Mu kwana lafiya
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 13 ga watan Janairun 2026.
Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Iran ta ce aƙalla mutum dubu biyu, ciki har da jami'an tsaro, ne suka mutu a zanga-zangar ƙin jinin gwamnati, wadda ta dage cewa ta kawo ƙarshen ta.
Sai dai, shugaba Trump ya buƙaci ƴan Iran ɗin su ci gaba da zanga-zangar, inda ya tabbatar musu cewa taimako na nan zuwa.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump bai yi ƙarin bayani ba kan kalamansa na cewa masu kisa da zalunci za su ɗanɗana kuɗarsu.
Wwannan sanarwa ce da ta fito fili ta nuna yana da niyyar ɗaukar mataki, kuma duba da irin kalamansa da wahala ya janye.
Tawagar da ke bai wa Trump shawara kan harkokin tsaro ta gana a yau Talata domin tattauna matakin da za a ɗauka kan Iran, sai dai babu tabbacin ko an yanke wani hukunci.

Asalin hoton, Mustapha Ibrahim/BBC
Gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da sake buɗe makarantar Sakandiren ƴanmata ta Maga, inda aka sace ƴanmata 24 kafin daga baya a ceto su.
Kwamishiniyar makarantun Firamare da Sakandare a jihar, Dakta Halima Bande, ita ce ta bayyana haka yayin tattaunawa da manema labarai bayan wani taro kan tsaro da shugabannin makarantu a birnin Kebbi a yau Talata.
Bande ta bayyana cewa al'amura sun fara komawa daidai kuma an karfafawa iyaye da ɗalibai gwiwa ta hanyar shawarwari da kuma aika jami'an tsaro - lamarin da ya buɗe kofar komawa don cigaba da karatu.
Kwamishiniyar ta ce gwamnati na shirye wajen ɗaukar matakan tsaro domin tabbatar da tsaron lafiyar ɗalibai da malamai.
A cewarta, gwamna Nasir Idris ya bayar da umarnin aiwatar da shirye-shiryen wayar da kan shugabannin makarantu da kuma malamai kan tsaro domin kauce wa afkuwar abin da ya faru a nan gaba.
"Shugabannin makarantu, mataimakansu, malamai da kuma ɗalibai na da rawar taka wa wajen tabbatar da tsaro a makarantu," in ji dakta Halima.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano ta ce ta tabbatar da zargin da aka yi na cewa ma’aikatan lafiya sun bar almakashi a cikin wata mata mai suna Aishatu Umar a lokacin tiyata, lamarin da ya yi sanadin rasuwarta daga bisani.
Wata sanarwa da ta fitar na cewa Babban Sakataren Hukumar Dr. Mansur Mudi Nagoda ya dakatar da ma’aikatan da lamarin ya faru a lokacin aikinsu tare da gabatar da batun a gaban kwamitin ladabtarwa.
Hukumar ta ce ta dakatar da ma'aikata uku waɗanda suke da hannu a cikin lamarin nan take.
Har ila yau, sanarwar ta ce an miƙa batun ga kwamitin ladabtarwa ga ma'aikatan lafiya a jihar domin ci gaba da bincike da kuma ɗaukar matakan da suka dace waɗanda dokoki suka tanada.
Hukumar ta kuma miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan marigayiya Aishatu Umar kan abin bakin ciki da ya faru.
Ta tabbatar da cewa ba za ta lamunci kowane irin sakaci ba kuma za ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai domin kare rayuka da kuma samun amincewar marasa lafiya a faɗin cibiyoyin lafiya na jihar.

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ƴansanda a jihar Katsina ta ce ta cafke wasu mutum uku waɗanda ake zargi da mallakar tarin abubuwan fashewa.
An kama abubuwan fashewar ne a cikin wata mota ƙirar Golf a ƙauyen Koza da ke karamar hukumar Daura na jihar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴansandan jihar, Abubakar Sadiq ya fitar, ya ce an samu nasarar ce bayan wani samame ranar 7 ga watan Janairun 2026, bayan cafke motar wanda wani mai suna Jamilu ke tuka wa.
Sadiq ya ce bayan binciken da suka yi, sun gano ababen fashewa 6,975 a wajen mutanen da ake zargi.
Ya ce mutanen sun amsa cewa sun karɓi ababen ne wajen wani mutum Najib, wanda aka yi niyyar kai wa Kwangolam a karamar hukumar Mai'adua na jihar Katsina daga Kano.
"Waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu kuma nan ba da jimawa ba za a tura su zuwa kotu da zarar an kammala bincike, yayin da ake ƙoƙarin ganin an kama waɗanda suke tsere," in ji kakakin ƴansandan.

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon kocin Real Madrid Xabi Alonso ya ce yana alfaharin cewa ya yi ƙoƙarinsa kafin barin ƙungiyar.
Alonso ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram a yau Talata.
"Wannan babi na rayuwata ya kare, kuma bai tafi yanda muke so ba. Horar da Real Madrid nauyi ne da kuma girmamawa gare ni, a kowace rana.
"Na gode wa ƙungiyar, ƴan wasanta da kuma ɗaukacin magoya baya saboda yardarsu da kuma goyon baya - Na bar Madrid cikin mutunci da alfaharin cewa na yi iya ƙoƙarina," in ji Alonso.
A ranar Litinin ne Madrid ta sanar da raba gari da kocin nata, bayan ya amince ya ajiye aiki bisa raɗin kansa.
Tuni dai hukumomin ƙungiyar suka maye gurbinsa da Alvaro Arbeloa - wanda ya taɓa buga mata a baya, a matsayin sabon mai horaswa.

Asalin hoton, Universal Images Group/Getty Images
Hukumomi a Uganda sun bayar da umarnin katse intanet a ƙasar gabanin zaɓen shugaban ƙasar da za a yi ranar Alhamis.
Sun ce sun ɗauki matakin ne domin tabbatar da tsaron ƙasar da kuma hana yaɗa labaran ƙarya.
Tun da farko gwamnatin ƙasar ta ce babu wani shirin kaste intanet ɗin.
An yi ta samun tashin hankali da tsoratarwa a yaƙin neman zaɓen da aka yi, inda masu sanya ido daga ƙasashen waje suka bayyana cewa an kama ɗaruruwan magoya bayan jamiyyun adawa.
Shugaba Yoweri Museveni ya kammala gangamin yaƙin neman zaɓensa a yau Talata, taron da ƴan jarida suka kasa samun damar shiga.
Yayin da babban ɗan takara na jamiyyar adawa Bobi Wine, wanda ke takara a zaɓen shugaban ƙasa karo na biyu, ya kammala yaƙin neman zaɓensa a ranar Litinin.

Asalin hoton, Mandel NGAN / AFP via Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya buƙaci al'ummar Iran su jajirce sannan su ci gaba da zanga-zanga.
Trump ya faɗi haka ne a wani sako da ya wallafa a kafar sada zumunta na Truth Social.
"Ku ci gaba da zanga-zanga ƴan Iran - Ku mamaye hukumominku, ku rubuta sunayen waɗanda suke kisa da kuma aikata ɓarna. Za su ɗanɗana kuɗarsu.
"Na soke duk wata tattaunawa da jami'an Iran har sai an dakatar da kashe masu zanga-zanga.Taimako na nan zuwa," in ji Trump.

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa akwai aƙalla ƴan gudun hijira 21,807 daga ƙasashen makwabta da suka tsere wa rikici da ba a yi wa rijista ba a Najeriya, lamarin da ke hana su samun tallafin abinci da kiwon lafiya da sauran muhimman abubuwan jin-kai.
Rahoton hukumar kula da ƴan gudun hijira ta MDD UNHCR na Nuwambar 2025, ya nuna cewa mafi yawan waɗanda ba a yi wa rijista ba sun fito ne daga yankin Anglophone na Kamaru mai fama da rikici.
Masu neman mafaka da ƴan gudun hijira 127,000 suka je Najeriya daga ƙasashe 41, inda 21,807 ke jiran hukumar ƙasa ta ƴan gudun hijira NCFRMI ta yi musu rijista.
A halin yanzu, akwai mutum 80,915 da aka amince da su a matsayin ƴan gudun hijira, yayin da aka tantance bayanan masu neman mafaka fiye da 25,000.
Binciken na UNHCR ya nuna cewa adadin ƴan gudun hijira da ba a yi wa rijista ba ya ƙaru cikin shekara guda, daga 21,095 a Disambar 2024 zuwa 32,750 a Yuni 2025, kafin ya sake sauka zuwa 21,807 a Nuwambar 2025.
Ƴan gudun hijira da ba a yi wa rijista ba dai ba su da damar samun tallafin abinci ko kuɗi ko inshorar lafiya da sauran tallafin jin-kai daga UNHCR.

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Dinkin Duniya ta ce aƙalla yara 100 sojojin Isra'ila suka kashe a Gaza tun bayan tsagaita wutar da aka yi watanni uku da suka gabata.
Asusun kula da ƙananan yara na majalisar, UNICEF, ya ce a ƙiyasi duk rana ɗaya sojojin Isra'ila ko hare- harensu ta sama na kashe yaro ɗaya.
Wani mai magana da yawun hukumar ya ce duk da dai yarjejeniyar ta rage yawan hare- haren, hakan bai wadatar ba saboda har yanzu ana binne yara.
Majalisar Dinkin Duniyar ta kuma ce aƙalla yara shida ne suka mutu a Gaza a makonni biyu da suka gabata saboda yanayi na tsananin sanyi.

Asalin hoton, Getty Images
Bayanai na ci gaba da fitowa kan irin ƙarfin da jami’an tsaron Iran suka yi amfani da shi wajen murƙushe zanga-zangar ƙin jinin gwamnati, bayan da wasu ’yan ƙasar suka samu damar fitar da bayanai zuwa ƙasashen waje.
Ko da yake har yanzu ba a dawo da intanet gaba ɗaya a ƙasar ba, wasu sabbin bidiyo kan zaluncin da aka yi wa masu zanga-zangar na ƙara bayyana a kafafen sada zumunta.
Shaidu na cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu na iya kai wa kusan dubu ɗaya.
Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da samun zanga-zanga a wasu sassa na ƙasar, sai dai kafar yaɗa labaran gwamnati ta Iran ta ce ba a samu wani tashin hankali ba a daren Litinin.
Masu sharhi na ganin rage katsewar sadarwa da aka yi na iya nuna cewa hukumomin ƙasar na ganin sun samu galaba kan zanga-zangar baki ɗaya.
A nasa ɓangaren, Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya shaida wa Aljazeera cewa an ɗauki matakin katse sadarwar ne tun ranar Juma’a, bayan da wasu da ya kira ’yan ta’adda suka shiga cikin zanga-zangar.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin lafiya a jihar Kano sun bayyana cewa sun kafa wani kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike kan yadda wata mata ta rasa ranta, bayan an bar almakashi a cikinta a lokacin da aka yi mata tiyata.
Matar ta rasa ranta bayan wani likita ya manta bai cire almakashin da ya yi mata aikin da shi ba.
Dangin matar sun buƙaci a bi musu haƙƙinta tare da ɗaukar matakin da ya dace a kan wanda ya aikata laifin.
Ma’aikatar lafiyar ta tabbatar da cewa sun sami bayanin cewa matar ta rasa ranta, sanadiyar barin almakashi a cikinta bayan kammala yi mata tiyata.
To sai dai kwamishinan ma’aikatar Dr Abubakar Labaran Yusuf yace ba za su iya yin cikakken bayanin abinda ya faru ba, sai sun yi bincike.
Mijin matar da ta rasu, Abubakar Muhammad ya shaida wa BBC cewa tun bara ne cikin watan Satumba aka yi mata tiyata, kuma a cewarsa daga nan ta riƙa jin ciwo.Bayanai na cewa marasa lafiya da dama suna kokawa da yadda ake samun sakaci wajen kula da su.
Sakataren hukumar kula da asibitoci ta jihar,Dr. Mansur Mudi Nagoda ya tabbatar wa da BBC cewa ya karbi umarni daga kwamishinan lafiya, inda suka fara gudanar da bincike don gano abinda ya faru har wannan mata ta rasa ranta.
Ba wannan ne karon farko da marasa lafiya ke gamuwa da irin wannan lamari ba, ko a watan janairun 2023 ma, hannun wani jariri dan kasa da mako daya ya lalacewa sanadiyar ɗaurin da aka yi masa, bayan da wani likita ya manta bai cire robar da ya ɗaure hannun ba, lokacin da yake gudanar da wasu gwaje-gwaje.

Asalin hoton, X/USAfricaCommand
Rundunar sojin Amurka da ke gudanar da aikinta a nahiyar Afirka ta sanar da bai wa Najeriya kayan aiki bunƙasa yaƙi da matsalar tsaro.
Rundunar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, yau Talata.
Sanarwar ta ce "dakarun Amurka sun sauke muhimman kayan aikin soji ga abokan huldarmu na Najeriya a Abuja.
"Wannan tallafi zai taimaka wa Najeriya a wajen ayyukanta, kuma hakan ya ƙara jaddada alaƙar tsaro da ke tsakanin mu," a cewar sanarwar.
Haka kuma sanarwar na ƙunshe da hoton wani jirgin dakon kaya da ƙofarsa a buɗe, yayin da za a iya ganin wasu kaya jibge a kusa da jirgin.
Sai dai babu ƙarin bayani kan ko mene ne ke ƙunshe a cikin kayan.
Najeriya na fama da matsalar tsaro a yankunanta daban-daban: waɗanda suka hada da matsalar ƙungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar, da ƙungiyoyin ƴan bindiga a arewa maso gabashin ƙasar da arewa ta tsakiya, sai kuma ƴan aware a kudu maso gabashin ƙasar.
A ranar 25 ga watan Disamban 2025 ne Amurka ta ce ta kai hari kan ƴan bindiga masu alaƙa da ƙungiyar IS a jihar Sokoto da ke Najeriya.
Duk da babu cikakken bayani kan tasirin harin, amma shugaban Amurka Donald Trump ya ce hare-haren "suna da ƙarfi da haɗari".

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin Najeriya sun ce jami’an tsaro sun kashe fiye da ‘yanbindiga 200 a wani "gaggarumin samamen hadin gwiwa" da aka gudanar a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, yayin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke ci gaba da ƙoƙarin daƙile matsalar rashin tsaro a ƙasar.
‘Yansanda sun kuma kama wasu da ba a fayyace adadinsu ba, wasu daga cikin su sun ji raunuka daban-daban sakamakon musayar wuta da aka samu. Ana kuma bin sawun sauran ƴanbindigan da suka tsere, kamar yadda hukumomin suka faɗi.
Kwamishinan harkokin yaɗa labarai na Jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya shaida wa BBC cewa an lalata sansanonin ‘yanbindiga da dama a lokacin samamen da aka ƙaddamar a ƙarshen mako, wanda ya haɗa da ɓangarori daban-daban na jami’an tsaro da na sojoji.
Ya ce wannan farmaki ya kawo cikas sosai ga ayyukan ƙungiyoyin ‘yanbindiga da ke yankin.
“Har yanzu ana ci gaba da kai samamen, a daren Lahadi an samu musayar wuta mai tsanani a kusa da yankin Obajana, inda jami’an tsaro suka saka ƴanbindigar cikin mawuyacin hali. Babban matsalar ita ce ƴanbindigar sun sace mutane da dama suna amfani da su a matsayin garkuwa, domin sun san jami’an tsaro ba za su so su kashe su ba tare da waɗanda suka sace,” in ji shi.
Hukumomi sun bayyana cewa an tsara samamen ne tare da haɗin gwiwar gwamnatin Jihar da goyon bayan mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro da kuma shugabancin hukumomin tsaro na Najeriya.
Wannan farmakin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Tinubu ke fuskantar matsin lamba daga jama’a wajen daƙile yawaitar tashin hankali a fadin ƙasar, yayin da jihar Kogi ke ƙara zama muhimmin wurin da tsaro ke ƙara taɓarɓarewa saboda hanyar da ke haɗa arewa da kudancin ƙasar ta cikin dazuka.

Asalin hoton, Getty Images
An ga wasu bidiyoyi da suka yaɗu, inda Kyian Mbappe ke yi wa abokan wasansa wata alamar da ke nuna yana son su bar fili bayan kammala wasan da ƙungiyar ta yi rashin nasara a wasan ƙarshe na kofin Spanish Super Cup da aka buga a Saudiyya.
A cikin bidiyon an ga yadda Xabi Alonso ya buƙaci Mbappe ya tsaya, amma sai ɗan wasan ya dage, sai kuma aka ga daga ƙarshe Alonso ya haƙura, inda ya bi muradin Mbappe suka fice daga filin.
Lamarin da ya hana ƴan wasan yi wa tawagar Barcelona tsayuwar girmamawa domin karɓar kofin bayan lashe shi a karshen mako.
Masana ƙwallon ƙafa da dama suna kallon hakan a matsayin rashin girmama wasanni, wani abu da ba a taɓa alaƙanta wa da Alonsa ba.
Haka kuma hakan ya nuna cewa ba ƴan wasan ne ke juya ƙungiyar ba kocin ba.
Hukumomi a yankin Kudu maso Yammacin Habasha sun tabbatar cewa an kashe wasu ƴan Turkiyya masu yawon buɗe ido biyu tare da direbansu ɗan Habasha a gundumar Suri da ke yankin Western Omo a safiyar ranar 12 ga Janairu, 2026.
A cewar mai kula da gundumar, Bardula Olepuseni, makiyaya masu ɗauke da makamai waɗanda ba a tantancesu ba ne suka kai harin.
Ya shaida wa BBC cewa maharan sun kai farmaki kan masu yawon buɗe idon ne da nufin sace kayan su.
Shaidun gari sun bayyana cewa ‘yan Turkiyyan sun shafe kwanaki biyu a gundumar Suri kafin su koma, inda aka kai musu hari a kusan karfe 8:20 na safe kuma aka kashe su.
A cikin wata sanarwa, gwamnatin yankin ta ce tana ɗaukar matakai kan waɗanda suka aikata laifin, tare da kira ga al’umma da su taimaka wajen gano da kuma kama maharan.
Mai kula da gundumar ya ce an tura gawarwakin wadanda aka kashe zuwa Addis Ababa.

Asalin hoton, Getty Images
Afirka ta Kudu ta buƙaci Iran da ta janye daga wani babban atisayen sojin ruwa na ƙungiyar BRICS da aka fara ranar 9 ga Janairu, domin kauce wa ƙara taɓarɓarewar dangantakar diflomasiyya tsakaninta da Amurka, kamar yadda gidan talabijin na gwamnati SABC News ya ruwaito.
Ana sa ran za a gama atisayen ranar 16 ga Janairun 2026.
A cewar rahoton, China da Iran sun aika da na'urorin kakaɓar da makamai yayin da Rasha da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) suka tura jiragen yaƙin ruwa, Afirka ta Kudu kuma ta tura jiragen yaƙi ita ma.
Ƙasashen Indonesia, Habasha da Brazil dai sun halarci atisayen a matsayin masu sa ido.
Sai dai an ce jiragen ruwan Iran da suka isa yankin Simon da ke a lardin Western Cape a makon da ya gabata, ba za su ƙara shiga atisayen ba.
Kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta Afirka ta Kudu, Kyaftin Nndwakhulu Thomas Thamaha, ya ce atisayen ya fi mayar da hankali a horo na soja ne kawai, wanda ke nuni da ƙudurin ƙasashen na yin aiki tare.
Atisayen ya ƙunshi na yaƙi da ta’addanci da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su domin kare manyan hanyoyin sufurin ruwa da ayyukan tattalin arziki.

Asalin hoton, Getty Images
Rasha ta sake kai wasu manyan hare-hare da jirgin sama maras matuki da kuma na makami mai linzami a kan biranen Ukraine.
Hukumomin Ukraine sun ce aƙalla mutum huɗu sun rasa rayukansu a birnin Kharkiv da ke gabashin ƙasar.
Rahotanni sun kuma ce an ji fashe-fashe a babban birnin ƙasar, Kyiv, lamarin da ya tayar da hankula a tsakanin mazauna birnin.
Hare-haren sun sake janyo cikas ga rayuwar jama’a, musamman wajen samar da wutar lantarki da makamashin dumama waje.
Ma’aikata na ƙoƙarin dawo da wutar lantarki da hanyoyin samar da makamashi, tun bayan harin da Rasha ta kai kan muhimman kayayyakin samar da makamashi a makon da ya gabata.
A ɗaya ɓangaren kuma, Rasha ta ce Ukraine ta kai mata hari a birnin Taganrog da ke kudancin ƙasar, inda rahotannin da ba a tabbatar ba ke nuna cewa an kai harin ne kan wata masana’antar ƙera jiragen sama marasa matuƙa.

Asalin hoton, Reuters / AFP via Getty Images
BBC ta nemi kotu da ta yi watsi da ƙarar da shugaban Amurka Donald Trump ya shigar, inda yake neman a biya shi diyyar dala biliyan biyar.
Trump ya kai karar ne kan yadda BBC ta gyara wasu kalamansa a cikin wani fim da kafar ta shirya, musamman maganganun da ya yi ranar 6 ga watan Janairu, 2021.
A takardun da aka mika wa kotu, BBC ta ce jihar Florida ba ta da hurumin sauraron ƙarar, kuma harabar kotun da aka shigar da karar ba ta dace ba.
Haka kuma BBC ta ce Trump bai iya tabbatar da cewa fim ɗin ya bata masa suna ba, domin kuwa har ma an sake zaɓensa bayan an nuna fim ɗin.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Nijar ta soke lasisin kamfanonin sufuri sama da talatin da kuma na direbobin manyan motoci, sakamakon ƙin yarda su kai mai zuwa makwabciyar ƙasar Mali bisa dalilan tsaro.
Ƙungiyar JNIM, wadda ke da alaƙa da al-Qaeda, ta kakaba takunkumin hana shigar da mai cikin ƙasar Mali, abin da ya janyo mummunan ƙarancin mai tun daga watan Satumba.
Lamarin ya shafi harkokin sufuri da kasuwanci da rayuwar yau da kullum a ƙasar.
A watan Nuwamba, Nijar ta samu nasarar tura tankokin mai har guda 82 zuwa Mali, ƙarƙashin rakiyar sojoji.
Sai dai duk da wannan yunƙuri, mayaƙan masu iƙirarin jihadi sun ci gaba da kai hare-hare kan ayarin motocin da ke ƙoƙarin shigar da man, abin da ya ƙara tsoratar da direbobi da kamfanonin sufuri.
Rahotanni sun nuna cewa ƙungiyar JNIM na kai hare-hare kan motocin mai ne a matsayin wani ɓangare na yunƙurinta na raunana gwamnatocin yankin.
Sakamakon ƙarancin man, filin jirgin saman Bamako ya soke tashin wasu jirage a ‘yan kwanakin nan.
Nijar, Mali da Burkina Faso duk ƙasashe ne da ke ƙarƙashin mulkin sojoji bayan juyin mulki, kuma sun haɗa kai a ƙarƙashin ƙungiyar haɗin kan ƙasashen yankin Sahel AES.
Ƙasashen sun kuma nisanta kansu daga ƙungiyar ECOWAS, yayin da suke fuskantar ƙalubalen tsaro da na tattalin arziƙi a yankin Sahel.