Ko APC da Tinubu za su iya hana tsige Fubara?

Rivers
Lokacin karatu: Minti 5

A daidai lokacin da siyasar jihar Rivers ke ƙara ɗaukar zafi, musamman kan sake yunƙurin majalisar jihar ta tsige Gwamna Sim Fubara, masu sharhi kan harkokin siyasa sun fara muhawara kan abubuwan da za su iya faruwa.

A ranar Alhamis, 8 ga watan Janairun 2026 ne dai majalisar jihar Rivers ta sake bijiro da batun yunƙurin tsige gwamna jihar, bayan musayar yawu da takun-saƙa da aka lura akwai a tsakaninsu.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Major Jack ne ya gabatar da takardar neman majalisar ta fara yunƙurin tsige gwamnan, bisa zarginsa da aikata manyan laifuka da ya ce sun saɓa da doka.

Ya ce sun yi la'akari ne da sashe na 188 na kundin tsarin mulkin Najeriya wajen tattarawa da tantace laifukan da suke ganin gwamnan ya yi, waɗanda kuma suke ganin sun saɓa da doka.

Daga cikin laifukan da suke zargin shi da aikatawa akwai:

  • Rushe ginin majalisar dokokin jihar
  • Kashe kuɗin ba tare da kasafi ba
  • Riƙe kuɗin gudanar da ayyukan majalisa
  • Ƙin yin biyayya ga umarnin kotun ƙoli na bai wa majalisar ƴancin kanta
  • Naɗa muƙamai ba tare da amincewar majalisa ba

Ƴan majalisar guda 26 cikin 32 ne suka sanya hannu a takardar buƙatar, sannan shugaban masu rinjayen ya miƙa takardar ga shugaban majalisar.

Sai dai gwamnan ya mayar ta martani kan batun, inda ya buƙaci ƴan jihar da magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu kan matsalar, sannan ya yi nuni da cewa yana tare da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.

Tuni dai majalisar ta yi zargin akwai wasu mutane da ta ce suna yunƙurin daƙile yunƙurin da ƴan majalisar ke yi na tsige gwamnan da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu.

Majalisar ta yi iƙirarin cewa waɗannan mutane na neman samun umarnin daga Babbar Kotun Jihar Rivers da ke wajen birnin Fatakwal don dakatar da yunƙurin.

Wannan ne karo na biyu da majalisar ta yi yunƙurin tsige Fubara, domin a bara ma sun yi irin wannan yunƙurin, lamarin da ya haifar da hargitsi a jihar har aka kai ga ƙaƙaba dokar ta-ɓaci.

Rawar Tinubu da APC

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai ganin yadda batun ya taso jim kaɗan bayan gwamnan ya koma jam'iyyar APC mai mulki, sai ake ganin wannan sake yunƙurin zai jefa shugaban Najeriya Bola Tinubu da ma uwar jam'iyya cikin tsaka mai wuya.

Domin jin yadda ya kamata Tinubu ya fuskanci lamarin, BBC ta tuntuɓi Dokta Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a, inda har yanzu ƴan majalisar jihar Rivers mutanen Wike ne.

A game da za a iya tsige shi, Sufi ya ce, "zai yiwu su tsige Fubara duk da komawarsa APC. Ai kuma an ga Nyesome Wike ya ziyarci ƴan majalisar a makon jiya, kuma sun masa tarba mai kyau."

Masanin siyasar ya ce akwai yiwuwar Wike ya tura ƴan majalisar ne su fara share masa hanya.

"Wataƙila aika su ya yi ko kuma ya ba su su riƙe masa domin hana fuskantar ƙalubale daga ɓangaren gwamna," in ji Sufi.

A game da ko Tinubu da APC za su zura ido a tsige musu gwamna, Sufi ya ce Tinubu ba zai bari ba.

Ita dai APC tuni ta nuna cewa Fubara ne jagoran jam'iyyar a jihar ta Rivers, sannan ta nuna cewa ya kamata ministan na Abuja ya daina sa mata baki a harkokinta kasancewar ba ya cikinta, lamarin da ya ƙara harzuƙa Wike.

"Yanzu haka ana ganin akwai shirye-shiryen neman maslaha ko ba gwamnan kariya da ake tunanin fadar shugaban ƙasa ke yi. Dama a baya ai duk wata matsala da ta taso daga Rivers, fadar Tinubun ce aka zuwa domin neman maslaha," in ji Kabiru Sufi.

A game da tsaka mai-wuya da ake tunanin Tinubu ya shiga kan zaɓin wanda zai mara wa maya tsakanin Wike ko Fubara baya, Sufi ya ce akwai ƙalubale a gaban shugaban, "amma Wike minista ne a gwamnatin Tinubu, don haka Tinubu ne kaɗai ne zai iya magance matsalar."

Amma masanin siyasar ya ce akwai wata matsalar, musamman kan burin Fubara na neman wa'adi na biyu.

"Idan Fubara ya koma wa'adi na biyu to daga lokacin Wike ba shi da wani kataɓus, sannan kuma suma ɗin kusan za a iya cewa babu wani aiki da zai musu a irin wannan lokacin."

Sai dai duk da haka masanin siyasar ya ce duk wata matsalar da ake tunani, fadar shugaban ƙasa za ta iya magance ta, domin a cewarsa, Tinubu ne ke da wuƙa da nama kan komai.

"Sai dai kuma yadda Wike zai karɓa matsayar gwamnati ne abun lura. Ko ya haƙura ya aminta cikin sauƙi, ko kuma ya yi yunƙurin yin tutsu, wannan kuma lokaci ne kawai zai nuna," in ji shi.

Yadda rikicin ya samo asali

Ana kallon rikici tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers, da ubangidansa Minista Nyesom Wike a matsayin fafutikar ƙwatar iko da siyasar jihar mai arzikin man fetur.

Kusan za a iya cewa Wike ne ya uwa ya yi makarɓiya wajen tabbatar da Fubara ya zama gwamnan jihar domin ya gaje shi bayan ya kammala wa'adinsa na biyu na mulki.

Tun a shekarar 2023 bayan samun nasara a zaɓen ne shugabannin biyu suke takun-saƙa a kan jan ragamar jihar, lamarin da ya sa siyasar jihar ta ɗauki zafi, har ta zama abar kallo da magana a faɗin ƙasar.

Tun a farko-farkon mulkin Fubara aka fara rikici a game da shugabannin ƙananan hukumomi, inda bayan wa'adin waɗanda Fubara ya gada daga Wike ya ƙare, ya buƙaci su tafi, su kuma suka ce allambaran suna da sauran lokaci.

Ana cikin wannan ne ya sanar da naɗa shugabannin riƙon ƙwarya domin su maye gurbin waɗancan, lamarin da ya tayar da tashin hankali a jihar.

Kafin nan, an yi rigima wajen zaɓen shugabannin PDP na jihar Rivers, inda tsagin Wike na PDP ya samu a nasara a kan tsagin Fubara, lamarin da ya haifar da saɓani mai girma tsakanin Wike da ƙungiyar gwamnoni, har Wiken ya yi barazanar kunna wutar siyasa a duk jihar da ta sa baki a jiharsa.

Daga baya ƴan majalisar jihar da ke tare da Fubara sun sanar da tsige mafi yawan ƴan majalisar da ke tare da Wike, lamarin da ya ƙara ta'azzara rikicin siyasar jihar, sannan Fubara ya gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi, inda mutanensa suka lashe.

Daga bisani kotun ƙoli ta ta soke zaɓen, sannan ta soke cire ƴan majalisun, tare da umartar Fubara ya je gabansu ya gabatar da kasafin kuɗi.

Ana cikin haka ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da gwamnan, tare da naɗa gwamnan riƙon-ƙwarya na wata shida, sannan ya jagoranci sulhunta Wike da Fubara.

Bayan sulhun ne aka yi sabon zaɓen ƙananan hukumomi, inda mafi yawansu suka kasance na kusa da Wike.

Sai tun bayan da Fubara ya sanar da komawa APC ne rikici ya ƙara komawa ɗanye, inda aka fara rikici kan waye ya kamata ya jagoranci tallata Tinubu.