Konate na son karin albashi, Mainoo zai ci gaba da taka leda a Man U

Asalin hoton, Getty Images
Palmeiras na zawarcin dan wasan gaban Arsenal Gabriel Jesus. Dan wasan mai shekara 28 ya murmure daga raunin da yaji na tsawon lokaci sai dai zai kasance ba shi da kwantaragi da wata kungiya a 2027 kuma watakila ya koma gida Brazil. (Mail), external
Manchester United na bibiyar dan wasan tsakiyar Sunderland Noah Sadiki mai shekara 21, kuma watakila ta bayar da dan wasan tsakiya na kasar Uruguay, Manuel Ugarte mai shekara 24 a yarjejeniyar musaya da dan wasan Jamhuriyar Dimokraddiyar Kongo(Give Me Sport), external
A wani labarin kuma ana sa ran Kobbie Mainoo zai ci gaba da taka leda Manchester United bayan an nada kocin rikon kwarya Michael Carrick. Dan wasan tsakiyar mai shekaru 20, wanda ya buga wa Ingila wasanni 10, na tunanin za a bada shi aro domin ya kara buga wasa akai-akai.(Fabrizio Romano), external
Ipswich na son ta dauko dan wasa gaban Bristol City Anis Mehmeti. Dan wasan kasar Albania mai shekara zai kasance ba shi da kwantaragi da wata kungiya a bazara. (Football Insider), external
Kawo yanzu Flamengo na son daukar dan wasa tsakiyar West Ham United Lucas Paqueta duk da cewa bangarorin biyu basu tuntubi juna tun makon daya gabata ba game da kula yarjejeniya da dan wasan kasar Brazil mai shekara 28. (Sky Sports), external
Dan wasan tsakiyan Feyenoord Quinten Timber da West Ham da Aston Villa ke zawarci bai buga wa kungiyarsa tamaula ba a wasan da suka yi ranar Lahadi. Marseille ta riga ta nemi a sayar mata da dan wasan Netherlands mai shekara. (Mail), external
Kawo yanzu Liverpool da Ibrahima Konate sun kasa cimma matsaya kan sabon kwantaragi. Dan wasan kasar Faransa, mai shekara 26, na kakarsa ta 6 a Anfield kuma ya yi ammanar cewa yana cikin masu tsaron baya da suka cancanci a biyasu albashin mai gwabi a wasannin firmiya .(Teamtalk), external
Watakila Liverpool ta maye gurbin Konate da dan wasa mai tsaron bayan Tottenham Micky van de Ven mai shekara 24, wanda ke jan hankalin Real Madrid . (Teamtalk), external
Chelsea ta amince da bukatun da Jeremy Jacquet mai shekaru 20 ya gabatar mata, amma har yanzu za ta bukaci inganta yunkurinta na sayen dan wasan baya na Rennes da Faransa a tawagar 'yan kasa da shekara 21 wanda Arsenal ke so.(Metro), external
Bournemouth za ta yi watsi da duk wani yunkurin siyan Marcos Senesi a wannan wata duk da cewa dan wasan kasar Argentina mai shekara 28 ya ki ya tsawaita kwantaraginsa da kungiyar wanda zai kare a bazara . Juventus na Barcelona duk suna sha'awar dan wasan (Talksport)













