Kalaman Sarkin Musulmi da Janye tallafin wutar lantarki
Ana neman wadanda suka fitar da dala miliyan shida da sa-hannun bogi na Buhari

Asalin hoton, Buhari
Mai bincike na musamman da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya nada ya bukaci hukumar yan sanda ta kasa da kasa wato interpol ta sanya ido kan wani ma'aikacin babban bankin Najeriya CBN da wasu mutum biyu.
Matakin ya zo ne bayan bankado wasu takardun bogi da sunan tsohon shugaba Muhammadu Buhari na zargin satar dala miliyan shida da dubu dari biyu kafin babban zaben 2023.
Tun farko wani tsohon sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha ya shaida wa babbar kotu a Abuja kamar yadda jaridar DailyTrust ta rawaito cewa takardun da aka yi amfani da su wajen biyan masu sa ido a zaben dala miliyan shida da dubu dari biyu na boge ne.
Tsohon sakataren gwamnatin Najeriyar ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana a matsayin shaida ta hudu a shari'ar da ake yi kan tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, bisa zargin karkatar da dala miliyan shida da dubu dari biyu.
Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin lantarki ba

Asalin hoton, NIGERIA ELECTRICITY
Ministan lantarki na Najeriya, Adebayo Adelabu, ya ce ƙasar ba za ta iya ci gaba da biyan kuɗin tallafin wutar lantarki ba.
Ya ce dole ne ƙasar ta fara ɗaukar matakai don magance basukan da kamfanonin samar da wutar ke bin gwamnati, inda a yanzu ya ce bashin da kamfanonin ke bin gwamnatin ƙasar ya kai naira tiriliyan 1.3, waɗanda su kuma kamfanonin samar da gas ke binsu bashin naira biliyan 1.3.
Mista Adelabu, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gabatar a Abuja, ya ce kasafin kuɗin wannan shekara ya ware naira biliyan 450 don biyan tallafin, a yayin da ma'aikatar lantarkin ke buƙatar fiye da naira tiriliyan biyu don biyan tallafin.
Ya ƙara da cewa a yanzu za a bai wa gwamnatocin jihohi damar samar da wutar kansu don raba wa jihohin nasu.
Najeriya na kan tsini - Sultan Sa'ad

Asalin hoton, other
Mai alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bayyan afargabar cewa Najeriya na fuskantar barazanar tsaro bisa la'akari da yadda dumbin matasan kasar ke fama da rashin aikin yi da yunwa.
Sarkin Musulmin ya yi wadannan kalamai ne yayin da yake jawabi a wani taron majalisar sarakunan gargajiya ta arewacin Najeriya ranar Laraba a Kaduna.
Muhammad Sa'ad Abubaakr III ya ce " mun shiga wani sabon zango na shugabanci. An samu sabbin gwamnoni inda kuma wasu suka yi tazarce a karo na biyu amma har yanzu muna fama da matsalar tsaro.
Babban matsalar ma ita ce karuwar talauci. Mafi yawancin mutanenmu ba su da hanyoyin samun abin da za su ci su sha".
Ya kara da cewa idan dai har gwamnoni na son zaman lafiya a jihohinsu, dole ne su sama wa matasa aikin yi sannan dole ne su yi aiki tare da sarakunan gargajiya.
Ƙungiyar Ƙwadago ta kira zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC ta ayyana gudanar da gagarumar zanga-zangar kwana biyu a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu.
Shugaban ƙungiyar Kwamared, Joe Ajaero, ne ya bayyana haka a shalkwatar ƙungiyar lokacin wani taron gaggawa da ƙungiyar ta kira ranar Juma'a.
Mista Ajaero ya ce an ɗauki matakin zanga-zangar ne bayan ƙarewar wa'adin kwanaki 14 da ƙungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya kan tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.
Ƙungiyar dai ta bai wa gwamnati wa'adin ne domin da ɓullo da wasu sauye-sauyen da za su magance matsalolin da 'yan ƙasar ke fuskanta sakamakon matsain rayuwa.
Sojojin Najeriya sun kashe 'ƴan ta'adda' 254 cikin mako ɗaya

Asalin hoton, XNigeria
Sojojin Najeriya sun ce sun kashe 'ƴan ta'adda 254 tare da kama guda 264 a ayyukan da ta gudanar cikin mako ɗaya a faɗin ƙasar.
Daraktan yaɗa labaru cibiyar tsaro ta Najeriya, Mano Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labaru a yau Juma'a.
Ya ce "shirye-shiryen da muke aiwatarwa na yaƙi da ƴan ta'adda da masu tayar da ƙayar baya ya hana masu aikata miyagun laifuka cimma manufofinsu."
Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro a kowane ɓangare na ƙasar.
Zulum ya ce al'ummar Borno su yi azumi don neman sauƙin rayuwa

Asalin hoton, X/Borno Gov
Gwamnatin Jihar Borno ta buƙaci al'ummar jihar su yi azumi a ranar Litinin 19 ga watan Fabrairu, domin neman sauƙin ubangiji dangane da tsadar kayan abinci da fashewar abubuwa a wasu manyan titunan jihar.
Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi kafar yaɗa labaran jihar.
“Ina magana da ku a yau cikin tsananin takaici, amma ina da yaƙinin cewa za mu iya magance matsalolin da ke addabar jiharmu'', na damu matuƙa da halin matsin rayuwa da al'ummar jiharmu ke fuskanta, musamman tsadar kayan abinci'', in ji Zulum.
Gwamnan ya ci gaba da cewa a gwamnatance suna ɗaukar matakan da suka dace don magance matsalar.











