Ko shirin nukiliyar Iran barazana ce ga duniya?

A giant banner in Tehran features artwork depicting tall metal centrifuges similar to those at the Natanz nuclear enrichment facility and of scientists killed in Israeli attacks during the 12‑day war in June 2025

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani hoton da ke alamta kayan aikin inganta makamashin Uranium na Iran da kuma masana kimiyyar ƙasar da Isra'ila ta kashe a wani hari da ta kai cikin watan Yunin 2025
    • Marubuci, Luis Barrucho
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 6

Muhawara ta sake kaurewa kan shirin nukiliyar Iran.

Amurka ta jibge jiragen sama da na ruwa na yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ke nuna cewa ta shirya tsaf domin kai hari a Iran idan ƙasar ta ƙi amincewa da yarjejeniya kan ayyukanta na nukiliya.

A ranar 19 ga watan Fabarairu shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa "abubuwa marasa kyau" za su faru idan aka gaza cimma "yarjejeniya mai kyau".

Inda ya jaddada matsayarsa cewa: "Abu ne a bayyane, ba zai yiwu su mallaki makamin nukiliya ba...ba za a taɓa samun zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ba idan suka mallaki makamin mukiliya."

Iran ta sha musanta cewa ba ta taɓa yunƙurin hada makamin nukiliya ba, sai dai ƙasashe da dama - da kuma hukumar makamashin atam ta duniya mai sanya ido kan harkokin nukiliya (IAEA) - ba su gamsu da bayanan na Iran ba.

Wane mataki Iran ta kai a shirin nukiliya?

Har yanzu dai babu tabbacin matakin da Iran ta kai a shirinta na nukiliya, musamman bayan hare-haren a cibiyoyinta a yaƙin kwana 12 da ta gwabza da Isra'ila a bara.

Haka kuma Amurka ta shiga yaƙin na wani ɗan lokaci, inda ta ƙaddamar da hare-hare guda uku a cibiyoyin nukiliyar.

An kai harin ne a manyan cibiyoyin nukiliyar Iran, wato Isfahan da Natanz da Fordo, wuraren da ƙasar ke amfani da su domin inganta makamashin uranium.

Bayan hare-haren ne Trump ya ce ya "tarwatsa" cibiyoyin, duk da cewa mako daya bayan haka kuma shugaban cibiyar nazari da bibiyar makamin nukiliya ta duniya wato IAEA, Rafael Grossi cewa hare-haren sun yi "ɓarna" amma ba a "tarwatsa" su ba, sannan ya ce za a iya cigaba da aikin a cikin watanni kaɗan.

Taswirar da ke nuna cibiyoyin nukiliyar Iran uku da Amurka ta kai wa hari a watan Yunin 2025: Fordo, Natanz da Isfahan
Bayanan hoto, Taswirar da ke nuna cibiyoyin nukiliyar Iran uku da Amurka ta kai wa hari a watan Yunin 2025: Fordo, Natanz da Isfahan

IAEA ta yi ƙiyasin cewa a lokacin da Isra'ila ta kai hari a Iran a ranar 13 ga Yuni, ƙasar tana da kusan kilogram 440 na uraniun, da aka inganta zuwa kashi 60, wanda hakan ke nufin saura kaɗan ya kai matakin zama makami.

Grossy ya bayyana a watan Oktoba cewa da zarar an ƙara aiki kaɗan, za a iya haɗa makamin nukiliya guda 10 na sinadarin.

A watan Nuwamba, ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya bayyana wa jaridar Economist cewa sun tsaya aikin nukiliya.

Amma a watan jiya ya faɗa wa kafar Fox News cewa, "kun lalata kayan aikin da inginan, amma kuma fasahar na nan ai. Sannan kuma ba za a iya daƙile manufar ba," in ji shi.

Haka kuma Grossi ya bayyana wa Reuters a watan Janairu cewa IAEA ta ziyarci cibiyoyin nukiliyar Iran da ba a kai wa hare-hare ba.

Trump ya sha nanata cewa ba zai amince Iran ta samu nukiliya ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Trump ya sha nanata cewa ba zai amince Iran ta samu nukiliya ba

Yada aka kai wannan matakin

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gwamnatin Iran dai ta sha nanata cewa tana aikin nukiliya ne don ayyukan fararen hula.

Ƙasar na cikinn yarjejeniyar taƙaita samar da makamashi, wadda ta ayyana cewa za a iya sarrafa nukiliya ne kawai ayyukan fararen hula, ciki har da magunguna da noma da makamashi, amma ta haramta amfani da shi a matsayin makamashi.

Amma binciken IAEA ya gano cewa Iran ta aiwatar da wasu ayyuka da suke kama da samar da makami tun daga tsakankanin 1980s har zuwa 2003.

IAEA ta ce Iran ta dakata da aikin, wanda ake kira da Shirin Amad, amma a shekarar 2009, sai dai a shekarar 2009 hukumomin leƙen asirin ƙasashen yamma suka gano cibiyar Fordo.

A 2015, IAEA ta ce rahotanni ba ta da isasshen bayani da ke nuna cewa Iran ta cigaba da aikin nukiliya tun bayan 2009.

Haka kuma a shekarar ta 2015, Iran ta shiga yarjejeniyar da manyan ƙasashen duniya guda shida, inda ta amince ta taƙaita shirinta na nukiliya domin a rage mata wasu takunkumi.

Amma a 2018, Shugaba Trump ya fice daga yarjejeniyar, inda ya ce ba ta hana Iran aikin na nukiliya ba.

Bayan nan ita kuma Iran ta cigaba da aiki a cibiyarta ta Fordo, inda ta inganta uranium zuwa kashi 60.

Iran a ƙarƙashin jagoran addinin ƙasar Ayatollah Ali Khamenei, ta amince a 2015 ta taƙaita aikinta na nukiliya domin a rage mata takunkumi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Iran a ƙarƙashin jagoran addinin ƙasar Ayatollah Ali Khamenei, ta amince a 2015 ta taƙaita aikinta na nukiliya domin a rage mata takunkumi

Shin Iran na ci gaba da aiki yanzu?

Hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna cewa ana cigaba a gudanar da aiki a cibiyoyin Natanz da Isfahan a ƴan watannin da suka gabata.

A Isfahan, kusan duk hanyoyin zuwa cibiyar a rufe suke kamar yadda aka hango daga hotunan tauraron ɗan'adam.

Haka kuma hotunan sun nuna an rufe cibiyar Natanz.

Hotuna huɗu da ke nuna aikin gyara da aka yi a cibiyar inganta makamashin uranium ta Natanz a ranar 31 ga watan Mayun 2025, 30 ga watan Satumban 2025, 27 ga watan Disamban 2025 da kuma 9 ga watan Fabarairun 2026, inda za a iya ganin kafin, da kuma bayan hari, lokacin da ake aiki da kuma lokacin da aka kammala buga kwano.
Bayanan hoto, Hotuna huɗu da ke nuna aikin gyara da aka yi a cibiyar inganta makamashin uranium ta Natanz a ranar 31 ga watan Mayun 2025, 30 ga watan Satumban 2025, 27 ga watan Disamban 2025 da kuma 9 ga watan Fabarairun 2026, inda za a iya ganin kafin, da kuma bayan hari, lokacin da ake aiki da kuma lokacin da aka kammala buga kwano

Yaushe Iran za ta iya kammala makamin nukiliya?

Hukumar leƙen asirin Amurka DIA ta yi nazari a watan Mayun bara, kadin hare-haren Amurka da Isra'ila, inda ta ce Iran za ta iya kammala makamin "wataƙila a ƙasa da mako ɗaya."

DIA ta ƙara da cewa, "lallai Iran ba ta fara haɗa makamin nukiliya ba, amma ta ɗauki matakan da ake buƙata domin haɗa makaman a duk lokacin da take so."

Amma rundunar tsaron Isra'ila ta bayyana a watan Yuni cewa ta tattara bayanan da ke nuna cewa Iran "ta yi nisa" a aikin na nukiliya.

Ita ma Dr Patricia Lewis, masaniyar makamai mai zaman kanta ta ce Iran ta yi nisa a aikin, kafin ta dakata a shekarar 2003.

Shugaban IAEA Rafael Grossi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban IAEA Rafael Grossi

Me ya sa nukiliyar Iran ke da muhimmanci?

Ƙasashen yamma dai sun nace cewa ba ta saɓu ba a bari Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.

Trump ya bayyana a watan Mayun 2025 ce idan Iran ta samu nukiliya, "za ta tarwatsa duniya,"

Firaministan Birtaniya, Sir Keir Starmer ya ce idan Iran ta mallaki makamin nukiliya, "hakan zai zama babbar barazana ga yankin."

Wasu masanan sun bayyana cewa idan Iran ta mallaki makamin nukiliya, lamarin zai ƙara hargitsa yankin, da ƙara kusancinta a China da Rasha, sannan ta fara gogoriyon mallakar makamai da Saudiyya.

An dai san Isra'ila na da makamin nukiliya, amma ba ta taɓa tabbatarwa ko musantawa ba.