Me ya sa Alonso ya raba gari da Real Madrid?

Guillem Balague

Asalin hoton, BBC Sport

Lokacin karatu: Minti 5
Real Madrid former boss Xabi Alonso

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Xabi Alonso ya yi aikin wata bakwai kawai a matsayin kocin Real Madrid

An ga wasu bidiyoyi da suka yaɗu, inda Kylian Mbappe ke yi wa abokan wasansa wata alamar da ke nuna yana son su bar fili bayan kammala wasan da ƙungiyar ta yi rashin nasara a wasan ƙarshe na kofin Spanish Super Cup da aka buga a Saudiyya.

A cikin bidiyon an ga yadda Xabi Alonso ya buƙaci Mbappe ya tsaya, amma sai ɗan wasan ya dage, sai kuma aka ga daga ƙarshe Alonso ya haƙura, inda ya bi muradin Mbappe suka fice daga filin.

Lamarin da ya hana ƴan wasan yi wa tawagar Barcelona tsayuwar girmamawa domin karɓar kofin bayan lashe shi a karshen mako.

Masana ƙwallon ƙafa da dama suna kallon hakan a matsayin rashin girmama wasanni, wani abu da ba a taɓa alaƙanta wa da Alonsa ba.

Haka kuma hakan ya nuna cewa ba ƴan wasan ne ke juya ƙungiyar ba kocin ba.

Bayan hakan ne kuma Xabi ya sauya tunani game da aikinsa.

Amma wannan ba ritaya ba ce, ba abu ne kuma da ya shiryawa ba.

Ba a yi tsammanin Alonso zai bar Madrid ba - wata bakwai da rabi bayan fara horas da ƙungiyar da ya taka wa leda a baya.

A cikin sanarwar da Madrid ta fitar a hukumance, ƙungiyar ta bayyana rabuwa da kocin da cewa an yi hakan ne ''bisa amince da juna'', amma kuma rabuwa ce da babu makawa.

Dalilan Madrid na rabuwa da Alonso

Bayan rashin jituwa mai yawa da ta riƙa samu da kocinta kan dabaru da salon wasa, na tsawon watanni, a ranar Litinin da maraice ne, hukumar gudanarwar ƙungiyar ta yi wani zama da nufin raba gari da Alonso.

An yi masa bayanai masu gamsarwa, amma kuma masu harshen damo da suka haɗa:

  • Kasa aiwatar da dabarun da suka kai shi ga nasara a ƙungiyar Bayer Leverkusen.
  • Ƙarfin ƙungiyar bai kai yadda take buƙata ba.
  • Ƴan wasa sun kasa ƙara ƙoƙari'.
  • Wasan da suke bugawa bai nuna nasa ba ne.

An kuma lissafo rashin narasar da ya samu a ƙungiyar da suka haɗa da: Dioke ƙungiyar ta PSG ta yi a wasan kusa da ƙarshe na Gasar Kofin Duniya na Ƙungiyoyi da kuma ci 5-2 da Atletico Madrid ta yi wa ƙungiyar a Gasar La Liga.

To amma yanzu haka Madrid na mataki na takwas a teburin Gasar Zakarun Turai, gasar da ke fayyace ƙarfin ƙungiyar.

Haka kuma sun kai matakin gaba a Gasar Copa del Rey, kuma suna mataki na biyu a teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Barcelona ta ɗaya, kuma sun doke Barca a lokacin da suka kara cikin watan Oktoba.

Matsalolin da Alonso ya fuskanta a Madrid

Vinicious

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An tabbatar da cewa dama shugaban ƙungiyar Florentino Perez ba ya son aikinsa a ƙungiyar.

An ba shi shawarar ɗauko Xabi Alonso ne ba tare da gamsuwa da shi ba.

Bayanai na cewa ko a tsohuwar ƙungiyar tasa ma, Bayer Leverkusen ba kowa ba ne cikin mahukuntan ƙungiyar ya amince da ɗaukarsa.

To amma sai ya yi sa'ar samun haɗin kan ƴanwasan ƙungiyar.

Amma a Madrid duk da nasarorin da ya samu, bai samu haɗin kan ƴan wasan ba, wannan ne matsalarsa ta farko.

Kowane koci na da ƙarfi da kwarjini a lokacin da ya je ƙungiya, amma ƴan wasan Madrid sun nuna masa raini tun farkon zuwansa.

Ya so fara aiki ne bayan Gasar Kofin Duniya ta Ƙungiyoyi, ba kafinta ba.

An buga gasar bayan doguwar kaka da ƴan wasan suka buga, yayin da suka gaji, wasu ke tunanin hutu, wasu kuma ke tunanin sabbin ƙungiyoyin da za su koma, bayan ƙarewar wa'adinsu.

Amma ba a bai wa Alonso damar tattauna hakan ba.

Samun matsala da Vinicius Junior ne farkon abin da haifar masa cikas.

Ɗan wasan ya ɗora laifin rashin ƙoƙarinsa kan Alonso, sannan ya nuna ɓacin ransa ƙarara a cikin fili bayan sauya shi a wasan El Clasico, daga baya ya bai wa kowa hakuri, amma ban da Alonso.

Daga nan aka jingine maganar tsawaita kwantiragin ɗan wasan don ganin abin da zai faru da Alonso.

Matsalar jinya da ƴanwasan bayan ƙungiyar suka fuskanta.

Sannan ƙungiyar ta yi watsi da buƙatarsa na ɗauko ɗan wasan tsakiyar da yake so: Martin Zubimendi.

Babu haɗin kan manyan ƴanwasa don haɗe kan ƙungiyar.

Ko shi Federico Valverde ya fi damuwa da wujrin da zai buga wasa maimakon haɗin kan ƙungiyar.

Shi ma Mbappe ya fi mayar da hankali kan kafa tarihi, maimakon taimaka wa ƙungiyar, inda ya ƙi yin abin da ya kamata don warkewa daga raunin da yake da shi yanzu, don kawai kamo tarihin da Ronaldo ya kafa na cin ƙwallo 59 cikin shekara guda.

Xabi bai taɓa shawo kan ƴan wasan cewa ra'ayinsa shi ne daidai ba.

Kuma idan babu wannan ba zai iya yin aikinsa yadda ya kamata ba, har ya yi kamar ƙoƙarin da ya yi a Leverkusen.

Me ya rage wa Alonso yanzu?

Alonso

Asalin hoton, Getty Images

Dole ya yanke shawarar me ya kamata ya yi, hutawa zai yi don samun nutsjuwar inda zai koma?

Waɗanda suka san shi suna cewa barin Madrid a yanzu, duk da cewa ba haka ya so ba, zai zama hutu a gare shi, yayin da wasu ke da saɓanin ra'ayin hakan.

To amma da alama manyan ƙungiyoyin Turai za su buƙace shi a kaka mai zuwa, idan damar hakan ta samu.

A nata ɓangare Real Madrid za ta mayar da hankali kan sabon kocinta don ganin ko zai fitar mata kitse daga wuta, ko kuwa shi ma zai bi sahun Alonso.

Wane ne Arbeloa sabon kocin Madrid?

Alvaro Arbeloa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Alvaro Arbeloa ya shafe shekara biyar yana horas da ƙaramar ƙungiyar Madrid

A yanzu ta naɗa Alvaro Arbeloa, kocin ƙaramar ƙungiyar, wanda ya taɓa buga wa ƙungiyar wasanni a baya.

Sabon mai horaswar ya yi shekara biyar a matsayin kocin ƙaramar ƙungiyar a Bernabeu amma bai taɓa jagorantar babbar ƙungiyar ba.

Arbeloa ya taɓa buga wa Liverpool wasa kafin komawa Madrid inda ya lashe Kofin Zakarun Turai sau biyu tare da shi.

Ya kuma taɓa cin Kofin Duniya tare da Sifaniya.

Sai dai masana wasanni na ganin cewa aikin da ke gabansa ba ƙarami ba ne.

Inda wasu ke ganin idan tsohon shahararren ɗan wasan ƙungiyar kamar Xabi Alonso ya kasa sauya al'adar ƙungiyar, da alama Arbeloa zai fuskanci jan aiki a gabansa.

Idan har ya ƙare kakar bana ba tare da kofi ba, zai yi wahala ƙungiyar ta bar shi.

Amma idan ya yi sa'a ƙungiyar ta ɗauki wani kofi, to wataƙila ya tsallake siraɗi.