Ban sani ba ko zan yi aure a duniya - Matashin da ya shekara 42 babu aure
Ban sani ba ko zan yi aure a duniya - Matashin da ya shekara 42 babu aure
Wani mazaunin garin Wudil na jihar Kano a arewacin Najeriya ya ce babu tabbas ko burinsa na yin aure zai cika a rayuwarsa duk da cewa yana da sana'a.
Yanzu shekarar Gambo Musa 42 da haihuwa kuma har yanzu yana nan da burin haifar 'ya'ya goma sha wani abu, kamar yadda ya faɗa wa BBC.
Gambo yana da shagon sayar da takalma, sannan yana soyawa tare da sayar da kifi.
Bincike ya nuna cewa albarkar haihuwa ta ragu a duniya, inda a farkon shekarar 1970 duk mace ɗaya ke iya haifar yara huɗu. Amma zuwa 2015, kowace mace ɗaya bai fi ta haifi yara biyu da rabi ba.



