Me ya sa ake muhawara kan sarautar sarkin Musulmi a Najeriya?

Sarkin Musulmin Najeriya, Sa'ad Abubakar III

Asalin hoton, Sultanate Council Sokoto

Majalisar dokokin jihar Sokoto za ta fara tattaunawa kan wani ƙudurin doka da ɓangaren zartaswar jihar zai gabatar mata, wanda tun farko gwamnatin ta ce zai yi gyara ne ga sashe na 76, kashi na biyu na dokar ƙananan hukumomin jihar.

Lamarin zai shafi ikon Sarkin Musulmi na naɗa hakimai da dagatai kai tsaye, inda ikon hakan zai koma hannun gwamnan jihar.

Sai dai lamarin na ta haifar da ce-ce-ku-ce.

A cikin jawabin da ya gabatar ranar Litinin, a wajen taro kan matsalar tsaron da ke addabar jihohin arewa maso yammacin ƙasar, wanda ke gudana a Katsina, mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya ce dole ne a kare martabar Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar III.

Shettima ya ce Sultan jagora ne na al'umma ba wai Sokoto kaɗai ba, don haka ya kamata a martaba shi a ko'ina.

"Sultan jagora ne da ya kamata dukkan mu a ƙasarmu kare domin ci gaban ƙasarmu," in ji Shettima.

Muna zura ido - MURIC

Ita ma ƙungiyar Kare Muradun Musulman Najeriya (MURIC) ta tsoma bakinta kan lamarin.

A wata sanarwa da ta fitar ta hannun shugabanta, Ishaq Akintola a ranar Litinin ta ce "al'umman Musulmi a Najeriya sun yi watsi da duk wani yunkuri na cire sarkin Musulmi".

"Idan gwamnan Sokoto ya ɗauki matakin tumɓuke Sultan, Musulman Najeriya za su ɗauki mummunan mataki domin hakan bai kamata ba," in ji Akintola.

"Ya kamata gwamnan ya sani cewa, Sultan Sa'ad Abubakar ba Sultan ne na Sokoto kaɗai ba, shugaba ne kuma ga al'umman Najeriya. Yanayin jagorancinsa da kuma ƙoƙarinsa ya sanya shi soyuwa cikin zukatan ƴan Najeriya," a cewar shugaban na MURIC.

Me ya haifar da muhawarar?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A taronta na biyar cikin wannan shekara ta 2024, majalisar zartaswar jihar Sokoto ta amince da yin gyara ga dokar ƙananan hukumomin jihar ta shekara ta 2008.

A lokacin da ya yi jawabi ga manema labarai bayan taron, kwamishinan albarkatun ruwa na jihar, Yusuf Muhammad Maccido ya ce: "akwai wani kuduri da aka gabatar a majalisa yau wanda ya shafi yin gyara ga dokar kananan hukumomi ta jihar Sokoto ta shekara 2008, a karkashi. Sashe na 76 kashi na biyu, wanda ya shafi nada uwayen kasa da hakimai a jihar Sokoto, wanda aka daidaita shi ga yadda yake inda aka fito.

“Tsarin shi ne, majalisar sarkin Musulmi za ta gabatar da bukata ga gwamna domin nada wadanda ake so a matsayin uwayen kasa da kuma hakimai, shi me yadda tsarin yake.

Amma dokar 2008 ta nuna cewa damar nafi tana ga sarkin Musulmi, wanda kuma ga yadda abin yake damar yin nadi tana ga gwamna ne”.

Kwamishinan ya kara da cewa za a koma taarin da ake bi kafin shekara ta 2008 da zarar majalisar dokokin jihar ta amince da kudurin.

Wani na kusa da masarautar Sarkin Musulmin ya shaida wa BBC cewa tabbas gabanin shekara ta 2008 Sultan na gabatar da sunayen waɗanda ake son nadawa a matsayin iyayen ƙasa da hakimai ne ga gwamna, inda gwamna ke da damar ya amince da naɗin ko kuma a’a.

A cewarsa hakan ya samo asali ne tun zamanin mulkin turawa, inda sarkin Ingila ne kawai ke da damar amincewa a naɗa duk wani muƙami na sarauta, sai dai a wasu lokuta baturen 'razdan' na Sokoto, wanda ke a matsayin gwamna a wancan lokacin shi ne ke amincewa da irin waɗannan naɗe-naɗe.

To amma a shekara ta 2008, gwamnan jibar Sokoto na wancan lokaci Aliyu Magatakarda Wamako ya sa an yi wa dokar gyaran fuska, inda aka bai wa sarkin Musulmi damar naɗa duk wanda ya cancanta a irin waɗannan mukamai kai-tsaye.

Abin da ya sa ake fargaba

A cikin bayanin nasa, makusancin na fadar sarkin Musulmi ya ce babban dalilin da ya sa ake ta muhawara kan lamarin shi ne domin gudun kada hakan ya zamo tushen wani 'babban al’amarin' da ya fi wannanmatakin a nan gaba.

Ya ce “ana gudun kada wannan mataki ya zama soman-tabi ne na abin da zai iya zuwa a gaba”.

Amma baya ga haka, a cewarsa, wannan ba wani abu ba ne kasancewar dama tun asali haka dokar take.

“Gaskiyar ala’amari shi ne ba wata sabuwar doka ba ce, za a koma tsarin da ake amfani da shi ne a baya.”

Gani ga wane...

Sai dai wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake kika-kaka game da naɗi da kuma sauke sarakai a Kano, ɗaya daga cikin masarautun ƙasar Hausa masu daɗaɗɗen tarihi.

Inda a ranar 23 ga watan Mayun da ya gabata, gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautar Kano.

Sabuwar dokar ta rushe sabbin masarautu biyar da tsohuwar gwamnatin jihar ta Abdullahi Ganduje ta ƙirƙira a ƙarshen shekarar 2019 bayan yi wa dokar masarautar Kano gyaran fuska.

Haka nan sabuwar dokar ta warware naɗin dukkanin sarakunan masarautun jihar tare da mayar da Muhammadu Sanusi II kan karagar mulki bayan sauke shi da aka yi a watan Mayun 2020.

Lamarin da har yanzu ake ta tafka shari'a a kai.

Wane hali dokar da za a yi wa gyara ke ciki?

Daya daga cikin jagororin Majalisar dokikin jihar Sokoto ya bayyana cewa ba a riga an gabatar da kudurin yin gyara ga dokar nadin sarautun ba a zauren majalisa kasancewar suna hutu.

Sai dai a cewar sa babu masaniya ko za a gabatar da dokar a ranar Talata, sa’ilin da majalisar za ta koma zama, a cewarsa a wannan lokaci me kawai za a tantance abin da dokar ta kunsa da kuma gyaran da majalisar za ta yi.

Wani abu da ke kara rura wutar muhawarar shi ne matakin da gwamnan jihar Ahmad Aliyu ya dauka na sauke hakimai 15 daga kan mukamansu a cikin watan Afrilu.

Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar a tanar 23 ga watan Afrilun 2024 - wadda ta samu sa hannun sakataren yada labarun ofishin gwamnan jihar, Abubakar Bawa, ta ce an sauke su ne bisa dogaro da shawarwarin kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin sake duba nade-naden sarauta da sanya wa kadarorin gwamnati suna.

Sanarwar ta ce hakiman da abin ya shafa sun hada da na Unguwar Lalle, Yabo, Wamakko, Tulluwa, Illela, Dogon Daji, Kebbe, Alkammu, and Giyawa.

Sai kuma Marafan Tangaza, Sarkin Gabas Kalambaina, Bunun Gongono, Sarkin Kudun Yar Tsakkuwa, Sarkin Tambuwal da kuma Sarkin Yamman Torankawa, wadanda wasunsu aka zarge su da rashin biyayya ga gwamnati da ingiza wutar rashin tsaro da mallakar kadarorin gwamnati ta haramtacciyar hanya.

Sai kuma wadanda aka ce an kora sanadiyyar rashin bin ka’ida wajen nadinsu ko kuma rashin samun karbuwa tsakanin al’ummarsu.

Martanin gwamnatin Sokoto

Sai dai a wani martani da ta mayar, gwamnatin jihar Sokoto ta ce dokar da za ta gabatar wa majalisar dokoki ba wani abu za ta yi ba face mayar da tsarin naɗin hakimai da dagatai zuwa yadda ya kasance tun fil-azal.

Sanarwar wadda ta samu sa hannun kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Sambo Bello Danchadi ta ce “Dokar kawai za ta sake dawo da tsarin da ake amfani da shi ne a gomman shekaru da suka gabata”.

Sai kuma ta ƙara da cewa “alaƙa tsakanin gwamnati da masarautar Sarkin Musulmi alaƙa ce mai kyau kuma za ta ci gaba da kasancewa a hakan”.

Haka nan sanarwar ta gargaɗi mutane da su daina yaɗa jita-jita kan cewa an shirya dokar ne domin yin zagon ƙasa ga fadar sarkin Musulmi.