Yadda za ku hana masu kisan gilla kutsawa cikin gidajenku

Wasu mutane a ƙofar wani gida

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Batun kisan da aka yi wa wata mata tare da ƴaƴanta shida a jihar Kano na ci gaba da razana al'ummar ciki da wajen jihar.

Wasu matasa ne dai ɗauke da makamai suka kutsa gidan matar da ke unguwar Dorayi Charanci da tsakar rana inda suka halaka ta tare da duka ƴaƴanta nata.

Lamarin na zuwa ne ƙasa da watanni bayan da wasu matasan suka shiga wani gida a unguwar Tudun Yola da ke birnin na Kano suka kuma kashe matan gidan biyu tare da ƙona gawarwakinsu.

Waɗannan kashe-kashe sun tayar da hankula tare da ƙara jefa tsoro da fargaba a zukatan al'ummar jihar - waɗanda ke ganin rayuwarsu na cikin barazana.

Kan haka ne masana tsaro ke ci gaba da bayar da shawarwari na matakan da ya suka mutane su ɗauka domin kauce wa wannan matsala.

AMB. Capt. Abdullahi Bakoji Adamu (mai ritaya), Mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya ya bayyana wa BBC dabaru bakwai da ya kamata magidanta su ɗauka domin kare iyalansu.

Kulle gida da kula da ƙofa

Wata mata

Asalin hoton, Getty Images

Masanin tsaron ya ce abu na farko da ya kamata kowane magidanci ya kula da shi ne sabar wa iyalansa rufe gida kodayaushe.

''Ya kamata ya kasance iyalanka su suba da cewa ƙofar gidanka koyaushe, safe rana da dare a rufe take''.

Ya ƙara da cewa idan wani ya yi sallama kada a buɗe ƙofar sai an tabbatar wane ne, daga ina ya fito kuma mene ne dalilin zuwansa.

''Kada a taɓa buɗe ƙofar kai-tsaye, koda mutumin ya bayyana cewa shi ne wane, sai an tabbatar ta waya ko ta makwabta'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa a hana yaran gida buɗe ƙofa.

Tsarin fita daga gida

Wani mutum na fita daga cikin gidansa

Asalin hoton, OTHERS

Capt Bakoji mai ritaya ya ce wata dabarar da ya kamata magidanta su riƙe ita ce bayyana wa iyalanka inda za ka je a duk lokacin da za ka fita daga gidanka.

''Ka sanar da su lokacin da kake sa ran dawowa, sannan idan za ka aiko wani mutum ka sanar da su tare da faɗa musu sunan mutumin da ka aiko da saƙon da ke tafe da shi'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa iyalanka su saba da cewa a duk lokacin da aiko wani mutum to za ka faɗa musu, ta yadda idan wani ya zo ya yi ƙaryar cewa kai ka aiko shi ba za su buɗe masa ƙofa ba.

Inganta tsarin sadarwa

waya

Asalin hoton, Getty Images

Mai sharhi kan al'amuran tsaron ya ce yana da kayu magidanci ya lazimci kiran iyalinsa akai-akai idan ya fita harkokinsa, don jin halin da suke ciki.

''Kada ka taɓa barin wayar iyalinka babu kati, ko da na naira 100 ne, koda buƙatar gaggawa za ta taso mata'', in ji shi.

Ya kuma ce yana da kyau magidanci ya tanadi waya ta musamman a gida don kiran gaggawa.

''A duk lokacin da ka ga kira da wayar to ka san akwai matsala''.

Masanin tsaron ya kuma shawearci magidanta su guji ƙin ɗaukar wayar iyalinsu ko ta makwabta saboda suna cikin uzuri.

''Ba ka san dalilin kiran ba, don haka ko kana cikin taro ko wata ganawa ka nemi uzurin ƴan daƙiƙoƙi domin ɗaga wayar ko ka kira idan ta kashe don ka ji dalilin kiran'', in ji shi.

Lambobin gaggawa

Capt Bakoji mai ritaya ya ce yana da kyau, kowane magidanci ya tabbatar iyalinsa suna da lambobin wayar makwabtansu 'nagari' (maza da mata).

''Yana kuma da kyau ka tabbatar suna da lambobin ƴan banga ko ƴanbijilan na unguwa da lambar mai unguwa da jami'an ƴansanda mafi kusa'', in ji shi.

Ya ƙara da abu ne mai kyau magidanci ya samu takarda ya rubuta duka waɗannan lambobi ya manne a jikin bango domin kowa ya hardace su.

Motar ƴansanda

Asalin hoton, Getty Images

Tsare sirrin gida

Masanin tsaron ya ce iyalai su guji bayyana sirrin gidansu a waje idan sun fita, ko abokai da ƙawaye idan sun zo gidan.

''A guji faɗar lokacin da maigida yake fita ko yake dawowa, ko faɗin cewa yanzu su kaɗai a gida'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa a yi ƙoƙarin hana yaran gida saurin sabawa da baƙi, idan sun zo.

Haɗa kai da maƙwabta

Capt. Bakoji ya ce yana da kyau kowane magidanci ya gina kyakkyawar alaƙa da maƙwabtansa.

''Su kuma makwabta a matakin unguwa su kafa tsaron unguwa, tare da raba jadawalin sanya idanu kan unguwarku''.

''Ku riƙa sanar da juna idan kun ga wani abu da ba ku yarda da shi ba a unguwarku''.

Masanin tsaron ya ce unguwa mai haɗin kai tana da wahalar kai mata hari.

Sanya fitilu a cikin gida

Capt Bakoji ya ce yana da kyau magidanta su sanya fitilu a ciki da wajen gidansu.

''Ɓarayi suna tsaron haske, don haka wannan zai taimaka ƙwarai'', in ji shi.

Ya ce magidanci ya tabbatar yana kula da lafiyar katantar da ta ƙofar gidansa.

''Idan ma kana da hali ka sanya kyamarar tsaro ta CCTV, wannan duk zai taimaka'', in ji shi.

Daga ƙarshe masanin tsaron ya ce tsaro ba aikin gwamnati kaɗai ba ne, ba na Jami'an tsaro bane kawai.

Tsaro alhakin kowa ne, musamman magidanci da duka haƙƙin iyalinsa ke rataye a wuyansa.

'A haɗa da addu'a'

Baya ga duka waɗannan matakan sai kuma a haɗa da addu'o'i.

Addu'a na da matukar tasiri wajen kariya, kamar yadda koyarwar addini ta nuna.

A tsananta addu'o'in safiya da maraice da ta fita daga gida da sauransu