Matsalar da cin jan nama da yawa kan haifar wa mutum

Ciwon gout kan haddasa raɗaɗi da kjumburi a gaɓɓan ɗan Adam
Bayanan hoto, Ciwon gout kan haddasa raɗaɗi da kumburi a gaɓɓan ɗan Adam
    • Marubuci, Hamet Fall Diagne da Papa Atou Diaw,
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afrique

Souleymane Sy, tsohon ma'aikacin gwamnati ne. Yanayin tafiya da takunsa kan sa a gane shi daga nesa.

Mutumin na fama ne da ciwon gaɓɓai na gout - wanda cin jan nama ke haifarwa. Cuta ce da ke samar da sinadarin uric mai yawa a jinin ɗan Adam, kuma yana faruwa ne sakamakon ruɓewar sinadarai a jikin mutum da ake kira purine da Ingilishi.

Akan samu purine a cikin abincin dabbobi da kuma saiwar tsirrai. Kazalika, an fi samun sa a cikin jan nama da kifi samfurin sadin da ababen maye da lemuka masu zaƙi da sauransu.

Jan nama, abu mai haɗari

Shi dai Souleymane ba wani abu ne ya saka shi cikin matsala ba illa jan nama.

"Ina yawan cin jan nama a lokacin. Idan na samu lokacin hutu a wajen aiki, kodayaushe za mu tafi wurin mai nama mu ci kusan kilo ɗaya. Ka ga kuwa muna ɗiban nama da yawa. Na ci nama mai yawa kuma ina fama da sakamakon hakan," a cewar Souleymane Sy.

Wani lokaci Souleymane kan yi nadamar cin nama mai yawa. Sai dai ba abu ne mai sauƙi ba mutum ya kauce wa cin nama a ƙasarsa ta Jamhuriyar Nijar. Nama muhimmin ɓangare ne na abincin yau da kullum a ƙasar.

Lokacin da yake matashin ma'aikacin gwamnati, Souleymane bai taɓa wuce tayi ba idan ya ga kilishi. Shi ma kilishi shahararren abin ƙwalama ne a Nijar.

kilishi
Bayanan hoto, Kilishi shahararren nama ne a Nijar da ake ci don ƙwalama

Sinadarin purine da ake samu a abincin dabbobi ba shi kaɗai ne mafi haɗari ba wajen kamuwa da ciwon gaɓɓai na gout ba.

A cewar wani likitan ƙoda a Nijar, Dr Alassane Amadou Seydou: "Akwai hanyoyi da ake iya kamuwa da wasu cutuka masu alaƙa da jini, kamar kansar jini kuma jinyarsu kan kai ga harbuwa da ciwon gout.

Sauran hanyoyin na da alaƙa da shan wasu ƙwayoyi kamar waɗanda ake bai wa masu fama da tarin fuka ko ciwon zuciya."

Ciwon Souleymane ya ta'azzara ta yadda aka samu wasu tsokoki sun tsiro a gaɓɓansa, abin da ya haddasa masa rashin jin daɗi. Bayan rashin barci da yake fama da shi da dare, kazalika yana shan wahala wajen yawatawa.

Hakan ya jawo gaɓɓansa suka kumbura, abin da ake kira tophi, musamman a gwiwar hannunsa.

Kumburi a gaɓɓai na haddasa rashin jin daɗi a jikin mutum
Bayanan hoto, Kumburi a gaɓɓai na haddasa rashin jin daɗi a jikin mutum

Sukan haddasa raɗaɗi a cikin ƙashi. Zugi da raɗaɗin kan faru ne cikin dare musamman a tafinb ƙafa.

A cewar Farfesa Abdou Niang: "Zafin yana da tsanani sosai ta yadda mutum ba zai so ko takarda ta taɓa shi ba."

Ciwon gaɓɓai na gout ya fi shafar maza manya. Sai dai su ma mata kan kamu da shi.

Ba a fiya gane alamun ciwon gout ba saboda raɗaɗinsa yana da tsanani sosai.

"Duk sanda mutum ya kamu da ciwon gout ba zai taɓa mantawa da raɗaɗinsa ba," in ji Farfesa Niang.

Haka nan, ciwon kan shafi musamman gwiwa, abin da kan jawo likita ya buƙaci a maras lafiyar ya ɗauki hoton wurin domin gano matsalar.

'Na sayar da kusan komai nawa'

Ciwon ya shafi tattalin arzikin Souleymane. Ya sayar da kadarorinsa wajen jinya saboda ba shi da inshorar lafiya.

"Saboda neman lafiya, dole na sayar da wasu kadarorina...na sayar da motata da gidana. Saboda ina da wani gidan, shi ma na sayar da shi. Duk da haka har yanzu babu wani cigaba," in ji shi. Amma ya ci alwashin ƙarar da duk abin da ya mallaka don ganin bayan ciwon da ya hana rayuwarsa sakat.

Souleymane Sy
Bayanan hoto, Souleymane Sy

Ya yi ƙoƙarin bin umarnin da likitansa yake ba shi, wanda ya ce ciwon bai fi ƙarfin magani ba.

"Ciwo ne da ake iya warkewa amma irin nasa dole ne mutum ya mayar da hankali kan nau'in abincin da yake ci a lokaci-lokaci," a cewar Dr Seydou.

"Muna bai wa masu ciwon gout shawarar cewa su guji cin nama. Idan muna magana kan jan nama har kilishi ma yana ciki. Haka ma wake da kabeji, duka don a guji ƙara yawan sinadarin uric a cikin jiki. Muna bayar da shawarar mutum ya dinga cin kayan hatsi da kuma na marmari."