Yaƙin Iran na ci gaba da ingiza tashin farashin kaya a Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Farashin kayan masarufi ya yi tashin da bai taba yi ba cikin shekara uku a Amurka sanadiyyar tashin farashin makamashi.
Farashin ya tashi da kimanin kashi 18% a watan Afrilu, kuma ana alaƙanta hakan da yaƙin da Amurkar ke yi a Iran.
Haka nan farashin abinci da na gidaje shi ma ya tashi, kamar yadda aka samu irin hakan a harkar sufurin jiragen sama da kuma farashin sutura.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana sa ran farashin mai zai sauka da zaran aka kawo ƙarshen yaƙin.













