Abin da ya sa Iran za ta zaɓi fito-na-fito da Amurka maimakon miƙa wuya

Wasu mata

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu Iraniyawa lokacin da suke wucewa kusa da wani allo da ke adawa da Amurka a birnin Tehran
    • Marubuci, Amir Azimi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Persian
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ci gaba da girke dakarun Amurka a Gabas ta Tsakiya na ƙara nuna yadda Amurkar ke shirin far wa Iran.

Isar jirgin ruwan yaƙin Amurka USS Abraham Lincoln kusa da gabar ruwan Iran, shi kaɗai wani babban mataki ne.

An kuma ga wani jirgin ruwan yaƙi USS Gerald R Ford kusa da mashigar Gibraltar inda ya nufi gabashi domin taimakawa. Har ila yau an kuma kai wasu kayan yaki zuwa yankin, abin da ke nuni da cewa Washigton na duba yiwuwar ɗaukar matakin soja.

Jirgin ruwan yaƙin Amurka.

Asalin hoton, US Navy / Reuters

Bayanan hoto, Lokacin da jirgin ruwan yaƙin Iran USS Gerald R Ford ke isa wani tsibiri a watan Disambar 2025

Aika irin waɗannan abubuwa na nuna cewa ba a ɗauki hanyar diflomasiyya ba. Hakan kuma na iya nuna cewa ba a cimma matsaya ba a tattaunawar kai-tsaye tsakanin Tehran da Washington - abin da zai sa a ɗauki matakin soji idan kowane ɓangare ya ja daga.

Wannan ya jawo ayar tambaya: Me ya sa shugabannin Iran ke ci gaba da nuna turjiya ga ƙasar da ta fi ƙarfin soji a duniya a bainar jama'a da kuma babbar ƙawarta a Gabas ta Tsakiya?

Amsar na ga sharuɗan da Washigton ta gindaya na tattaunawar da ake yi.

Jirgin ruwan yaƙin Amurka.

Asalin hoton, US Navy / Reuters

Bayanan hoto, Jirgin ruwan yaƙin Amurka USS Abraham Lincoln yayin wani atisaye a tekun Larabawa ranar 6 ga watan Fabrairu

Sharuɗan Amurka na nuna da wuya a cimma matsaya

Ga Tehran, tana ɗaukar waɗannan bukatun Amurka a matsayin wani abu na daban ba tattaunawa ba.

Sun haɗa da kawo karshen mallakar sinadaran uranium, rage yawan makamai masu linzami saboda su daina barazana ga Isra'ila, dakatar da bai wa ƙungiyoyin mayaƙa goyon baya a faɗin yankin da kuma sauya yadda Jamhuriyar ta Musulunci ke ɗaukar ƴan ƙasar, kamar yadda sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana

A ɓangaren shugabannin Iran, waɗannan ba tsare-tsare ne da za su yi watsi da su ba. Suna ɗaukar su a matsayin tsarin tsaron ƙasar.

Tehran ta shafe gomman shekaru tana gina gungun ƙawaye masu ɗauke da makamai a duka faɗin Gabas ta Tsakiya waɗanda ake kira ƙawancen gwagwarmaya wato "Axis of Resistance".

Suna da burin nesanta rikici da iyakokin Iran da kuma matsa lamba kan Isra'ila.

Tehran

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wata jarida a Tehran ta wallafa hoton wani gwajin makami mai linzami cikin teku

Shirin makamin linzami na Tehran ya zama abun da ake ganin zai maye gurbin dabaru yakin saman ƙasar da suka tsufa, ganin kuma ba sa samun fasahohin zamani na soji.

Shirin nukiliyar Iran wanda ake ganin na zaman lafiya ne a duniya, a gefe guda yana da barazana.

Tehran na ganin ragewa ko kuma watsar da waɗannan abubuwa a matsayin barazana gare ta.

Jiragen ruwan soji biyu

Asalin hoton, Iran Army Office / EPA

Bayanan hoto, Jirgin ruwan yaƙin Rasha a wani atisaye da takwaransa na Iran a tekun Oman ranar 19 ga Fabrairu

Barazana ga jagoran addini

Daga ɓangaren jagoran addini na ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, yana ganin karɓar waɗannan sharuɗa na da hatsari fiye da shiga yaƙi da Amurka karkashin Donald Trump.

Zai fi so a ce ya shiga yaƙi da Amurka duk da cewa akwai kasada maimakon watsar da tsarin tsaron ƙasarsa.

Sai dai, akwai hatsari a tattare da matakin, kuma ba ga Iran kaɗai ba.

Kwamandojin sojin Iran

Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images

Duk wani shiri da Amurka za ta yi, zai ta'allaka ne kan manyan jagororin Iran a matakin farko. Idan aka kashe Kamenei, hakan ba zai kawo karshen mulkinsa na gomman shekaru ba, sai dai zai ƙara dagula al'amura ga wanda zai gaje shi.

Hare-hare kan dakarun juyin juya-hali da sauran hukumomin tsaro za su ƙara rage ƙarfin tsarin tsaron Iran wadda ba da daɗewa ba da dadewa ba ta maido ka karfin ikonta bayan wata kazamar zanga-zanga da ta girgiza ƙasar, karon farko a tarihinta.

Har yanzu masu zanga-zangar da suka karaɗe tituna a makonnin baya-bayan nan - waɗanda suka janye ta ƙarfi - ba su gamsu ba zuwa yanzu.

Masu zanga-zanga

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam sun ce an kashe dubban mutane a lokacin zanga-zangar kin jinin gwamnati a Iran a 2026

Tehran na iya tunanin cewa burin Amurka shi ne tarwatsa shirinta na nukiliya da kuma makamai masu linzami. Sai dai, da wuya yake-yake su ɓarke a cewar masu hasashe. Amma rikice-rikice musamman na siyasa zai janyo rikici ya faɗaɗa.

Matsi kan tattalin arziki wata barazana ce da ke kan Iran. Tattalin arzkin wanda tuni ya fuskanci takunkumai, hauhawar farashi da kuma raguwar masu saye zai ƙara shiga wani yanayi.

Cikas ga hanyoyin fitar da mai da kuma lalata ababen more rayuwa zai ƙara janyo fushin al'umma wadanda tuni suka harzuka.

Cibiyar nukiliyar Iran

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani hari da Amurka ta kai cibiyar nukiliyar Iran na Natanz a watan Yunin 2025

Barazana ga Washington

Haɗarin ga Washington ba kaɗan ba ne.

A rubuce, sojojin Amurka suna da ikon cika burin babban kwamandan Amurka. Amma ba a yin yaƙi da baki kawai.

Ana tsara su ta wasu hanyoyi na daban wanda ma ba a yi niyya ba.

Donald Trump.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Shugaban Amurka Donald Trump na aika jiragen ruwan yaƙi zuwa Gabas ta Tsakiya

Yaƙin kwana 12 da Iran ta yi da Isra'ila a shekarar da ta wuce ya ƙara nuna ɓarakar sojin Tehran. Ya kuma nuna yadda za a kare kai daga hare-hare da kuma mayar da martani cikin gaggawa.

Takun-tsaka kuma zai janyo abin da kowane ɓangare ba zai ji daɗinsa ba.

Ayatollah Khamenei.

Asalin hoton, Iran's Supreme Leader Office via EPA

Bayanan hoto, Shugaban addini na Iran Ayatollah Khemenei zai yanke shawarar yadda zai mayar da martani ga buƙatun Amurka

Zaɓin da ya rage wa Ayatollah Khamenei ba su da yawa a yanzu. Amincewa da sharuɗan Washington kuma na da barazana ga tsarin tsaronta sannan watsi da su zai kara janyo yiwuwar fito na fito.

Trump da Ayatollah

Asalin hoton, EPA / Iran's Supreme Leader Office via EPA