Alvarez na son zuwa Barca, Ina Rudiger zai tafi?

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan gaba na Al-Ahli da Ingila Ivan Toney ya buɗe ƙofarsa ta son komawa taka leda a gasar Premier. (Sky Sports)
Liverpool ba ta son sayar da Dominik Szoboszlai duk da alaƙanta ɗanwasan na tsakiya da Real Madrid, amma tana ci gaba da tattaunawa da shi domin sabunta kwangilar shi. (Teamtalk)
Ɗanwasan gaba na Jamus Nick Woltemade ba ya jin daɗin zamansa a Newcastle kuma ɗanwasan mai shekara 24 na son ya koma taka leda a Stuttgart ko Bayern Munich. (Bild - in German)
Manchester United ba ta son rage farashin da ta saka kan ɗanwasan gaba na Ingila Marcus Rashford, wanda ke murza leda a matsayin aro a Barcelona. (Mail)
Sunderland na son sayen ɗanwasan gaba domin maye gurgin ɗanwasan Faransa Wilson Isidor, da ke son raba gari da ƙungiyar. (Football Insider)
Atletico Madrid na son ɗanwasan gaba na Argentina Julian Alvarez ya sabunta yarjejeniyar shi amma ɗanwasan mai shekara 26 ya fi son ya koma Barcelona. (Sport - in Spanish)
Tottenham da Crystal Palace da West Ham na cikin ƙungiyoyin da ke hamayya kan ɗanwasan baya na Real Madrid mai shekara 32 Antonio Rudiger a wannan bazara (Fichajes - in Spanish)
Chelsea na farautar ɗanwasan baya na Nottingham Forest da Brazil Murillo amma sai Chelsea ta biya fam miliyan 70. (Caught Offside)
Everton za ta yi watsi da tayin Tottenham kan ɗanwasan tsakiya na Ingila Kiernan Dewsbury-Hall a wannan bazara. (Football Insider)











