Su wane ne Sharifan Kano, kuma mece ce alaƙarsu da Annabi Muhammadu?

Asalin hoton, Ibrahim Salisu Ibrahim Al-Maghili/Facebook
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 6
A Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, da zarar an ce Sharifai, abin da ke zuwa ran mutane shi ne tsatso ko dangin Annabi Muhammad (S.AW.) waɗanda suka zamu mazauni a yankin yammacin Afirka.
Tarihi ya nuna cewa mutane masu wasu irin karamomi na musamman, amma karamar da ta fi girma da fice ita ce yadda ake cewa suna da wani iko a kan wuta, ko kuma a ce wuta ba ta kama su.
Su kansu al'umma ce daban-daban, daga mutane daban-daban da suka isa birnin na Kano tun shekaru aru-aru.
Sun samu tarba da karɓa mai kyau ne a Kano, wanda hakan ya taimaka wajen cigaba da zaman su, sannan suka hayayyafa, har ya zama yanzu suna da zuriya mai girman gaske.
Tun farkon zuwansu ne a sanadiyar karɓuwar da suka yi, sai suka riƙa auratayya da masu riƙe da sarautu da ƴan kasuwa na Kano, wanda wannan ma ya ƙara musu yaɗuwa da karɓuwa.
Asalinsu da zuwansu Kano
Domin sani. asalinsu da kuma zuwan su Kano, Dr Raliya Zubairu, ta sashen nazarin tarihi na Jami'ar Bayero da ke Kano, ta ce lallai tarihi ya nuna cewa suna da jiɓi da Annabi Muhammad, wanda shi ne annabin Musulunci wanda ya yi rayuwa a cikin karni na biyar bayan zuwan annabi Isa.
Bayani ya nuna cewa akwai gidaje daban-daban a tsakanin irin wadannan mutane.
"Akwai zuri'a daban-daban. Akwai zuriyar Muhammad Abdulkarim Al-maghili, akwai na Malam Abdurrahman Zaite da Malam Sharif Ujdud da sauransu," in ji ta Dr. Raliya.
Masaniyar tarihin ta ce suna da yawa, kuma akwai waɗanda suka shiga Najeriya daga Algeria da Sudan da Mauritania da Tunisia da Masar.
Ta ce sun samu karɓuwa sosai ne a Kano kasancewar suna karantar da addini ne, "sannan kuma da kasancewarsu jinin Annabi, ga kuma yadda Kanawa suke son Annabi, sai suka samu karɓuwa sosai."
Dr Raliya ta ce kasancewar su jinin Annabi, asalinsu zai zama Makkah ne da Madina. "Sun fito ne daga tsatson Nana Fatima ɗiyar Annabi, wato ta ɓangaren ƴaƴanta Hassan da Hussaini. Shi ne suka fara bazuwa zuwa ƙasashen duniya suna yaɗa addini."
Ta ce a haka suka fara isa ƙasashen yankin Afirka, "amma na fararen fata. Daga nan ne kuma suka gangara zuwa yammacin Afirka, lamarin da ya kai su ga zama a bir in na Kano.
Zuwan Sharifai Kano
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dr Raliya ta ce daga ƙasashen Larabawa na Afirka ne Sharifai suka fara zuwa Najeriya domin wa'azi da karantarwa.
Sai dai duk da cewa fitaccen Sharifin da aka fi sani a Najeriya shi ne Al-Maghili, masaniyar tarihin ta ce ba shi ba ne ya fara zuwa birnin Kano.
"Wanda tarihi ya nuna ya fara zuwa Kano shi ne Abdulrahram Zaiti daga Masar. Bayan shi ne Al-Maghili ya zo daga Algeria, Sai malam Ujdud daga Mauritania. Amma dukkansu asalinsu ɗaya ne."
Dr Raliya ta ƙara da cewa ba su ba ne suka kai Musulunci Kano, inda a cewarta, ƙara jaddada addinin suka yi.
"Kafin zuwansu akwai Musulunci a Kano. Musulunci ya isa Kano ne a ƙarni na 11, su kuma sun fara zuwa Kano ne a cikin ƙarni na 15 a zamanin Sarki Muhammadu Rumfa."
Ta ce a zamanin Malam Zaiti ne ya koyar da sarki yadda ake sallar idi, sannan ya koyar da shi, da wasu mutanen gari wasu abubuwan na addini.
"Sai daga bayan Al-Maghili ya shigo da littafai, musamman na shari'a, sannan ya rubuta littattafai na gudanar da masarautar Kano guda biyu, waɗanda har yanzu ana ci gaba da amfani da su," in ji ta.
A nasa bayanin, ɗaya daga cikin sharifan na Kano, Sharif Tijjani Ibrahim, daga majalisar Sarkin Sharifan Kano, Sidi Fari Abbas Adamu, ya ce su jinin Annabi ne, kuma kakanninsu sun isa Kano daga Gabas ta Tsakiya.
"Ka ga mu danginmu daga Algeria suka taso, wato Muhammad Abdulkarim Al-maghili. Abin da ya kawo su Kano shi ne yaɗa addinin Musulunci, kuma ya zo ne a bisa gayyatar Sarkin Kano Muhammadu Rumfa saboda ya warware wasu matsaloli na shari'a," in ji shi.
Imam Al-Maghili da nasabarsa da Annabi
Kabiru Sani Muhammad, mazaunin Unguwar Gwammaja da ke jihar Kano, marubuci ne wanda ya kasance cikin wasu masu bincike da suka gudanar da bincike har suka rubuta littafi kan tarihin Sharifai, musamman tarihin Al-Maghili.
A zantawarsa da BBC, ya ce an haifi Al-maghili a birnin Timisana na Algeria a shekara ta 820 bayan hijira.
Ya ce sunan mahaifiyarsa Ummul Masakin, wadda alkunya ce da ke nuna taimakon marasa ƙarfi, sai kuma sunan mahaifinsa Abdulkarim, wanda shi ma masanin addini ne.
Kabiru Sani ya ce nasabar Al-Maghili ita ce:
Sunansa Muhammad ɗan Abdalkarim ɗan Muhammad ɗan Makhlouf ɗan Ali ibn
al-Hasan ɗan Yahya ɗan Ali ɗan Ahmad ɗan Abdul-Qawi ɗan al-Abbas ɗan Adiyya ɗan Munad ɗan al-Sari ɗan Qais ɗan Ghalib ɗan Abubakar ɗan Abubakar ɗan Abubakar ɗan Abdullah ɗan Idris al-Saghir ɗan Idris al-Kabir ɗan Abdullah al-Kamil ɗan al-Hasan al-Muthanna ɗan Hasan al-Sibdi ɗan Ali ibn Abi Dalib da Fatima al-Zahra ƴar Annabi Muhammadu.
Al-Maghili a Kano

Asalin hoton, Fatihu Isa
Marubuci Kabiru Sani Muhammad ya ce Al-Maghili ya fara shiga Kano ne a lokacin Sarkin Kano Muhammad Rumfa kamar yadda Dr Raliya ta bayyana a tsakanin 1463 - 1499.
Marubucin ya ƙara da cewa a lokacin ne ya naɗa wani masanin Fiƙihu a lokacin, Malam Ahmad a matsayin limami, sannan ya naɗa Abdullahi wanda shi ma masani ne a matsayin alƙali.
An ce bayan ya tafi, ya bar ƴaƴansa uku a Kano - Ahmad da Sidi Fari da
Muhammad domin su ɗora daga inda ya tsaya.
Sannan uwa-uba ya rubuta littafi kan tsarin mulki a Kano, wanda har zuwa yanzu ake amfani da shi a birnin.
Haka bayan nan sun nuna cewa Imam al-Maghili ya shiga jihar Katsina a lokacin Sarki Ibrahim Maje a tsakanin 1599 zuwa 1613, inda ya kafa shari'ar Musulunci.
Khalifofin Al-Maghili daga 1499
Kamar yadda marubuci Kabiru ya bayyana, bayan tafiyar Al-Maghili, sai ya bar Sidi-fari a matsayin Khalifansa na farko.
Sauran khalifofin su ne:
- Sidi-fari Muhammad Hanatari Dan Imam Al-Maghili
- Isa Sidi Fari
- Zakariyya
- Abdulbaƙi
- Abdussadik ɗan Muhammad Hanatari
- Muhammad Al-mu'min
- Abdulkarim Katib Al-huruf
- Ahmad
- Ibrahim
- Muhammad Mai Nasara
Sarakunan Sharifan Kano bayan Shehu Ɗanfodio
Haka kuma bayan kafa daular Usman Ɗanfodio a Kano, an ci gaba da samun khalifofin Al-Maghili, wato daga shekarar 1807.
- Muhammad Mai Nasara ɗan Ibrahim Al-maghili ya rasu a 1822
- Sidi-Fari Musa ɗan Sidi Muhammad Mai Nasara ɗan Ibrahim Al- Maghili 1822- 1862 Sidi-Fari Adamu ɗan Sidi Muhammad Mai Nasara Al-Maghili 1862- 1899
- Sidi-Fari Muhammad Kwambo ɗan Sidi-Fari Adamu 1899- 1904
- Sidi-Fari Muhammad Amale ɗan Ja'far ɗan Muhammad Jaishu 1904- 1909
- Sidi-Fari Yusuf (Sarki) ɗan Sidi-Fari Musa 1909- 1936
- Sidi-Fari Abdullahi Hajj ɗan Sidi-Fari Musa 1936- 1938
- Sidi Fari Zakariyya (Ramadan) ɗan Sidi-Fari Adamu 1938- 1940
- Sidi-Fari Muhammad Bul-kasim dan Yusuf ɗan Sidi-Fari Musa 1940- 1954
- Sidi-Fari Isa ɗan Muhammad 1955- 1983
- Sidi-Fari Muhammad Awwal (Lawal) ɗan Zakariyya (Ramadan) 1983- 1999
- Sidi-Fari Yahya ɗan Isa (1999- 2014)/ Abdulmalik ɗan Zakariyya 1999- 2003
- Sidi-Fari Abbas ɗan Shariff Adam: Sarkin Sharifai daga 2015 zuwa yanzu
Sidi Fari Musa
Marubuci Kabiru Sani ya ce Sidi Fari Musa ɗan Sidi Muhammad ɗan Ibrahim ɗan ahmad ɗan Muhammad Mu'min ɗan Abdulsadiq ɗan Muhammad Hanatari ɗan Muhammad Abdulkarim Al -maghili.
Sidi Fari Musa ya kewaye birnin Kano wajen malamai daban-daban don samun ilimin addini.
Marubucin ya ƙara da cewa mahaifin Sidi Fari Musa, Sidi Muhammad Mai Nasara yana da alaƙa mai kyau da Sarakunan Kutumbawa wanda hakan ya sa bai shiga sahun masu jihadi. Bayan kafuwar Daular Usmaniyya a Kano, malaman sun cigaba da samun tasiri, don haka lokacin Sarkin Kano Dabo aka kafa tsarin farfaɗo da sarautu na lokacin mulkin Rumfawa.
"A tsakanin wannan lokaci ne Allah ya karbi ran Sidi Muhammad Mai-nasara, don
haka Sidi Fari Musa da ɗan'uwansa Sidi Fari Adamu suka cigaba da wannan
fafutuka har Allah ya tabbatar musu da Saruatar Sidi Fari da Sunan Sarkin
Sharifai."
Mece ce karamar sharifai?
A game da batun cewa suna da karamomi, da kuma uwa-uba cewa wuta ba ta kama su, Sharif Tijjani Ibrahim ya ce wannan wata baiwa ce da Allah yake ba su, inda ya ce ko ba ɗan zuriyyarsu ba, Allah zai iya ba wani wannan baiwar.
"Amma ba kowane Sharifi ba ne wuta ba ta kama shi," in ji shi.
Da take ƙarin haske kan karamomin Sharifai, Dr Raliya ta ce su ma mutane irin kowa, amma ta ƙara da cewa a cikinsu akwai masu baiwa.
"A gaskiya dai la'akari da tarihi mun yarda cewa su jinin Annabi ne. Matuƙar sharifin ne to jinin Annabi ne, sai dai idan ƙungiyar sharifan sun ce ba jininsu ba ne."
Ta ƙara da cewa tarihi ya nuna cewa sharifai suna da "wata izza ko nasara a kan wuta. Har yanzu sharifai suna bayar da maganin wuta ko gobara, wannan na cikin karamomi da wasu ke da su. Amma saboda juyawar zamani da fitintinu, wasu na rufa-ido na ƙarya."











