Laifukan da Majalisar dokokin Kaduna ke zargin El-Rufa'i da aikatawa

...

Asalin hoton, X/elrufai

Kwamitin da Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa kan nazari game da kuɗaɗen da aka kashe a gwamnatin da ta gabata a jihar ya miƙa sakamakon bincikensa a yau.

Cikin shawarwarin da kwamitin ya bayar har da na buƙatar hukumomi su binciki tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i.

Lokacin da ya gabatar da rahoton a ranar Laraba, shugaban kwamitin, Henry Zacharia ya ce an gano cewa akasarin kuɗin bashin da jihar ta karɓa a zamanin mulkin El-Rufa'i, ko dai ba a yi amfani da su kan abin da aka ciyo bashin domin su ba ko kuma ba a bi ƙa'ida wajen cin bashin ba.

Da yake karɓar rahoton, shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman ya ce kuɗi naira biliyan 423 ne suka zurare a lokacin gwamnatin El-Rufa'i tare da jefa jihar cikin ƙangin bashi.

'Laifukan da kwamitin ya gano' a kan El-Rufa'i

Rahoton kwamitin ya ce: tsakanin ranar 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayu 2023, shugaban ɓangaren zartarwa na jihar Kaduna ya karya ƙa’idojin aikin ofishinsa kamar yadda suke a kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 wanda aka yi wa gyaran fuska, inda ya aikata laifuka kamara haka:

  • Jefa jihar cikin ƙangin bashi na cikin gida da waje ta hanyar ha’inci ba tare da dalili ba, waɗanda suka zarce jimillar ɗaukacin basukan da jihar Kaduna ta taɓa ci daga shekarar 1965 zuwa 1999, kuma yawanci an karɓo bashin ne ba tare da bin ƙa’ida ba.
  • Bayar da kwangiloli barkatai ba tare da bin ƙa’ida ba kuma ba tare da bin diddigin aiwatarwa ba, wanda hakan ya haifar da yin watsi da kwangiloli da dama duk kuwa da kuɗaɗen da aka biya.
  • Bayar da izinin cire maƙudadan kuɗaɗen naira da dalar Amurka ba tare da bayanin yadda aka yi amfani da su ba, wanda hakan ya hana jihar samun isassun kuɗaɗen da za ta aiwatar da ayyukan ci gaba.
  • Haɗa baki da kwamishinoni da shugabannin hukumomin gwamnati domin ha’intar gwamnati ta hanyar umurtar hukumar KADPPA ta biya ƴan kwangila kuɗi ba tare da bin ƙa’ida ba, kamar yadda yake ƙunshe a wata wasiƙa mai kwanan wata 21st Yuni, 2021.
  • Karkatar da kuɗi da halasta kuɗaɗen haram wanda ya saɓa da dokoki da ƙa’idoji, kuma ya kamata a miƙa shi ga hukumomin tsaro domin gudanar da zuzzurfan bincike tare da ɗaukar matakan da suka kamata.

Wasu shawarwari da kwamitin ya bayar

...

Asalin hoton, fb/Kaduna State House of Assembly

Kwamitin na Majalisar dokokin jihar Kaduna ya ce: ya haƙiƙance cewa hujjoji sun bankaɗo ayyukan rashawa da dama a wajen tafiyar da lamurran gwamnati, da ma’aikatu da kuma hukumomin gwamnatin jihar Kaduna tsakanin ranar 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2023, kuma kwamitin ya bayar da shawarwari kamar haka:

  • Hukumar tara kuɗaɗen haraji ta jihar Kaduna ta cire kuɗi kuɗin da aka tara na cikin gida naira biliyan 20 waɗanda aka ajiye a wani asusun bankin Zenith, tare da umurtar bankin da ya mayar da duk wasu kuɗaɗe da ya cire waɗanda suka samo asali daga waɗannan kuɗade da aka ajiye.
  • A tura duk waɗanda suka riƙe muƙamin kwamishinan kuɗi na jihar daga watan 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2023 ga hukumomin tabbatar da tsaro na ƙasa domin fuskantar bincike.
  • A tura duk waɗanda suka riƙe muƙamin babban akanta na jihar daga 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2023 ga hukumomin tsaro domin fuskantar bincike
  • A tura duk waɗanda suka shugabanci hukumar tara kuɗaɗen haraji na jihar Kaduna daga 29 ga watan Mayu, 2015 zuwa 29 ga watan Mayu, 2023 ga hukumomin tabbatar da tsaro domin fuskantar bincike.
  • Kwamishinan kuɗi na jihar Kaduna da ke kan muƙami a yanzu ya sauka daga muƙaminsa domin samun damar gudanar da bincike yadda ya kamata kan ayyukan ma’aikatar kuɗin jihar daga 29 Mayu, 2015 zuwa 29 Mayu, 2023.
  • Shugaban hukumar bayar da ilimi a matakin farko mai ci a yanzu ya sauka domin bayar dadamar a binciki ma’aikatarsa kan ayyukan da ta gudanar daga 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2023.
  • Shugaban hukumar fansho ta jihar Kaduna mai ci a yanzu ya sauka daga muƙaminsa domin samun gudanar da bincike yadda ya kamata kan ayyukan hukumarsa daga 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2023.
  • A tura duk waɗanda suka riƙe muƙamin shugaban hukumar bunƙasawa da gudanar da kasuwannin jihar Kaduna daga 29 ga watan Mayun 2025 zuwa 29 ga watan Mayun 2023 ga hukumomin tsaro domin fuskantar bincike kan yadda suka tafiyar da ma’aikatar.
  • A tura shugaban shirin noman rani na alkama a Ruwan Sanyi da ke ƙaramar hukumar Kubau a shekarar 2016 ga hukumomin tsaro domin fuskantar bincike.
  • A tura tsohuwar shugabar hukumar KAPSO, Ms Dolapo Popoola zuwa wurin jami’an tsaro domin fuskantar bincike da kuma ƙwato kadadrorin gwamnati da ke hannunta.
  • A tura mai taimaka wa tsohon gwamnan kan yaɗa labaru da sadarwa tsakanin watan Mayun 2025 zuwa watan Mayun 2023, Muyiwa Adekeye ga hukumomin tsaro domin fuskantar bincike kan hannunsa a kwangilolin gyara Hukumar yaɗa labaru ta jihar Kaduna (KSMC).
  • A tura ɗaukacin shugabannin hukumar kula da tituna ta jihar Kaduna daga 11 ga watan Oktoba, 2017 zuwa Nuwamba, 2021 – in ban da Amina Ja’afar Ladan, wadda ta yi wata ɗaya kacal kan kujerar – zuwa ga hukumomin tsaro domin fuskantar zuzzurfan bincike kan yadda aka bayar da kwangiloli da kuma rashin ingancin ayyukan da aka bayar a lokacin shugabancinsu, sannan a sauya wa manyan jami’an hukumar wurin aiki zuwa wasu ma’aikatu da hukumomi masu alaƙa.
  • Dukkanin basuka na cikin gida ko na waje da gwamnatin jihar Kaduna ta karɓa tsakanin 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2023, waɗanda kwamitin ya gano cewa ba a karɓe su kan ƙa’ida ba, babu ruwan gwamnati da su kuma daga yanzu ba za ta ci gaba da cika duk ƙa’idojin da suka ƙunsa ba.
  • Kwamitin ya lissafo sunan wasu kamfanoni waɗanda ya ce su mayar wa gwamnatin jihar Kaduna jimillar kuɗi biliyan 36,351,126,811.65 ko dai saboda an biya su kuɗi ba su yi aiki ba ko an yi aringizon kuɗi wajen biyan su ko kuma an karkatar da kuɗin.
  • A miƙa batun kuɗi naira biliyan 4,936,916,333.00 waɗanda kwamishinan kuɗi da babban akantan jihar suka cire ba tare da wata hujja ba tsakanin shekarun 2019 zuwa 2022 ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike da ɗaukar mataki.
  • A miƙa batun kuɗi dalar Amurka miliyan 1.4 da aka cire daga asusun haɓɓaka tattalin arziƙin jihar tsakanin 30/10/2020 zuwa 06/05/2020 ga hukumomin tsaro domin gudanar da zuzzurfan bincike a kai.

Martanin El-Rufa'i

Sai dai tsohon gwamnan ya ce binciken da majalisar jihar ta ba da shawarar a yi kan gwamnatinsa "bi-ta-da-ƙulli ne kawai na siyasa".

Cikin wata sanarwa da Muyiwa Adekeye ya fitar a madadinsa, El-Rufai ya ce ya bauta wa Kaduna "da gaskiya kuma yana alfahari da abubuwan da ya yi".

"[El-Rufai] ya bi duk wasu dokoki a ayyukansa lokacin da yake gwamna...ya kamata a yi watsi da wannan binciken na ƙeta a matsayin bi-ta-da-ƙullin siyasa."

Kwamitin ya buƙaci da a binciki tsohon gwamnan da wasu jami'an gwamnatinsa kan zargin rashawa da bayar da kwangila ba bisa ƙa'ida ba da kuma halasta kuɗin haram.

...

Asalin hoton, fb/Kaduna State House of Assembly

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A watan Afrilu wannan shekara ne Majalisar Dokokin Kaduna ta kafa kwamiti domin binciken ayyukan da gwamnatin El-Rufa'i ta aiwatar tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.

Hakan ya zo ne bayan gwamnan jihar, Uba Sani, ya koka kan cewa jihar na fama da ƙangin bashin da ya kai na naira biliyan 85 da kuma wasu ayyukan da ke buƙatar kuɗi naira biliyan 115 domin kammalawa.

Uba Sani ya bayyana cewa a halin da ake ciki "jihar ba ta iya biyan albashi ba tare da ta ciyo bashi ba".

Lamarin ya haifar da muhawara, ganin cewar a baya ana yi wa gwamna Uba Sani da tsohon gwamna Nasiru El-Rufai kallon aminan juna.

A shekarar 2023 ne Nasir El-Rufa'i ya miƙa ragamar mulkin jihar ta Kaduna ga Sanata Uba Sani, bayan kammala wa'adin mulkinsa na shekara takwas.

Uba Sani ya zama gwamna ne bayan ya lashe zaɓen da aka gudanar a watan Maris na shekara ta 2023.

Kafin wannan lokacin, Uba Sani ya kasance ɗan majalisar dattijai mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta tsakiya, kuma ana ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen karɓar basussukan da gwamnatin jihar Kaduna ta samu a lokacin mulkin Nasir El-Rufa'i.

Kaduna na daga cikin jihohin Najeriya waɗanda suka fi yawan bashi a kansu.