suke da tasiri a fagen siyasar ƙasar.
Manyan jiga-jigan da ake gani cikin wannan sabuwar tafiya sun haɗa da:
Atiku Abubakar

Jagoran adawar ƙasar a baya ya sha yin takarar shugaban ƙasa, kuma a 2023 shi ne ya zo na biyu bayan da ya samu ƙuri'a kusan miliyan bakwai.
Atiku wanda a yanzu ɗan jam'iyyar PDP ne ya kasance jigo a siyasar Najeriya, tun lokacin da ya zama mataimakin shugaban ƙasa a 1999 zuwa 2007.
Ɗan siyasar - wanda Bafulatani ne daga jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya -ana yi masa kallon ɗaya daga cikin mafiya tasiri a fagen siyasar Najeriya.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar na daga cikin fitattun mutanen da suka ƙulla haɗakar da ta haifar da jam'iyyar APC a 2014, da ta yi nasarar ƙwace mulki a hannun PDP a 2015.
A yanzu dai jam'iyyar PDP na da gwamnoni 10 a faɗin Najeriya, kuma kodayake babu gwamnan da ya bayyana bin Atiku zuwa sabuwar haɗakar, ana ganin ficewar tasa za ta sa wasu gwamnonin su bi shi.
Peter Obi

Asalin hoton, Peter Obi
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar LP, na daga cikin mutane na gaba-gaba a kafa sabuwar tafiyar ta ADA.
Peter Obi - wanda tsohon gwamnan jihar Anambra ne har sau takwas - ya kasance na uku a zaɓen shugaban ƙasar da ta gabata a 2023, inda ya samu ƙuri'a fiye da miliyan shida.
Mista Obi - wanda ɗan ƙabilar Igbo ne daga kudu maso gabashin Najeriya - na da farin jini musamman tsakanin ƴanƙabilarsa.
Lamarin da ya sa jam'iyyarsa ta LP ta samu nasara a jihohi 12, ciki har da Legas da da Abuja a zaɓen shugaban ƙasar na 2023.
Jam'iyyarsa ta LP na da gwamnan guda a jihar Abia, kuma ana ganin wataƙila ya bi shi cikin sabuwar haɗakar.
Nasir El-Rufai

A watan Maris da ya gabata ne El-Rufai ya bayyana ficewa daga jam'iyyar APC tare da komawa SDP.
Nasir El-Rufai ya kasance ministan Abuja tsakanin 2003 zuwa 2007, kafin ya zama gwamnan jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin ƙasar, har wa'adi biyu tsakanin 2015 zuwa 2023.
A kakar zaɓen 2023, fitaccen ɗan siyasar - wanda Bahaushe ne - ya kasance na gaba-gaba wajen goyon bayan Bola Tinubu na APC.
To sai dai bayan lashe zaɓen Tinubu ɓaraka ta kunno kai tsakaninsa da El-Rufai bayan da majalisar dattawa ta ƙi amincewa da tantance shi domin ba shi muƙamin minista a gwamnatin.
Rotimi Amaechi

Ya kasance tsohon gwamnan jihar Rivers mai arzikin mai fetur da ke yankin kudu maso kudancin ƙasar daga 2007 zuwa 2015.
Bayan kammala wa'adinsa a matsayin gwamnan jihar Rivers, tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya naɗa shi ministan sufuri na tsawon shekara takwas daga 2015 zuwa 2023.
A 2022 ya bayyani anisarya ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, to amma ya sha kaye a hannun Tinubu a zaɓen fitar da gwani.
A wata hira da ya yi da BBC a baya-bayan nan, tsohon ministan ya ce a shirye yake domin shiga duk wata haɗakar da za ta kawar da gwamnatin Tinubu.
Rauf Aregbesola

Asalin hoton, Rauf Aregbesola
Rauf Aregbesola ya taɓa riƙe muƙamin gwamnan jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya, har tsawon wa'adi biyu daga 2010 zuwa 2018.
A shekarar 2019 tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya naɗa shi, muƙamin ministan harkokin cikin, muƙamin da ya riƙe har 2023.
Aregbesola Bayarabe ne da ya fito daga yankin kudu maso yammacin Najeriya.
A farkon shekarar nan ne Rauf Aregbesola ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar APC.
David Mark
David Mark ɗan asalin jihar Benue - wanda tsohon jami'in soji ne- ya taɓa zama gwamnan mulkin soji na jihar Neja daga 1984 zuwa 1986.
Ya kuma riƙe muƙamin ministan sadarwa kafin ya zama ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Benue ta Kudu.
Shi ne shugaban majalisar dattawa mafi jimawa a muƙamin, bayan jagorantar majalisar na tsawon wa'adi biyu (shekara takwas) daga 2007 zuwa 2015.
Ya kasance ɗan ƙabilar Idoma daga yankin arewa ta tsakiyar Najeriya.











