Abin da zai iya hana ka auren mace fiye da ɗaya

...

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A shekarar 2019, babban limamin Jami'ar Musulunci ta Al-Azhar a ƙasar Masar ya yi wani kalamin da ya yamutsa hazo, inda ya ce auren mace fiye da ɗaya "zai iya zama rashin adalci ga mata da yara".

Sheikh Ahmed el-Tayeb, wanda mashahurin malamin Musulunci ne ya ce auren mace fiye da ɗaya, wanda abu ne da ya yawaita tsakanin Musulmai sanadiyyar halascinsa a addini, na faruwa ne sanadiyyar "rashin fahimtar ayoyin Qur'ani yadda ya kamata game da mas'alar."

Malamin ya yi kalamin ne a wani shirin talabijin na mako-mako.

To amma kalaman malamin sun tayar da ƙura, lamarin da ya kai ga har sai da hukumomin jami'ar ta Al-Azhar suka yi ƙarin haske kan cewa ba manufar malamin ba ce ya nuna tamkar haramun ne auren mace fiye da ɗaya.

Tayeb has been the imam of Al-Azhar since 2010.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, El-Tayeb ya kasance limamin masallacin jami'ar Al-Azhar tun daga shekarar 2010

Sheikh Ahmed el-Tayeb ya yi ƙarin bayani, inda ya ce auren mace fiye da ɗaya abu ne da ya dogara kan cika wasu ƙa'idoji.

"Mutanen da suka ce auren mace fiye da ɗaya wajibi ne sun yi kuskure," in ji malamin.

Ya ƙara da cewa: "Al-Qur'ani ya gindaya sharaɗin yin adalci da ya kamata Musulmi ya cika kafin ya auri mace fiye da ɗaya, kuma idan har mutum ba zai iya yin adalcin ba to ya haramta a gare shi ya auri mace fiye da ɗaya."

Sheikh Tayeb ya kuma buƙaci al'umma su ɗauki matakan da za su inganta rayuwar mata.

"Mata ne fiye da rabin al'umma. Idan ba mu fifita su ba, to tamkar muna tafiya ne da ƙafa ɗaya," kamar yadda malamin ya yi ƙarin haske a wani bayani da ya wallafa a shafin sada zumunta.

Majalisar kula da harkokin mata ta ƙasar Masar ta yi maraba da bayanan malamin.

"Musulunci ya karrama mata, ya buƙaci a yi musu adalci da kare hakkokinsu da aka riƙa take musu a baya," in ji Maya Morsi, shugabar Majalisar Kula da al'amuran mata ta ƙasar Masar.

A Najeriya ma batun auren mace fiye da ɗaya abu ne da a wasu lokutan ke haifar da muhawara tsakanin a'umma.

Auren mace fiye da ɗaya abu ne da ya zama ruwan dare a Najeriya, musamman a arewacin ƙasar inda ke da yawan mabiya addinin Musulunci.

A shekara ta 2017 sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya taɓa jan hankalin al'umma kan auren mata da yaw aba tare da bin dokokin da suka dace ba.

"Mu a arewa duk mun ga illar yadda mutanen da ba za su iya riƙe mace ɗaya ba, amma suka auri huɗu," in ji basaraken.

"A ƙarshe sai ka ga sun haifi yara 20, su gaza bas u ilimi, su bar su suna yawo kan titi, a ƙarshe su zama ƴan banga ko masu aikata laifuka".