Me ya sa Iran ta fi kai hare-hare kan Daular Larabawa?

دود در تاسیسات امارات

Asalin hoton, AFP via Getty Images

    • Marubuci, Nasrin Hatum
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persia
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Bayan hare-haren makamai masu linzami da jiragen marasa matuƙa na baya-bayan kan Haɗaɗɗiyar Daualar Larabawa, wato UAE, waɗanda jami'an ƙasar suka alaƙata da Iran, an yi wata tattaunawa da ta ja hankali tsakanin Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da Shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Mohammed bin Zayed Al Nahyan.

Mista Netanyahu ya ce Isra'ila na tare da ''manyan ƙawayenta'' tare da jaddada ƙudurin ƙasarsa na aiki tare don samar da zaman lafiya da tsaro.

A cikin hirar, ya yi Allah wadai da hare-haren Iran kan fararen hula da ababen more rayuwa a ƙasar UAE, inda ya kira su ''mummunan saɓa wa ƴancin ƙasa da barazana ga zaman lafiyar yankin,'' kamar yadda wata sanarwar da ofishin jakadancin Isra'ila a UAE ya fitar.

Ma'aikatar tsaron Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta bayyana cewa na'urorin tsaron samaniyar ƙasar, sun kakkaɓo makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa a kwanakin nan.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu sauye-sauye siyasa da na aikin soji game da yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran, ciki har da batun janyewar UAE daga ƙungiyar OPEC+, ta ƙasashe masu arziƙin man fetur.

Da kuma ƙaddamar da shirin Shugaba Trump da ya kira "Project Freedom", wato aikin buɗe Mashigar Hormuz.

Haka kuma zaman ɗarɗar tsakanin UAE da Iran ya kai matsayin da ba a taɓa gani ba.

Abin da UAE ke gani a matsayin dalilan Iran

Yawan hare-haren da Iran ta kai wa UAE sun haifar da tambayoyin da suka zarta na na soji da ma na siyasa.

Amma me ya sa UAE kawai, kuma me ya sa ta tsananta hare-haren a yanzu, kuma me ya sa ƙasar ta fi fuskantar hare-hare daga Iran fiye da kowace gabanin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ranar 8 ga watan Afrilu?

Ko hare-haren na baya-bayan nan, wanda babu wani jami'in Iran da ya ɗauki alhaki, saƙo ne ga UAE ko ƙawayenta, musamman Amurka da Isra'ila?

An aza ayoyin tambayoyin ne bayan bayan wani rahoto da shafin Axios na intanet, ya ce Jami'an Amurka da na Isra'ila sun nuna cewa sojojin saman UAE na da hannu a hare-haren da aka kai wa Iran, kuma Isra'ila ta girke na'urorin Iron Dome masu kakkaɓo makamai, tare da tura sojojin Isra'ila zuwa ƙasar, iƙirarin da idan ya tabbata ke nuna ƙarfin ƙawancen tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

هواپیما در میان دود

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Rahotonni na nuna cewa Iran ta ƙaddamar da hare-hare zuwa cikin UAE fiye da kowace ƙasa a yankin Gulf
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sultan Al-Nuaimi, babban daraktan cibiyar bincike da nazarin tsare-tsare, ya ce ya yi imanin cewa gwamnatin Iran na ci gaba da keta dokokin duniya da alfarmar makwabtaka, wanda a cewarsa ya nuna ''ƙaryar da Iran ta yi a baya'', domin kafa hujjar hare-haren kan ƙasashen yankin Gulf tana mai kafa hujja da wanzuwar sojoji da sansanonin ƙasashen waje a cikinsu.

Ya shaida wa BBC cewa wannan hali na nuna gwamnatin Iran na ci gaba da abin da ya kira ''amfani da ta'addanci'' a matsayin abin da za ta mu'amalanci ƙasashen yankin.

Mr. Nuaimi ya ƙara da cewa tasirin UAE ya dogara ne da nasarar tattalin arzikinta, wanda ya ce ya zame wa gwamnatin Iran babban ƙalubalen kafa irinsa.

A cewar Nuaimi hari kan UAE da sauran ƙasashen yankin, hari ne kan ƙasashen duniya da suka dogara da ƙasashen yankin wajen samun makamashi da sauran abubuwa.

Shi kuwa Mohammed Baharoun, babban daraktan cibiyar bincike da tsare-tsare da ke Dubai ya faɗa wa BBC cewa Iran ce ya kamata a yi wa tambayar dalilan kai wa UAE hare-hare.

Ya ƙara da cewa Iran na kai hare-haren ne domin haifar da fargaba da sauya matsayinta, kuma hakan ne ya sa Tehran ke kai wa ƙasashen da suka ƙi amincewa da abin da ya kira ''ɓata suna'' ko ɗage mata takunkumai.

'Dalilai huɗu da suka janyo hare-haren'

Farfesa Leila Naqoula, ta jami'ar Lebanon, ta shaida wa BBC cewa akwai dalilai masu yawa na kai wa UAE hare-hare.

Na farko a cewarta shi ne alaƙarta da Isra'ila, bayan da ƙasashen biyu suka daidaita juna saboda yarjejeniyar Abraham, wadda ta sanya ƙasashen biyu kusanci da juna fiye da sauran ƙasashen yankin Gulf.

Ms. Naqoola ta ce dalili na biyu shi ne ficewar UAE daga ƙungiyar OPEC+, wanda a cewarta ya bai wa ƙasar damar haƙo mai tare da fitar da shi ƙetare ba tare da iyakancewa ba, wani abu da ya kara yawan mai a kasuwar duniya.

Ta ƙara da cewa ƙaruwar fitar da man zai rage matsin lamba kan Donald Trump, wanda ke ƙoƙarin hana mai tashi, saboda tsadar fetur na haifar da raunin tattalin arzikin Amurka da ma tattalin arzikin duniya baki ɗaya, kuma hakan zai janyo masa sukar siyasa a cikin gida.

تاسیسات نفتی

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, UAE ta fice da OPEC domin ta riƙa fitar da mai ba tare da iyakancewa ba.

Dalili na uku da Ms Naqola ta bayar shi ne yunƙurin UAE na fitar da mai ta wata hanyar daban da mashigar Hormuz da Iran ta rufe.

Hakan zai iya janyo UAE ta samu ƙarin ƙarfi a yankin Gulf, wani abu da Iran ba za ta so ba, a matsayin UAE na ƙawar Amurka da Isra'ila.

Ms Naqola ta ce dalili na huɗu shi ne rashin jituwa tsakanin ƙasashen yankin Gulf, musamman tsakanin Saudiyya da UAE, musamman bayan ficewar UAE daga ƙungiyar OPEC+, wani abu da ita kanta Iran ke kallo a matsayin abin da zai iya hana ta kai wa UAE hare-haren.

Ma'aikatar tsaron UAE ta bayyana cikin wata sanarwar cewa na'urorin tsaron samaniyarta sun kakkaɓo manyan makamai masu linzami 551 da ƙanana 29 da kuma jirage marasa matuƙa 2,265 tun bayan fara yaƙin.

Yunƙurin gina madadin mashigar Hormuz

 بندر فجیره

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tashar jiragen ruwa ta Fujairah mai matuƙar muhimmanci da ke wajen mashigar Hormuz.

Tashar jiragen ruwa ta Fujairah da ke UAE, tasha ce mai matuƙar muhimmanci ga ƙasar, musamman wurin da take, wato wajen mashigar Hormuz, wadda kuma ta samu ƙarin ƙarfi sakamakon rufe Hormuz inda jirage suka riƙa bi ta can domin fitar da mai, musamman bayan ficewar ƙasar daga ƙungiyar OPEC

Baya ga wannan ƙasar na da niyyar wani shiri da ta yi wa laƙabi da ''Hanyar Indiya zuwa Gabas ta Tsakiya zuwa Turai" shirin da idan an aiwatar da shi zai sa UAE ta zama cibiyar jigilar kasuwanci duniya ta gaba ta hanyar tashar jiragen ruwa ta Jebel Ali da tashar ruwan Fujairah, domin rage dogaro da mashigar Hormuz.

Shirin ya ƙunshi hanyoyin sufuri daban-daban da suka haɗa da sufurin ruwa da na jiragen ƙasa.

Duk da cewa shirin ba zai iya maye gurbin jigilar da ake yi ta mashigar Hormuz ba, amma za ta rage dogaro kacokan da mashigar, musamman ga jigilar abubuwan da ba man fetur ba, domin samun sauƙin fitarwa da shigo da kaya, musamman la'akari da halin da ake ciki a yankin.

پروژه «کریدور اقتصادی هند - خاورمیانه - اروپا» از هند آغاز می‌شود و پس از عبور از امارات، عربستان، اردن و اسرائیل به اروپا می‌رسد

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shirin gina babbar hanyar kasuwancin "India-Gabas Tsakiya - Turai'' zai fara be daga Indiya sannan ya bi ta Turai ya wuce ya dangana da UAE da Saudiyya da Jordan da kuma Isra'ila.

Farfesa Bernard Heikal daraktan cibiyar nazarin yankunan Gabas da halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka da Tsakiyar Asiya ya ce harin da aka kai wa tashar ruwa ta Furaijah babban saƙo ne da ke nuna cewa dogaro da shimfiɗa bututu daga Saudiyya da UAE wajen fitar da mai ba lallai ya zama ƙalubale ko barazana ga mashigar Hormuz ba.

Iran na son nuna cewa tana da ikon rufe mashigar Hormuz tare da kai wa bututun hare-hare kamar yadda ya ce.

Farfesa Haykal ya ce batun bai taƙaita kawai ga mashigar Hormuz ba, ya haɗa ne da batutuwan siyasa da tattalin arziki da kuma da'irar yankin, Kuma Iran na son tabbatar da matsayinta.

Ya ƙara da cewa hakan ya sake tabbatar da ƙudirin Iran na duba yiwuwar karɓar haraji daga ƙasashen Larabawa domin amfani da shi wajen sake gina wuraren da aka lalata mata a lokacin yaƙin.