Wane ne Mojtaba Khamenei, sabon sabon jagoran addinin Iran?

Hoton Mojtaba Khamenei da gidan talabijin na Iran ya nuna bayan zaɓen shi a matsayin sabon jagora

Asalin hoton, IRINN

Bayanan hoto, Hoton Mojtaba Khamenei da gidan talabijin na Iran ya nuna bayan zaɓen shi a matsayin sabon jagora
Lokacin karatu: Minti 3

Majalisar ƙwararru ta ƙasar Iran ta zaɓi Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addinin na ƙasar, wanda zai gaji mahaifinsa Ayatollah Ali Khamenei.

An sanar da hakan ne a gidan talabijin na gwamnatin ƙasar ta Iran, inda wani mai gabatar da labarai ya karanta sanarwar.

Ya ce: "Duk da matsanancin halin da ake ciki na yaƙi da kuma barazana daga maƙiya ga wannan hukuma, haka nan duk da jefa bamai-bamai a ofisoshin wannan majalisa ta ƙwararru, lamarin da ya kai ga shahadar mambobinta da dama da na ɓangaren tsaro, ba ta tsaya ba ko da na daƙiƙa ɗaya a ƙoƙarinta na zaɓe da kuma gabatar da jagorancin tsarin Musulunci."

Daga nan sai mai sanarwar ya ce "Allahu Akbar, Allahu Akbar, Khamenei shi ne jagora."

Bayanan da ke nuna cewa Mojtaba zai iya gadon muƙamin mahaifin nasa sun daɗe suna yawo tun bayan kashe mahaifin nasa a harin da Amurka da Isra'ila suka kai a ranar Asabar, sai dai tabbacin bai zo ba sai da tsakar daren Litinin agogon Tehran.

Shi ne jagoran addinin Iran na uku, kuma na farko da ya gaji mahaifinsa.

A baya shugaban Amurka Donald Trump ya buƙaci kasancewa cikin waɗanda za su zaɓi magajin Ali Khamenei.

Wane ne Mojtaba Khamenei?

An haifi Mojtaba ne ranar 8 ga watan Satumban 1969 a garin Mashhad, kuma shi ne na biyu a cikin ƴaƴan Ali Khamenei shida.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya yi karatunsa na sakandare ne a makarantar addinin Musulunci ta Alavi da ke birnin Tehran.

Lokacin da ya kai shekara 17, Mojtaba ya shiga aikin soja na wani ɗan lokaci, sa'ilin yaƙin Iran da Iraqi, kamar yadda kafafen yaɗa labaran Iran suka ruwaito.

Ba kamara mahaifinsa ba, Mojtaba mutum ne da ba a cika jin ɗuriyarsa ba. Bai taɓa riƙe wani babban muƙamin gwamnati ba, kuma bai taɓa yin jawabi ga al'umma ba ko kuma yin wata babbar tattaunawa da kafafen yaɗa labarai.

Sai dai an daɗe ana yaɗa labaran cewa shi ne ke lura da lamurran mahaifinsa.

Sai dai za a iya cewa zaɓen shi a matsayin Ayatollah na cike da kace-na-ce.

An kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne a 1979 bayan tuntsurar da masarautar ƙasar, kuma bisa tsari ana zaɓen jagoran addini ne ta hanyar la'akari da ilimin addini da gogewa wajen jagoranci, ba ta hanyar gado ba.

Ɗaya daga cikin mambobin majalisar ƙwararru ta ƙasar – wadda ta ƙunshi malamai waɗanda ke zaɓen jagoran addini – ya ce shekara biyu da suka gabata Ali Khamenei ya nuna adawa da cewa ɗansa ya zama cikin waɗanda za su iya gadon shi

Zargin shiga siyasa

An fara jin suna Mojtaba ne a zaɓen 2005 na shugaban ƙasar Iran, wanda Mahmoud Ahmadinejad mai ra'ayin mazan jiya ya lashe.

Bayan nasarar ne, Mehdi Karroubi ya rubuta wasiƙar zuwa ga Khamenei, inda ya zargi Mojtaba da katsalanda a zaɓen ta hanyar amfani da dakarun juyin juya-hali da dakarun Basiji, waɗanda suka riƙa raba kuɗi ga masu zaɓe domin taimakon Ahmadinejad.

Bayan shekara huɗu, Mojtaba ya sake fuskantar wani zargin, inda sake lashe zaɓen Ahmadinejad ya haifar da zanga-zanga a ƙasar da ake kira da gwagwarmayar Green Movement.

Mostafa Tajzadeh, wanda mataimakin ministan harkokin cikin gida ne a lokacin ya bayyana sakamakon zaɓen a matsayin "juyin mulkin zaɓe." An ɗaure shi shekara bakwai saboda wannan, wanda kuma ya alaƙanta da "umarnin Mojtaba Khamenei".

Haka kuma an yi wa wasu masu sauƙin ra'ayi guda biyu Mir-Hossein Mousavi da Mehdi Karoubi ɗaurin talala bayan zaɓen. A watan Fabrairun 2012, Mojtaba ya gana da Mousavi, inda ya buƙace shi da ya haƙura, kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyana.

Masana suna tunanin Mojtaba zai ɗaura daga inda mahaifinsa ya tsaya na ɗaukar matakai tsaurara, wasu ma suna ganin mutum da ya rasa mahaifinsa da mahaifiyarsa da matarsa a hare-haren Amurka da Isra'ila, zai fi zafin rai da ƙin amincewa da ƙasashen yamma.

Amma zai fuskanci ƙalubalen tabbatar da wanzuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da kuma bayyana wa mutane cewa zai iya aikin, musamman fitar da ƙasar daga matsalolin taɓarɓarewar tattalin arziki da siyasa.