Mutumin da ya kwashe shekara 50 babu aure saboda rashin asali ya samu mata

Mustafe da amaryarsa
    • Marubuci, Saleebaan Saxansaxo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Weriye
  • Lokacin karatu: Minti 5

Bayan kwashe sama da shekara 20 yana fuskantar ƙalubale wajen samun matar aure, yanzu wahalarsa ta zo ƙarshe.

Mustafa, wani mutum da ya shafe shekara 50 a duniya a matsayin gwauro, wanda ke zama a birnin birnin Hargeisa na yankin Somaliland, a ƙarshe ya samu wadda ta amince ta aure shi.

An yi auren nasu ne a bara (2024), inda ya samu gagarumin sauyi a rayuwarsa.

Mustafa ya samu kansa a wannan hali na rashin samun matar da za ta aure shi da tsangwamar rayuwa ne sanadiyyar wani abu da ya faru da shi a lokacin da yake jariri.

Mutumin, wanda ya tattauna da BBC, ya ce dukkanin mata bakwai da ya tunkara da nufin aure sun ƙi amincewa kasancewar ba a san mahaifinsa ba, kuma an tsince shi ne a ƙasan wata bishiya lokacin da yake jariri, lamarin da ya sanya ya riƙa fuskantar tsangwama.

Yadda rayuwar Mustafa ta samo asali

Mustafa ya shaida wa BBC cewa a shekarar 1975 ne aka tsince a unguwar Goljano da ke birnin Hargeisa, inda al'umma suka kai shi wata makaranta a cibiyar matasa ta Hargeisa, inda ya yi karatun firamare da sakandare.

Ya ce "na yi rayuwa mai kyau a cibiyar gabanin ɓarkewar rikici tsakanin wata ƙungiyar ƴan bindiga da gwamnati."

A lokacin da ya kai shekara 12, Mustafa ya tambayi masu kula da shi game da yadda ya ga iyaye na ziyartar yaransu a makarantar suna kawo musu kayan wasa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Lokacin da na kai shekara 12, na ga iyaye na kawo wa yaransu kayan marmari da alawa suna kuma wasa da su cikin nishaɗi. Yara ne kamar ni, sai na ce wa kaina mene ne yara ke iya samu daga iyayensu?"

Mustafa ya ce bayan haka ne sai ya fara fafutukar neman iyayensa, inda ya yi wa shugaban cibiyar da yake magana.

"Na je wurin shugaban cibiyar, na tambaye ni ina iyalina suke, daga nan sai ya ciro wasu takardu, ya ce min waɗannan dattijan, 'su huɗu ne suka kawo ka nan, kuma sun faɗa min cewa an tsince ka ne a cikin unguwa lokacin asuba."

Mustafa ya bayyana cewa duk da bai samu kulawa irin ta iyaye ba, amma ya ji daɗin zamansa a cibiyar matasan ta Hargeisa, inda aka riƙa kula da shi, aka kuma riƙa ciyar da shi.

Bayan ɓarkewar rikici ne "sai muka gudu daga wurin, sai na taho Djibouti, inda na samu kaina cikin wahala, daga nan na fara wata ƴar ƙaramar sana'a, kasancewar ba na da iyaye kuma ga shi ina da ƙarancin shekaru," in ji Mustafa.

Ya bayyana cewa ya koma Hargeisa a shekarar 1998 bayan fuskantar matsaloli, inda bayan dawowarsa sai ya fara wata ƙaramar sana'a wadda ta taimaka masa wajen rayuwa, sai dai daga baya kuma ya talauce baki ɗaya.

A shekarar 2002 sai ya fara aikin gadi a wurin shaƙatawa na Freedom Park Center da ke Hargeisa, inda yake har zuwa yanzu.

Mustafe da amaryarsa

Ƙalubalen da ya fuskanta a rayuwa

Mustafa ya shaida wa BBC cewa a tsawon shekara 20 ya yi soyayya da mata bakwai a lokuta daban-daban, sai dai dukkaninsu sun rabu da shi a lokacin da ya faɗa musu cewa ba ya da uwa, ba uba kuma babu dangi.

"Na nemi auren kimanin ƴanmata bakwai wadanda muka yi soyayya da su, wadda muka fi daɗewa tare ita ce wadda muka yi wata tara tare, to amma sai su guje ni da zarar na faɗa musu cewa ba na da iyaye ko dangi. Sukan ce min za su tuntuɓi iyaliansu, daga nan ba zan sake ganin su ba kuma ba za su sake kula ni ba.

Ya ce "sukan ce min 'su wa za ka turo neman auren tunda ba ka da kowa? Idan ba ka da lafiya su wane ne za su zo gaishe ka? Irin haka dai."

Mustafa ya ce ɗaya daga cikin ƴammatan da ya yi soyayya da su ta so ta aure shi amma iyalanta suka hana saboda ba ni da iyaye. A lokacin da ta matsa har barazanar yin watsi da ita suka yi.

Ba kawai wurin neman aure ne Mustafa ya fuskanci ƙalubale ba, domin kuwa ya samu matsala daga sauran al'umma. "Na fuskanci tsangwama sosai a cikin al'umma, sukan yi min gorin cewa ban da uwa ban da uba, nakan ce musu babu matsala."

Mustafe da amaryarsa

Ta yaya ya samu mata?

Mustafa ya bayyana cewa shekarar da ta gabata ta bambanta matuƙa da sauran sama da shekara 20 da ya yi yana neman matar aure, kasancewar a bara ne ya samu matar da ya aura, inda ya haɗu da wata budurwa mai suna Gudoon Hassan Farah, ƴar shekara 19, inda aka ɗaura musu aure a ranar 14 ga watan Disamban 2024.

Lokacin da yake yin bayani kan auren, Mustafa ya ce lamarin ya faru ne babu zato babu tsammani.

"Nakan je wurin karatu, wata rana sai na faɗa wa malamaina matsalar da ke damu na. Sai malamin ya haɗa ni da wannan budurwa da na aura, kuma iyalanta sun karɓe ni hannu bibbiyu."

Da BBC ta tambaye shi yadda aka yi ya shawo kan matar tasa, sai ya ce "An ɗan ɗauki lokaci kafin na shawo kanta. Lokacin da ta amince sai na je na gaishe da mahaifinta. Sai na ga abin ya sha bamban da sauran na baya, ya yi maraba da ni sosai. Ya ce idan tana so na to shi babu abin da zai ce sai dai ya yi mana addu'a. Yanzu shekarun da na kwashe ina shan wahala sun ƙare."

Ba Mustafa ne kaɗai ke fuskantar irin wannan matsala ba, akwai wasu da dama, sai dai ba za su su bayyana halin da suke ciki ba domin gudun tsangwama.