Abin da ya sa na ƙi bin jami’an tsaron da suka so su kama ni - El-Rufai

NAE
Lokacin karatu: Minti 5

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya ce babu wani nau'in bita da ƙulli da zai hana shi ci gaba da adawa da gwamnatin Najeriya, wadda ya ce ta jefa al'ummar ƙasar cikin mummunan yanayin da dole a tashi domin yaƙi da shi.

A ranar Alhamis 12 ga watan Faburairun 2026 jami'an tsaron Najeriya suka yi yunƙurin kama tsohon gwamnan jihar Kaduna, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja babban birnin Najeriya, jim kaɗan bayan saukar sa a Najeriya daga ƙasar Masar lamarin da ya janyo sa-in-sa a tsakanin su.

A hirar shi ta farko da BBC bayan dambarwar, Nasir El-Rufai ya yi bayanin abin da ya faru lokacin da jami'an tsaro suka yi yunƙurin kama shi.

Ya ce jayayyar ta taso ne lokacin da jami'an tsaron suka nemi ya bi su zuwa ofishin su domin ''ana son ganin shi'' a can, shi kuma ya nemi su nuna mashi takardar gayyata a hukumance, lamarin da kuma ya ci tura saboda babu takardar a tare da su.

''Ina sauka daga jirgi wani ɗan matashi ya zo da ƴar kwat ɗinshi ya ce su sun zo daga DSS kuma suna son su ganni a office ɗinsu, sai na ce ian takarda, say a ce za a bada takarda.

To da muka fito sai shugabannin shi su ma suka zo, suka yi wannan maganar, na ce takarda za ku bani. Gidana kusa da office ɗinku ne, in dai DSS ne, zan je gida idan baku da takardar yanzu ku kawo mani takarda can, amma haka nan kawai ba za ka tare ni a airport ka ce inzo ba.'' In ji El-Rufai

Ya bayyana abin da farun a matsayin wani ƙoƙari na cin mutumcin ɗan Adam wanda kundin mulkin Najeriya bai yarda da shi ba.

Tsohon gwamnan Kadunan ya kuma ce ba tsoro ya hana shi bin jami'an tsaron da suka yi yunƙurin maka shi ba.

Ya ce ''ban tsoron komai sai Allah, kuma na yi shekaa da shekaru ina aikin gwamnati a ƙasar nan, kuma na sha tura ƙalubale ga duk wanda ke da wani abu, duk wanda ya ce ya bani kwabo ko na nemi kwabo hanci wurin shi ko kuma akwai wata dukiya tawa wadda ba da gumina na tara ba, ya fito ya ce ni makaryaci ne,

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Nasir El-Rufai ya ce shekara biyu da rabi kenan jami'an EFCC da na ICPC suna yi wa jami'an gwamnatinsa bita da ƙullin siyasa, amma har yanzu ba su samu wani abu ba.

Ya ce dole ne sai ma'aikatan gwamnati sun yi aiki yadda ya kamata, ta hanyar bin doka da oda kamar yadda doka ta yi tanadi wajen bincike da hukunta mutane idan har ana son Najeriya ta ci gaba.

Ya kuma bayyana aniyarsa ta amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi masa domin amsa tambayoyi kan zargin rashawa wanda ya ce tuni ya bai wa hukumar amsa cewa yana nan zuwa a ranar Litinin 16 ga watan Faburairu, da misalin ƙarfe 10 na safe.

Malam Nasir El-Rufai wanda tsohon ministan babban birnin Najeriya, Abuja ne na cikin jagororin adawa a ƙasar waɗanda suka dunƙule a jam'iyyar ADC domin ƙalubalantar shugaba mai ci Bola Tinubu a babban zaɓen da za a yi a shekara mai zuwa.

A baya-bayan nan El-Rufa'i ya tsananta sukar da yake yi wa gwamnatin shugaban Najeriya Bola Tinubu da kuma jam'iyyar APC mai mulki, wadda a ƙarƙashinta ne ya yi gwamnan jihar Kaduna na shekara takwas.

A wata tattaunawa da BBC, El-Rufa'i ya ce duk da cewa ba a riga an kama shi ba, amma an kama na kusa da shi, kuma yana tunanin za a iya zuwa kansa nan ba da daɗewa ba.

"An kama mutum wajen guda huɗu waɗanda muka yi aiki da su a Kaduna, saboda haka ni ma lokaci ne, ni ma za a neme ni," in ji El-Rufa'i a tattaunawar tasa da BBC.

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

Wane ne Nasir El-Rufai?

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, kuma tsohon ministan Abuja, babban birnin Najeriya, na daga cikin mutanen da suka fi yamutsa hazo a siyasar Najeriya.

Akwai lokacin da sanatocin Najeriya suka taɓa yin yajin aiki domin tursasa wa shugaban Najeriya na wancan lokacin Olusegun Obasanjo ya cire shi daga muƙamin ministan Abuja saboda wani kalami da ya yi game da su, wanda suke ganin tamkar cin fuska ne.

An haife shi ne a watan Fabarairun 1960 a ƙaramar hukumar Faskari da ke jihar Katsina, arewa maso yammacin Najeriya.

Sai dai ya yi akasarin rayuwarsa da karatu ne a jihar Kaduna.

Ya yi karatunsa na sakandare a sananniyar makarantar nan ta Barewa College da ke Zariya, inda ya gama a matsayin ɗalibi mafi hazaƙa a shekara ta 1976.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda a nan ma ya kammala da sakamako mai kyawu, a ɓangaren karatun safiyo.

Ya kuma yi digiri kan harkar shari'a a Jami'ar Landan da ke Ingila sannan ya yi karatun digiri na biyu kan aikin gwamnati a shahararriyar jami'ar nan ta Harvard da ke Amurka, baya ga yin kwasa-kwasai da dama.

Ya kafa kamfanin safiyo da kula da ayyuka a shekara ta 1982.

A tsakanin shekara ta 1999 zuwa 2003 ya shugabanci ma'aikatar kula da kuma sayar da kadarorin gwamnati.

Daga nan kuma ya zama ministan Abuja daga 2003 zuwa 2007.

Ya zama gwamnan jihar Kaduna daga 2015 zuwa 2023.

Nasir El-Rufai mutum ne da ake wa kallon mai kaifin ƙwaƙwalwa da sanin dabarun tafiyar da al'amura, kuma ya ɗauki matasa masu ƙwazo a matsayin waɗanda yake aiki da su a duk muƙaman da ya riƙe.

Mutum ne mai yawan faɗar abubuwan da ke tayar da ƙura, ya yi kakkausan suka ga mutanen da suka soki yadda aka tafiyar da shirin sayar da kadarorin gwamnati a lokacin gwamnatin Olusegun Obasanjo.

Aikin da ya yi a matsayin ministan Abuja na daga cikin abubuwan da suka sa ya yi ƙaurin suna, lokacin da ya ce zai tabbatar da bin ainahin tsarin birnin.

Wannan ya haifar da rushe-rushe a lokuta da dama, inda daga nan ne ya samu laƙabin 'Mai rusau', saboda rusa gine-ginen da aka yi ba bisa ƙa'ida ba.

Kuma har yanzu akan auna aikin duk wani minstan Abuja ne da ayyukan da El-Rufai ya gudanar a zamaninsa na ministan Abuja.