Bawa Jan-Gwarzo da alaƙarsa da Usman Ɗanfodio

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Isiyaku Muhammad
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
Daga cikin mutanen da ake yawan ambato da zarar an ambaci suna da jihadin Shehu Usman Ɗanfodio akwai Bawa Jan-Gwarzo, duk da cewa ba a cola bayyana asalin tasirinsa ga jihadin ba.
Bawa Jan-Gwarzo sarki ne da ya mulki masarautar Gobir daga shekarar 1777 zuwa shekarar 1795.
Asalin sunansa Malam Umar, amma an fi saninsa da laƙabin Bawa Jan-gwarzo, lamarin da masana tarihi suke alaƙantawa da jajircewarsa wajen yaƙi da ƙoƙarin tabbatar da abin da ya dace.
Domin tantance asalin rawar da ya taka wajen mulkin ƙasar Gobir, da ma irin rawar da ya taka a jihadin Usman Ɗanfodio, BBC ta zanta Farfesa Mukhtar Umar Bunza, wanda masanin tarihi da zamantakewa ne.
Masanin tarihin wanda a yanzu yake shugabantar Jami'ar North West da ke jihar Sokoto, ya ce Bawa Jan-Gwarzo bai samu matsala da Ɗanfodio ba, domin a cewarsa, shi ne wanda ya ƙarfafa shehun.
Mulkin Bawa Jan-Gwaro
Farfesa Mukhtar Bunza ya ce Bawa Jan-Gwarzo ne sarkin Gobir na 55, "sunan mahaifinsa Malam Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Gobir Babari, wanda shi ne Sarkin Gobir na 53."
Bunza ya ce ba a iya tantance asalin ranar da aka haifi Sarki Bawa Jan-Gwarzo ba, "amma dai ya zama sarki ne bayan rasuwar mahaifinsa da shekara shida," in ji masanin.
Bunza ya ce sarkin ya yi mulki a garin Alƙalawa, wato babban birnin ƙasar Gobir a wancan lokacin. "Mahaifinsa Sarki Babari ne ya kafa garin. Asalin gonar hutawar Sarkin Zamfara ce a lokacin, amma Sarki Babari ya aura wata ƙanwar sarkin na Zamfara, sai sarkin ya mayar masa da garin a ƙarƙashin Gobir."
Farfesan ya ce a garin ne Bawa Jan-Gwarzo ya rayu, ya yi sarauta, kuma a garin ya rasu, sannan aka binne shi.
"Amma yanzu garin ya zama kufai bayan da aka ci garin da yaƙi. Amma yanzu haka hukumar adana tarihi na yunƙurin mayar da shi garin tarihi mai muhimmanci," in ji Bunza.
Bunza ya ce sarkin ya samu yabo daga mutanensa, "saboda ya kwatanta mulki na adalci. Ya yi amfani da diflomasiyya da haɗin kai wajen jawo wasu da zama lafiya da wasu ƙasashen, amma ya yi amfani da ƙarfin soja a wuraren da ake buƙatar hakan."
Alaƙarsa da Ɗanfodio
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Farfesa Bunza ya ce ana yi wa Sarki Bawa kallon Mujaddadi na farko, "saboda shi ne ya fara yunƙurin faɗaɗawa da cigaban addinin Musulunci sannan shi ne ya ƙarfafa gwiwar Shehu Usman Ɗanfodio sosai domin ya samu nasara."
"Lokacin da Shehu ya fara wa'azi ya yi daidai ne da lokacin Bawa Jan-Gwarzo. A lokacin Shehu ya fi mayar da hankalin wa'azinsa ne a tsakanin Kebbi da Zamfara da Gobir."
Masanin tarihin ya ƙara da cewa tun asali Bawa Jan-Gwarzo ya samu laƙabin ne saboda jajircewarsa, "amma duk da ya girma shehu, sai ya kasance ya jawo shi jiki saboda iliminsa da kuma aminta da ya yi da ilimin Shehu Ɗanfodio."
Bunza ya ce da kansa sarkin ya je har garin Ɗagel wajen Shehu, sannan ya nemi ya koma garin Alƙalawa ya kafa makaranta.
"Shehu ya koma Alƙalawa, ya buɗe makaranta, sannna sarkin ya saka ƴaƴan gidan sarki, ciki har da Sarki Nafata da Sarki Yumfa a lokacin suna ƴaƴan gidan sarki. Sannan tun Shehu na Ɗagel ne sarkin ya kai masa gudunmuwar kusan shanu 50 domin faɗaɗa wa'azinsa da ƙarfafa masa gwiwa," in ji shi.
Bunza ya ce yadda Jan-Gwarzo ya kusantar da shehu da masarauta da sanya ƴaƴan sarki a makarantarsa ne suka sa shehu ya ƙara samun sauƙin gudanar da wa'azinsa da karatuttukansa.
Buƙatun Ɗanfodio ga Sarki Bawa Jan-Gwarzo
Farfesa Bunza ya ce akwai wasu buƙatu da Shehu Usman Ɗanfodio ya miƙa ga Sarki Bawa Jan-Gwarzo guda biyar, waɗanda a cewar masanin tarihin su ne suka zama gaba-gaba a cikin abubuwan da suka jawo jihadi daga baya, bayan Sarki Bawa ya rasu.
Abubuwan da shehu ya nema su ne:
- Damar wa'azi
- Bayar da damar amsa wa'azi ga wanda ya so
- Girmama alamun addinin irin su rawani da hijabi
- Rage haraji
- Sakin fursunonin yaƙi
Ya ce sarkin ya amince masa da buƙatunsa, "sannan kuma bai saɓa masa ba har ya bar duniya."
Saɓani da ƙasar Gobir
Kusan babban abin da yake jan hankali a game da tarihin Bawa Jan-Gwarzo shi ne sanin haƙiƙanin abin da ya jawo saɓani tsakanin Shehu Ɗanfodio da ƙasar Gobir, lamarin da Farfesa Bunza ya ce babu hannun basaraken.
A cewarsa, "Bawa Jan-Gwarzo ya rasu ne a shekarar 1794, sai ƙaninsa Sarki Yaƙuba ya yi sarauta ta shekara shida. Ba a fara samun matsala ba sai a zamanin Sarki Nafata da Sarki Yumfa."
"Abin da ya fara kawo matsala shi ne fara saɓa alƙawarin da Bawa Jan-Gwarzo ya yi wa Shehu a zamanin Sarki Nafata da Sarki Yumfa, kuma duk sun kasance tsofaffin ɗaliban makarantar Shehun."
Bunza ya ce a zamanin Sarki Nafata ne aka fara samun matsala, amma bai daɗe a sarauta ba, inda ya yi shekara biyu kacal.
"Da Sarki Yumfa ya karɓa mulki ne sai ya ƙara matsa lamba wajen taƙaita wa'azi, inda aka ce sai shehu ne zai yi wa'azi, aka fara taƙaita amfani da hijabi da ajiye gemu da sauransu."
Masanin tarihin ya ce izzar mulki ta taka rawa, "domin ka san ba kowane mai mulki ba ne yake so a samu wani a ƙasarsa yana da ƙarfin ikon faɗa a ji. Kuma irin ƙarfin da Sarki Bawa Jan-Gwarzo ya ba shehu, sai ya kasance yana da ƙarfi sosai a ƙasar Gobir."
"Daga baya Sarki Yumfa ya buƙaci Shehu ya yi hijira ya bar garin, inda ya koma can tsakanin Tangaza ta yanzu Gudu ya ci gaba da karantarwa da wa'azi. Yana can ne Sarki Yumfa ya kai masa hari. Shi ya dalilin daga baya jihadi ya kaure."











