Fari da rage tallafin jin ƙai na ƙara haddasa bala’i a Somalia - MSF

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar agajin lafiya ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta yi kira da a ɗauki matakin gaggawa domin faɗaɗa shirye-shiryen ciyar da masu fama da yunwa da rigakafi da samar da ruwan sha a Somalia.
Ƙungiyar ta gargaɗi cewa idan har ba a samar da martani haɗin gwiwa tsakanin sassa daban-daban ba, za a iya fuskantar asarar rayuka masu yawa.
Kiran na zuwa ne a daidai lokacin da kakar rani ta fara, yayin da MSF ke kira ga masu ba da tallafi da hukumomin Somalia su gaggauta sakin kuɗaɗen agajin gaggawa domin ceto rayuka.
Somalia na fuskantar mummunar matsalar lafiya sakamakon fari tare da raguwar tallafin jin ƙai.
A watan Nuwambar shekarar da ta gabata, gwamnatin Somalia ta ayyana dokar ta-baci kan fari.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, MSF ta ce cibiyoyinta a yankunan Baidoa da Mudug na fuskantar ƙaruwar yara masu fama da tsananin yunwa da kuma ɓarkewar cututtukan da za a iya kauce musu, ciki har da sankarau da cutar mashaƙo da gudawa.
MSF ta ce fari na lalata hanyoyin samun abinci da abin dogaro, tare da tilasta wa iyalai guduwa zuwa sansanonin ’yan gudun hijira inda ake fama da ƙarancin ruwa mai tsafta.





