Madrid na son ɗauko Allegri, ƙungiyoyin Firimiya na rububinThuram

Massimiliano Allegri

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Real Madrid na shawarar maye gurbin mai horad da 'yan wasanta, Alvaro Arbeloa da kociyan AC Milan Massimiliano Allegri a kaka mai zuwa. (Corriere dello Sport).

Real Madrid ta hakura da zawarcin dan wasan tsakiya na Manchester City Rodri, saboda a cewarta daya daga cikin dalilian da suka sa ta hakura da dan wasan na tawagar Sifaniya, mai shekara 29, shi ne, zai kai tsadar akalla yuro miliyan 60. (Sport).

Kociyan Bournemouth Andoni Iraola na shawarar kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar duk da sha'awarsa da Crystal Palace da Tottenham ke nunawa (Mail)

Tsohon dan wasan tsakiya na Tottenham da Ingila Dele Alli, mai shekara 29, ya koma atisaye a kungiyar ta Spurs, a yunkurin da yake yi na komawa fagen wasan bayan ya bar kungiyar Como, ta Italiya a watan Satumba. (Standard).

Crystal Palace ta sanya sunan tsohon kociyan Tottenham Thomas Frank, cikin jerin wadanda za ta nema domin maye gurbin Oliver Glasner, wanda zai bar kungiyar. (Sun)

Arsenal, da Liverpool da kuma Manchester United, na duba yuwuwar zawarcin dan wasan tsakiya na Juventus da tawagar Faransa, Khephren Thuram mai shekara 24. (CaughtOffside)

Dan wasan gaba na Faransa Antonie Griezmann, mai shekara 34, na shawarar ko dai ya ci gaba da zama a Atletico Madrid ko kuma ya amince da tayin tafiya kungiyar Orlando City ta babbar gasar Amurka (Major League Soccer). (Footmercato)

Bayern Munich na matukar duba yuwawar sayen dan wasan gaba na Galatasaray da tawagar Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 27, a shirin da suke na samun wanda zai maye gurbin Harry Kane, na Ingila mai shekara 32, idan ya tafi. (Footmercato)

Kungiyar RB Leipzig ta Jamus, za ta nemi wajen yuro miliyan 80, idan har za ta sayar da dan wasnta na gaba na gefe Yan Doimande, dan kasar Ivory Coast, mai shekara 19, wanda kuma ake alakantawa da tafiya wasu kungiyoyi da suka hada da Liverpool da Manchester United. (Football Insider).

Liverpool ta mayar da hankalinta kan Diomande ne, saboda tana ganin cewa, ba za ta iya samun Michael Olise, na tawagar Faransa, daga Bayern Munich, ba, saboda dan wasan mai shekara 24, yana son ci gaba da zama a Munich har bayan kwantiraginsa na 2029. (Sky Sports).

A karshe dai watakila Hearts za ta nemi kudin da ya kai fam miliyan 2, daga Manchester City, a kan matashin dan wasanta Keir McMeekin, mai shekara 16, na tawagar Scotland ta 'yan kasa da shekara 17, ganin yadda kungiyar ta Premier ta ke neman yin yarjejeniya da matashin, kafin ainahin yin kwantiragin komawarsa can kafin bazara. (Mail)