Trabzonspor ta ce Onana ya yi mata tsada, Tottenham na laluben kociya

Asalin hoton, Getty Images
An sanar da Manchester United cewa Trabzonspor, ba ta da niyyar biyan fam miliyan 40 zuwa 43 a kan golanta dan Kamaru, Andre Onana, mai shekara 29, a bazaran nan. (MEN)
Tottenham ta tattauna da tsohon kociyan Marseille Roberto de Zerbi a kan nada shi kociyan kungiyar a bazara idan har ta yi nasarar ci gaba da zama a gasar Firemiya. (Telegraph)
Tsohon kociya kuma tsohon dan wasan kungiyar Glenn Hoddle ya yi tayin tabbatar da ganin kungiyar ba ta fadi daga gasar Firemiya ba idan har za a kori kociyan rikon-kwarya Igor Tudor bayan da ya yi rashin nasara a wasansa na farko uku. (Mail)
Haka kuma wani tsohon dan wasan Tottenham din, Robbie Keane, ya bayyana a matsayin daya daga cikin wadanda ake ganin za su karbi aikin horad da kungiyar idan ta kori Tudor. (TeamTalk)
Napoli na fatan ta yi sauri ta zare dan wasan tsakiya na Scotland, Scott McTominay, mai shekara 29, ganin yadda wasu kungiyoyin Firmiya ke sha'awarsa. (Goal)
Dan wasan gaba na Newcastle United William Osula, ya ce bai san abin da gobe za ta haifar ba, amma dai a yanzu hankalinsa na nan a kungiyar, ta Tyneside. A baya ana danganta dan Denmark din mai shekara 22 da kungiyar Stuttgart, ta Jamus. (ChronicleLive)
Antoine Griezmann, mai shekara 34, ya yanke shawarar ci gaba da zama a Atletico Madrid, bayan da wajen tsakiyar kaka Orlando City ta nuna sha'awarta a kan tsohon dan gaban na Farsana. (L'Equipe)
Manchester City ta nuna cewa lalle za ta sake bai wa dan wasan Ingila Phil Foden sabon kwantiragi idan na yanzu ya kare a karshen kaka mai zuwa, to amma kuma ana ganin yarjejeniyar ba za ta kasance da sauki ba ganin yadda dan wasan na tsakiya mai shekara 25 a yanzu ba ya tashe sosai. (The Athletic)
Shi kuwa dan wasan Ingila na tsakiya Mason Mount, mai shekara 27, ba shi da niyyar cewa lalle sai ya bar Manchester United a bazaran nan. (Football Insider)
Dan wasan gaba na gefe na Brentford Kevin Schade, mai shekara 24, na ci gaba da daukar hankalin Tottenham, da Bayern Munich da kuma Inter Milan, inda suke son saye dan wasan na tawagar Jamus. (TeamTalk)











