Mutanen da ya kamata su yawaita cin ƙafar kaza

x

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Shin ka taɓa tunanin amfanin cin ƙafar kaza?

Mutane da yawa suna tunanin ƙafar kaza ba ta da wani amfani, amma a ƙasar Singapore, ƙafar kaza na da matuƙar muhimmanci.

Kowane kilogram na ƙafar kaza ana sayar da shi ne a farashin dala huɗu, wanda ya kai kimanin sama da naira 5,000.

A ƙasashe irin su Afirka ta Kudu da Mexico, ƙafar kazar takan fi asalin naman kazar tsada.

Ana rububin ƙafar kaza a ƙasashen duniya. Ƙasashe irin su Vietnam da China da Uzbekistan duk suna shigar da ƙafar kaza daga ƙasashen duniya.

A shekarar 2022, Amurka ta shigar da kusan tan 133,000 na ƙafar kaza daga ƙasar China.

Shin me ya sa ƙafar kaza, abin da ake watsarwa kuma ake ganin ba ta da amfani ke da muhimmanci a wasu ƙasashen duniya? shin waɗanne sinadarai ne suke ƙunshe a cikin ƙafar kaza?

Sinadaran da ake samu a ƙafar kaza

Cagaha digaagga

Asalin hoton, Getty Images

Duk da cewa mutane da dama na kallon ƙafar kaza a matsayin maras muhimmanci, to amma binciken cibiyar nazarin lafiya ta Amurka ya nuna cewa ƙafa kaza na ƙunshe da alfanu mai ɗimbin yawa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amurka ce ta fi samar da kajin turawa tsakanin ƙasashen duniya, inda ake fitar da kashi 15% na kajin da ake kiwo a ƙasar zuwa ƙasashen waje.

Hakan ya ƙunshi ƙafar kaza mai ɗimbin yawa.

Sanannen tsohon ɗan ƙwallon Ingila Andros Townsend ya taɓa shaida wa BBC cewa: "Ƙafar kaza ba ta da tsoka amma ta fi kowane ɓangare na jikin kaza daɗi.

Ana cin ƙafar kaza sosai a ƙasashe irin su China da Afirka ta Kudu da Portugal.

Wani bincike da aka gudanar ya ce ƙafar kaza ta ƙunshi fata da ƙashi da jijiya, kuma ƙafar ta ƙunshi sinadarin 'collagen' har kashi 30% zuwa 35%.

Ƙafar kaza na ƙunshe da sinadarai masu gina jiki da maiƙo da sinadarai masu samar da ƙarfi da kuma ƙarfin ƙashi, sai kuma sinadaran 'vitamin A da B9'.

Wata ƙwararriya kan abinci Dr Sri Vidya ta ce kashi 70% na sinadarin gina jiki na protein da ke ƙunshe a ƙafar kaza 'collagen' ne.

'Collagen' sanadari ne da ake samu a cikin jikin bil'adama, inda ake samun shi a cikin fata da ƙashi da jijiya da kuma tsakankanin gaɓoɓi.

x

Asalin hoton, Getty Images

To sai dai yayin da mutum ke ƙara tsufa, yawan sinadarin 'collagen' da yake samarwa na raguwa.

Dr. Srividya ta ce a saboda haka jikin ɗan'adam na zuƙar sinadarin 'collagen' na cikin ƙafar kaza cikin sauƙi.

Sinadarin 'collagen' na taka muhimmiyar rawa wajen lafiyar fata da ƙasusuwa.

Ta ce gazawar jiki wajen samar da isasshen sinadarin collagen a lokacin tsufa ne ke haifar da tamuƙewa da bushewar fata. Haka nan lamarin na shafar lafiyar mahaɗar gaɓoɓi.

Likitar ta ce a saboda haka sinadarin na collagen wanda ake samu a ƙafar kaza na taimakawa sosai ga lafiyar fata da ƙashi da gaɓoɓi da kuma ƴan hanji.

Wani nazari da aka yi kan masu fama da lalurar ciwon gaɓoɓi na 'arthritis' ya nuna cewa samun ƙarin sinadarin collagen na taimakawa wajen rage munin ciwon.

Yadda ya kamata a ci ƙafar kaza

 Dr. Sri Vidya

Asalin hoton, Dr. Sri Vidya

Bayanan hoto, Dr. Sri Vidya

Dr. Srividya ta ce yana da muhimmanci a wanke ƙafar kaza da kyau kafin dafawa kasancewar ƙafar kaza na cin karo da abubuwa da dama na ƙazanta, waɗanda ta ce taɓa su ko kuma cin su zai iya zama mai haɗari ga lafiya.

Ta ce baya ga wankewa da kyau, yana kuma da muhimmanci a kware fatar sannan a dafa ta da kyau.

Rashin dafa ƙafar kaza da kyau zai iya bayar da dama ga ƙwayoyin cuta irin su 'salmonella' da 'campylobacter' su shiga jikin bil'adama su haifar da cuta.

Farfesa Ono Suparno na jam'iar IPB ya ce ya fi kyau a yi amfani da ƙafar kaza wajen yin miya, kamar yadda ake yin farfesun ƙafar akuya.

Dr. Srividya ta ce kasancewar jiki na buƙatar a dafa ƙafar kaza kafin ya iya tsotse sinadaran da ke cikinta, yana da kyau kuma a riƙa shan romon ƙafar.

Ta ce ana iya yin miyar ƙafar kaza mai romo, amma bai kamata a soya ƙafar ba.

Ta bayyana cewa soya ƙafar kaza na iya zama mai haɗari ga lafiya saboda suna ɗauke da daskararren maiƙo da sinadarin sodium wadanda ke da haɗari ga lafiyar zuciya.

Su wane ne ya kamata su yawaita cin ƙafar kaza?

Cagaha digaagga

Asalin hoton, Getty Images

Dr. Srividya ta ce sinadarin 'vitamin B9' da ke ƙunshe a ƙafar kaza na taimakawa wajen girman jariri a cikin mahaifa, amma ya kamata a tantance yawan ƙafar kazar da za a ci.

Ta ƙara da cewa kowane mutum zai iya cin ƙafar kaza huɗu ko biyar, wat kimanin giram 100 zuwa giram 150, wanda aka dafa ko a ka yi farfesun ta.

Ta ce ya kamata a nuna wa yara cewa suna buƙatar tauna ƙafar sosai kafin su haɗiye.

Bai kamata a bai wa yaran da ba su fara haƙori ƙafar kaza ba, haka nan ma manya wadanda ba su da lafiyar hakori.

Ta yi gargaɗin cewa ƙafar kaza za ta iya maƙalewa a makoshi idan ba a tattauna ta yadda ya kamata ba, wanda hakan zai iya kawo hatsari ga lafiya, sannan ta buƙaci mutane su tuna cewa ƙafar kaza na ƙunshe da maiƙo sosai.