Yadda ɗan majalisa ya aurar da marayu 100 a Kebbi

Wani ɗan majalisar wakilan Najeriya a jihar Kebbi ya aurar da ‘yan mata marayu su 100 a wajen wani ƙasaitaccen buki da aka gudanar ranar Asabar.
An ɗaura wa marayu 100 auren ne a fadar mai martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Ismail Muhammad wanda ya jagoranci daurin auren.
Bukin ya ja hankalin jama’a a wannan yankin Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.
An ɗaura aurarrakin ne ɗaya bayan ɗaya bayan sanar da biyan sadaki da kuma waliyan kowane ango da amarya.
Kowace ɗaya daga cikin amaren ta samu kyaurar saitin gado da kujeri da sauran kayan ɗaki da kuma AlKur’ani mai girma.
Ɗaya daga cikin amaren Hafsat Ismail Haruna ta bayyana auren a matsayin wani babban al’amari ga rayuwarta.
“Wannan ba ƙaramin gata ba ne domin ban taɓa tunanin zan yi aure nan kusa ba saboda ban san uwa da uba ba,” in ji ta.
Ɗan majalisar mai wakiltar mazabar Argungu/Augie a majalisar wakilai Hon Sani Yakubu Noma wanda ya ɗauki nauyin aurar da ‘yan matan har 100 ya ce ya san maraici domin shi maraya ne kuma wannan ne dalilin da ya sa ya jagoranci aurar da marayun.
Ɗan majalisar ya kafa kwamiti da suka jagoranci tabbatar da auren na marayu. Ya kuma ce zai ci gaba da aurar da marayun duk shekara tsawon wa’adin shekaru huɗu da zai yi a majalisar tarayya.
Angwayen amaren na cike da farin ciki baki har kunne saboda sauƙin da suka samu wajen samun abokan zaman rayuwa, abin da sai wasu sai sun yi gumi kafin su samu.
Sun kuma gode wa ɗan majalisarsu kan kyautata masu da ya yi ya aurar da su.
Sannu a hankali wannan al’adar ta aurar da mutane masu yawa a lokacin guda kuma kyauta, wadda aka fara a jihar Kano yanzu ta yi naso zuwa sauran jihohin arewacin Najeriya.
Al’ummar yankin arewa ta dauki aure cikin abubuwa mafiya muhimmanci a rayuwa amma rashin sukuni da kuma tsadarsa ke yi wa mutane da yawa tarnaki wajen taka wannan muhimmin mataki a rayuwa.











