Real Madrid ce kan gaba a neman Schlotterbeck, Gordon zai maye gurbin Salah a Liverpool

Nico Schlotterbeck

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nico Schlotterbeck
Lokacin karatu: Minti 2

Tottenham da Newcastle suna sha'awar dawo da dan wasan gaban Al-Hilal mai shekaru 26 Darwin Nunez tsohon dan wasan Liverpool zuwa gasar Premier. (Teamtalk)

Tottenham da Aston Villa suna cikin kungiyoyin da ke sa ido kan dan wasan tsakiya na Lyon mai shekaru 25 Pavel Sulc. (Mail)

Dan wasan baya na Ingila Joe Gomez yana shirin barin Liverpool a wannan bazararinda AC Milan da Bayern Munich ke neman wasan mai shekaru 28. (Cought Offside)

Roma da Juventus sun shiga takarar sayen dan wasan baya na Argentina mai shekaru 28 na Bournemouth Marcos Senesi a karshen kakar wasa. (Corriere Dello Sport)

Real Madrid ce ke kan gaba wajen neman dan wasan baya na Jamus na Borussia Dortmund Nico Schlotterbeck, amma Barcelona ma tana sha'awar dan wasan mai shekaru 26. (AS Sport)

Newcastle na sha'awar siyan dan wasan baya na Sifaniya Hugo Bueno mai shekaru 23 daga Wolves a wannan bazarar. (Football Insider)

Liverpool na shirin mika tayin £83m ga dan wasan gefe na Ingila Anthony Gordon mai shekaru 24 na Newcastle idan dan wasan gaba na Masar Mohamed Salah, mai shekaru 33, ya bar kungiyar a wannan bazarar. (Fichajes)

Everton na shirin gabatar da tayin £30m ga dan wasan gaba na Chelsea mai shekaru 23 Liam Delap a wannan bazarar. (Teamtalk)

Crystal Palace na kokarin shawo kan Gareth Southgate ya maye gurbin Oliver Glasner a matsayin kocin rikon kwarya har zuwa karshen kakar wasa. (Football Insider)