KAI TSAYE, Arsenal na daf da lashe kofin Premier League na bana

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 17 zuwa 24 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Wasannin da za a buga ranar Talata, Premier League

    Liv

    Asalin hoton, BBC Sport

  2. Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Arsenal yanzu ta san cewa idan ta yi nasara a ranar Lahadi a kan Crystal Palace za ta lashe Premier League na Ingila na bana.

  4. An tashi wasan Arsenal 1-0 Burnley, Arsenal 1-0 Burnley

    Arsenal na daf da lashe Premier League, watakila a ranar karshe a karon farko tun bayan 2004.

  5. Mikel Arteta, Arsenal 1-0 Burnley

    Mikel Arteta ya yi canji biyu

    Leandro Trossard da Martin Odegaard sun fita an maye gurbinsu da Gabriel Martinelli da kuma Martin Zubimendi.

  6. Katin gargadi, Arsenal 1-0 Burnley

    Dan wasan Burnley, Zian Flemming ya yi karo ya samu kwallo sai ya yi karo da David Raya lokacin da suka tsalle, amma golan Arsenal ya fado kasa da karfi.

    Alƙalin wasa zai iya ɗaukar mataki kan wannan karo mai ƙarfi, domin ya yi kama da keta.

  7. An yi karin lokaci na minti bakwai, Arsenal 1-0 Burnley

    Lokaci na kurewa Arsenal na bukatar cin kwallo kada a samu matsala a farke.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  8. , Arsenal 1-0 Burnley

    Dan wasan Burnley, Josh Laurent ya yi kuskure mai sauƙi inda ya ture Myles Lewis-Skelly daga baya.

    Wannan ya bai wa Arsenal damar samun bugun tazara, inda za su iya ɗaukar lokaci su tsara kai hari cikin nutsuwa.

  9. , Arsenal 1-0 Burnley

    Arsenal na amfani da Viktor Gyökeres a gaba kamar wani injin—yana matuƙar wahala da ƴan bayan Burnley..

    Ƙarfin jikinsa da yadda yake riƙe ƙwallo ya sa Burnley ta kasa kwacewa da sauƙi, kuma hakan ya haifar wa Arsenal da jefa ƙwallo daga gefen fili.

  10. , Arsenal 1-0 Burnley

    Mai tsaron ragaR Burnley, Max Weiß ya yi jinkiri wajen fita da ƙwallo, sannan Viktor Gyökeres ya matsa masa da matsin lamba sosai.

    Gyökeres ya faɗi yayin da Weiß ya buga ƙwallon, amma alkalin wasa ya nuna cewa ba laifi ba ne.

  11. , Arsenal 1-0 Burnley

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  12. , Arsenal 1-0 Burnley

    Burnley na kokarin ci gaba da tazagawa a wasan, yayin da Loum Tchaouna ya fadi yana bukatar kulawar likitoci, sakamakon wani turewa ba tare da ƙwallo ba daga Piero Hincapié.

    Duk da haka, al’amarin bai yi kamar rauni mai tsanani ba, shi ya sa ake ganin ba a bayyana dalilin da ya sa aka kira likitoci nan take ba.

  13. , Arsenal da Burnley

    Arsenal ta yi nasara a dukkan wasa 10 a Premier League da ta buga da ƙungiyoyin da tuni suka fice daga gasar a wannan kakar — mafi kyakkyawan tarihin nasara da kaso 100% a gasar.

    Arsenal ba ta yi rashin nasara ba a gida cikin wasan 44 a Premier League da ƙungiyoyin da suka hau daga Championship (ta yi nasara 39 da canjaras biyar) tun bayan shan kashi 1-0 a hannun Newcastle United a Nuwambar 2010. Ta lashe wasa 15 na bayan nan da jimillar ƙwallaye 43-9.

  14. Arsenal ma ta yi canji, Arsenal 1-0 Burnley

    Wannan lokacin canji ne daga Arsenal, yayin da Kai Havertz da Eberechi Eze da kuma Riccardo Calafiori suka fita waje aka sauya su da Myles Lewis-Skelly da Viktor Gyokeres da kuma Piero Hincapie.

  15. Canji daga Burnley, Arsenal 1-0 Burnley

    Hannibal Mejbri da Lesley Ugochukwu sun fita daga fili, an mye gurbinsu da Zeki Amdouni da kuma Josh Laurent.

  16. , Arsenal 1-0 Burnley

    Sauran mintuna 30 a kare wasan a arewacin London.

    Idan har bambancin ƙwallaye (goal difference) zai zama abin da zai ƙayyade komai tsakani da Manchester City, to Arsenal za ta bukaci ta ƙara cin ƙwallaye a daren nan.

  17. , Arsenal da Burnley

    Arsenal ta yi rashin nasara a wasan gida na ƙarshe a rufe gasar Premier League a kaka ɗaya kacal cikin shekara 28 da suka gabata (nasara 23 da canjaras huɗu), kuma ba ta yi rashin nasara ba a irin wannan wasa cikin shekara 14 tun bayan shan kashi 2-1 a hannun Aston Villa a kakar 2010-11.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  18. Man City na shirin rabuwa da Guardila a karshen kakar nan, Arsenal 1-0 Burnley

    Manchester City na shirye-shiryen rabuwa da Pep Guardiola a Etihad, bayan wasan Premier League a ranar Lahadi a karawa da Aston Villa.

    Majiyoyi sun shaida wa BBC cewa ana sa ran fitaccen kocin zai bar Etihad Stadium a ƙarshen kakar bana.

    City dai tana nan kan matsayinta cewa Guardiola yana da kwantiragi har zuwa kakar wasa mai zuwa, kuma tana fatan zai ci gaba da zama a kungiyar.

    Sai dai ana ci gaba da shirye-shiryen ficewarsa a karshen kakar bana, inda wasu ma’aikata ke ganin zai bar aikin.

    Haka kuma an fahimtar cewa wasu daga cikin ƴan wasan suna tsammanin zai yi bankwana bayan wasan ƙarshe a kakar bana da Villa.

    Tsohon kocin Chelsea, Enzo Maresca, wanda ya taba aiki ƙarƙashin Guardiola a City, shi ne kan gaba wajen maye gurbin mai shekara 55.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  19. , Arsenal 1-0 Burnley

    Burnley tana samun ɗan lokaci mai kyau yanzu, yayin da Hannibal Mejbri ya kutsa gaba da gudu sannan ya yi buga kwallon da ƙarfi, amma ƙwallon ta wuce saman raga.

  20. , Arsenal 1-0 Burnley

    Leandro Trossard ya yi ƙoƙari sosai wajen aika ƙwallo daidai kan Eberechi Eze.

    Eze ya yi ƙoƙarin kai ta kusurwar raga da kai, amma bai iya sarrafa ta yadda ya kamata ba.