Yadda mai hawa shafukan sada zumunta zai kare mutuncin azuminsa

Mace riƙe da waya

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Shiga shafukan sada zumunta ya zamo wani ɓangare na rayuwarmu. Sauyin zamani ya sanya kusan kowa a wannan zamani yana amfani da aƙalla daya daga cikin shafukan sada zumunta.

Duk da cewa akwai waɗanda suke iya hana kansu amfani da shafukan a lokacin Ramadana, domin mayar da hankali kan ibada, amma akasarin mutane na ci gaba da amfani da shafukan, ko dai domin gudanar da sauran al'amuran rayuwa ko kuma saboda sabo.

Sai dai Malam Abu Jabir Abdullah, wanda malamin addinin Musulunci ne a Najeriya ya ce "Watan Ramadana lokaci ne mai matuƙar tsada, wanda ba a son mutum ya ɓata lokacinsa" wajen ayyuka marasa amfani.

Malamin Addini

Ya bayyana cewa akwai abubuwa da dama da mutane kan yi a lokacin azumin wanda yakan rage musu ladan azumin da suke yi. "Abin da Allah ya hana mu yi kafin Ramadana, idan muka yi shi lokacin azumi, ƙila ba zai ɓata mana azumin ba, amma zai rage mana ladar azumin, ko ma ya hana samun ladar baki ɗaya," in ji Abu Jabir.

Malamin ya bayyana daya daga cikin manyan abubuwan da za su rage wa mai azumi lada:

Kallon haram:

Idan mutum yana azumi cikin watan Ramadana sai ya je soshiyal midiya yana kallon haramun, zai iya rage masa ladan azumin ranar ko kuma ya rasa ladar azumin baki ɗaya, a cewar Abu Jabir.

Malamin ya ambaci wani Hadisin annabi Muhammad, inda yake cewa ”da yawa daga cikin mutane za su yi azumi amma babu abin da suke samu a azuminsu illa yunwa kawai."

Wannan na nufin za su yi azumi, amma babu lada, in ji malamin.

Ta yaya mai hawa soshiyal midiya zai kare ingancin azuminsa?

Tambayar da mai amfani da shafukan sada zumunta zai yi wa kansa shi ne ta wace hanya zai kare ingancin azuminsa?

Malam Abu Jabir Abdullah ya ce a duk lokacin da mutum zai yi amfani da shafin sada zumunta a cikin watan Ramadana, ya kamata ya yi wa kansa wasu tambayoyi guda biyu:

  • Shin alheri zan yaɗa ko kuwa na je neman alheri ne?
  • Me zan samu da zai amfani rayuwata?

Malamin ya shaida wa BBC wasu abubuwa da suka kamata mai azumi ya yi domin guje wa tauye ladan azuminsa.

  • A kauce wa latsa abubuwan haram: Idan Musulmi na son ya kare ingancin azuminsa "idan kafin Ramadan ka kalli wasu abubuwa da ba su da amfani, amma yanzu kuma sai ka ga irin waɗannan abubuwan sun bijiro maka (saboda algorithm) abu na farko da za ka yi shi ne nan take ka ambaci Allah, ka tuna cewa Allah Yana ganin ka, sai ka yi sauri ka fita.
  • A riƙa bin shafukan yaɗa abubuwan addini: Malamin ya bayyana cewa a lokutan Ramadana wasu mutane kan tsara yadda za a gudanar da abubuwan amfani ga rayuwar bil'adama, ''kamar masu sauke Qur'ani, ko fassara ayoyin Qur'ani ko hadisa ko tarihin sahabba.

"Irin wannan zai ƙara maka imani kuma zai kare martabar azuminka," in ji Abu Jabir.

Sauran abubuwan da malamin ya bayar da sahawarar a ƙaurace mawa su ne:

  • Yaɗa gulma
  • Yaɗa labaran ƙarya