Hukunce-hukuncen da suka shafi azumin matafiya

Wasu maniyyata daga Najeriya zuwa Saudiyya

Asalin hoton, Nahcon

    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 3

Duk da kasancewar azumin watan Ramadana wajibi ga mabiya addinin Musulunci, akwai rangwame da aka yi wa matafiya, inda suke da zaɓin ajiye azumin a halin balaguro.

Azumin Ramadana rukuni ne daga cikin rukunnan Musulunci biyar, wanda ya haɗa da kaɗaita Allah, da amincewa da Annabi Muhammadu a matsayin manzon Allah, da yin sallah, da bayar da zakka, da kuma aikin Hajji ga wanda ya samu iko.

Musulamai kan shafe tsawon wuni ba tare da ci ko shan wani abu ba tsawon kwana 29 ko 30 a wata na tara na kalandar Hijira.

Akwai rukunnai na mutane da kuma yanayi da ake yi wa rangwame, cikinsu har da matafiya.

Wace irin tafiya ce za ta sa mutum ya ajiye azumi? Sannan yaushe ya kamata ya rama?

Mun tambayi malamai domin amsa waɗannan da ma wasu tambayoyin.

Shin ajiye azumi wajibi ne ga matafiyi?

Sauƙin da aka bai wa matafiya na ajiye azumin Ramadana ya samo asali ne daga ayar Al-Ƙur'ani da ta ce maras lafiya ko matafiyi zai iya ajiye azumi, kamar yadda Dr. Yahaya Gwani Yahuza, malami a sashen darussan Musulunci na Jami'ar Bayero, ya shaida wa BBC.

"An bai wa mutane wannan damar ce da zimmar zai rama azumin a wani lokaci nan gaba," in ji shi.

Sai dai malamai sun yi saɓani ka ko dole ne matafiyi ya ajiye azumi yayin balaguro.

"Wasu malamai na gani dole ne mutum ya ajiye azumi idan zai yi tafiya. Sun kafa hujja da hadisin Annabi Muhammadu (SAW) da ya ce 'ba shi daga cikin ɗa'a mutum ya yi azumi a lokacin tafiya,'" a cewar Dr Yahaya.

"Sai dai mafi yawan malamai na ganin ajiye azumi sauƙi ne daga Allah. Wanda ya ajiye ya kyauta, wanda kuma ya yi azuminsa bai yi laifi ba."

A gefe guda kuma, Sheikh Idris Mainasara Gandun Albasa ya ce idan aka yi la'akari da ayar Al-Ƙur'ani, za a ga cewa "yin azumi ya fi alheri ga matafiyi".

"Sai dai kuma ajiye azumi sassauci ne da Allah ya bai wa mutum, kuma Allah na son idan ya bayar da sassauci a karɓa. Matuƙar mutum ya san zai sha wahala ko yaya ne a tafiyar, to yana da dama ya ajiye," a cewar malamin daga jihar Kano.

Wace irin tafiya ce aka yarda mutum ya ajiye azumi?

Wasu matafiya

Asalin hoton, EPA

Fatawowin da malaman addinin Musulunci suka bayar ta nuna cewa ba kowane balaguro ne ko tafiya suka cancanci mutum ya ajiye azumi ba.

Dr. Yahaya ya ce za a ajiye ne kawai a tafiyar da ta dace a yi wa ƙasaru - wato taƙaita salla mai raka'a huɗu zuwa raka'a biyu.

"Tafiyar da ta cancanci a yi wa ƙasaru kuma ita ce mai tsawon kilomita 83, ko kuma mil 43," a cewarsa.

Shi ma Sheikh Mainasara ya tabbatar da hakan, inda ya ce "duk wanda zai yi tafiyar da ta kai kilomita 80 zuwa sama zai iya ajiye azumi.

Yaushe ne matafiyi zai ajiye azumin?

Akwai yanayin da mutun zai shiga na ƙila waƙala game da yiwuwar tafiyar tasa. Sheikh Mainasa ya ce a irin wannan yanayin mutum ba zai ajiye azumi ba.

"Sai mutum ya fara tafiya zai ajiye azumi. Da ma ko sallar ƙasaru, an ce sai mutum ya wuce gonakin garinsu sannan zai fara yin ta.

"Saboda haka, ba wai tun daga lokacin sahur mutum zai ɗauki niyyar ajiye azumi ba. Za a ɗauki azumi har sai tafiya ta tabbata tukunna, har ma sai mutum ya je tashar jirgi ko mota, an fara tafiya sannan zai ajiye azuminsa."

Da wane lokaci matafiyi zai yi aiki wajen buɗe-baki?

Akan samu lokutan da matafiyi zai bar ƙasarsu bayan an ga watan sallah - ma'ana an gama azumi baki ɗaya - amma ya isa ƙasar da ya nufa kuma ya tarar ba a ga watan ba. Me mutum ya kamata ya yi a irin wannan yanayi?

Dr. Yahaya ya bayar da amsa da cewa: "Ɗaya daga cikin sharuɗɗan azumin Ramadana shi ne niyya, shi kuma bai ɗauki niyyar yin azumi ba.

"Saboda haka hukuncinsa shi ne, zai kame bakinsa ya ci gaba da azumi, kuma zai ajiye azumin ne tare da mutanen garin da ya je, ba in da ya baro ba.

"Idan kuma ya tarar sun ajiye azumi suna yin Idi a daidai lokacin da shi kuma azuminsa bai kai 29 ba, to zai yi ajiye azumin sannan kuma ya rama sauran bayan sallah."

Kazalika, wannan hukuncin ya shafi wanda ya bar ƙasarsu bayan an sha ruwa kuma ya isa ƙasar da rana ba ta fadi ba.

Shin hukuncin ɗaya ne da matafiyi a jirgi?

Malamai sun ce babu bambancin hukunci game da abin da aka yi amfani da shi wajen yin balaguro.

"A tasari na Musulunci, da wanda yake tafe a jirgi, da na mota, da na dabba, indai ya cika sharaɗin kasancewarsa matafiyi to hukuncin iri ɗaya," in ji Sheikh Mainasara.

Shi ma Dr. Yahaya ya tabbatar da hakan. "Abu mafi muhimmanci dai shi ne ya zamana ya cika sharaɗin yin tafiyar," a cewarsa.