Yadda 'yansanda suka yi amai suka lashe kan sace mutane a Kaduna

Tambarin ƴansandan Najeriya

Asalin hoton, NPF

Lokacin karatu: Minti 2

Rundunar ƴansandan Najeriya ta sanar da sauya matsayar da ta ɗauka a baya cewa ba a sace mutane ba a garin Kurmin Wali na ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, inda a yanzu rundunar ta tabbatar da garkuwa da mutanen.

A ranar Litinin aka fara samun rahotannin cewa wasu mahara sun shiga ƙauyen na Kurmin Wali tare da sace mutane kimanin 170 a yankin mai fama da matsalar tsaro.

Amma a ranar Litinin ɗin, sarkin Kurmin Wali, Ishaku Dan'azumi ya tabbatar wa BBC cewa maharan sun je ƙauyen ne a ranar Lahadi, inda suka sace mutane sama da 160.

"Sun zo ranar Lahadi wurin karfe 9, lokacin muna coci, suka bazu a garin, suka sa mu a tsakiya.

"Waɗanda suke a hannunsu yanzu 166," in ji Ɗan'azumi.

Shi ma shugaban ƙungiyar CAN a arewacin Najeriya Jospeh Hayab ya tabbatar wa kafafen yaɗa labarai batun sace mutunan a ranar ta Litinin.

Ya ce, "duk da cewa ban cika son ambata adadi ba, amma bayanan da na samu daga yankin na nuna cewa ƴanbindiga sun sace kusan mutum 172, amma guda 9 sun tsere sun koma gida, amma har yanzu ana neman mutum 163," in ji shi.

A ranar Litinin da dare ƴansandan suka fara fitar da sanarwa a kan batun, suna jaddada rashin bayanan da za su tabbatar da rahotannin da jaridun ƙasar da dama suka wallafa cewa an sace mutane fiye da 100 a wuraren ibadar su a ranar Lahadi, tare da kiran rahotannin a matsayin labaran bogi.

Sai dai a wata sanarwar ta daban da ƴansandan suka fitar cikin dare a ranar Talata, rundunar ta ce ba a fahimci sanarwarta ta farko ba ne, tana mai cewa dama can ta nemi a bayar da sahihan bayanai ne masu tabbatar da sunayen mutanen da aka sacen da kuma ƙauyukansu.

Kakakin rundunar ƴansandan Benjamin Hundeyin ya ce binciken da sashin tattara bayanan sirri na rundunar ya gudanar ya tabbatar masu cewa an yi garkuwa da mutanen.

Bai sanar da yawan mutanen da aka sace ba, amma ya ce rundunar ta tura jami'anta zuwa Kajuru da kewaye domin aikin gano wajen da ake tsare da mutanen da aka sace.

Tuni dai ƙungiyoyin fararen hula suka fara martani kan batun, inda ƙungiyar Amnesty International soki hukumomin Najeriya, waɗanda ta ce suna neman ɓoye haƙiƙanin abin da ya faru.

Ƙungiyar ta ce "Dole ne mahukunta su ɗauki matakan gaggawa domin hana ci gaba da garkuwa da mutane masu yawa da ke neman zama ruwan dare a Najeriya.''

Abin da mutanen Kurmin Wali suka ce

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wasu mazauna Kurmin Wali sun shaidawa BBC cewa mutane 177 aka yi garkuwa da su a coci-coci uku a garin. Kuma sun ce mutane 11 daga cikin su sun tsero daga hannun maharan, yayin da sauran 160 ke tare da su.

Wani jerin sunaye da BBC ta samu gani a ranar Talata na ɗauke da sunaye 160 da aka ce maharan sun yi garkuwa da su, sai dai babu wani bincike da ya tabbatar da gaskiyar hakan.

Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na safiyar Lahadi.

Ya ce "Wasu mutane sun yi yunƙurin tserewa amma sun gaza saboda yadda maharan ɗauke da makamai suka zagaye ƙauyen,''' Some people tried to run, but they couldn't because the armed men had surrounded the village," Ya ƙara da cewa "Sun tara mutane a waje ɗaya sannan suka shige daji da su.''

Mazauna ƙauyen sun ce an kai harin ne a coci-coci uku da suka haɗa da: Cocin Pentecostal Fellowship Assembly (PFA) ta ɗaya, da cocin Pentecostal Fellowship Assembly (PFA) ta biyu, da kuma cocin Evangelical Church Winning All (ECWA).