Real Madrid na son Tonali, Man U ta duƙufa kan Sangare

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan gaban Ingila Callum Wilson, mai shekaru 34, ya amince da sabuwar yarjejeniyar shekara guda a West Ham 'yan makonni bayan da aka yi ta tunanin zai bar kungiyar. (Telegraph)
Manchester United ta ƙara sunan ɗan wasan tsakiya na Ivory Coast na Nottingham Forest Ibrahim Sangare, mai shekaru 28, cikin jerin 'yan wasan da za ta saya a wannan bazarar. (CaughtOffside)
Manchester City na gab da kammala sayen ɗan wasan baya na Ingila na Newcastle United Tino Livramento, mai shekaru 23. (Football Insider)
Newcastle na nuna sha'awar sayen ɗan wasan tsakiya na Ingila Marcus Tavernier, mai shekaru 26, daga Bournemouth. (Teamtalk)
Wakilan Real Madrid sun kalli wasu ɗan wasan tsakiya na Italiya Sandro Tonali, mai shekaru 25, yayin da ƙungiyarsa ta Newcastle ta sha kashi a hannun Manchester City a gasar FA ranar Asabar. (Sun)
Andy Robertson na Liverpool ya ce tattaunawa kan makomarsa za ta kasance ne a asirce, bayan da aka yi ta yada batun cewa dan wasan bayan na Scotland, mai shekaru 31, ya kusa tafiya Tottenham a watan Janairu. (Athletic)
Arsenal ce ke kan gaba wajen neman siyan dan wasan tsakiya na Bayern Munich mai shekaru 31 Leon Goretzka. (Christian Falk)
Dan wasan gefe na Jamus Julian Brandt, mai shekaru 29, zai bar Borussia Dortmund a kan yarjejeniyar canja kungiya a kyauta a ƙarshen kakar wasa. (Sky Sports)
RB Leipzig ta amince da yarjejeniyar sirri da dan wasan tsakiya na Borussia Monchengladbach Rocco Reitz. (Florian Plettenberg)











