Dalilan da suka sa Majalisar Rivers ta sake ƙaddamar da shirin tsige Fubara

Rivers

Asalin hoton, Rivers state Government House Media

Lokacin karatu: Minti 3

Rikicin siyasar jihar Rivers ya sake ɗaukar zafi bayan majalisar dokokin jihar ta sake ƙaddamar da shirin tsige gwamna Siminilaya Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu.

An bijiro da maganar tsige gwamna ne a zaman majalisar na ranar Alhamis, 8 ga watan Janairun 2026.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Major Jack ne ya karanta takardar neman majalisar ta ƙaddaamar da shirin tsige gwamnan, bisa zargin shi da aikata manyan laifuka da ya ce sun saɓa da doka.

Ya ce sun yi la'akari da sashe na 188 ne na kundin tsarin mulkin Najeriya wajen tattarawa da tantace laifukan da suke ganin gwamnan ya yi, waɗanda kuma suke ganin sun saɓa da doka.

Daga cikin laifukan da suke zargin shi da aikatawa akwai:

  • Rushe majalisar dokokin jihar
  • Kashe kuɗin da ba a kasafta ba
  • Riƙe kuɗin gudanar da ayyukan majalisa
  • Ƙin yin biyayya ga umarnin kotun ƙoli na bai wa majalisar ƴancin kanta
  • Naɗa muƙamai ba tare da amincewar majalisar ba

Ƴan majalisar guda 26 cikin 32 ne suka sanya hannu a takardar buƙatar, sannan shugaban masu rinjayen ya miƙa takardar ga shugaban majalisar.

Shugaban majalisar, Amaewhule ya ce za su miƙa takardar zuwa ga gwamnan a cikin kwana bakwai.

Zargin mataimakiyar gwamna

Bayan laifukan da majalisar take zargin gwamnan da aikatawa, mataimakiyar shugaban masu rinjaye na majalisar, Linda Stewart ta gabatar da takardar ƙorafe-ƙorafe kan mataimakiyar gwamnan jihar, Farfesa Ngozi Odu.

Daga cikin laifukan da ake zarginta da aikatawa akwai:

  • Kashe kuɗin gwamnati ba tare da ƙa'ida ba
  • Hana majalisar gudanar da ayyukanta kamar yadda doka ta tsara
  • Haɗa baki wajen naɗa muƙamai ba tare da amicewar majalisa ba
  • Gabatar da kasafin kuɗi a gaban wasu ƴan majalisa daban
  • Riƙe albashin ƴan majalisar

Tsakanin Wike da Fubara

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ana kallon rikici tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers, da ubangidansa Minista Nyesom Wike a matsayin fafutikar ƙwatar iko da siyasar jihar mai arzikin man fetur.

Kusan za a iya cewa Wike ne ya uwa ya yi makarɓiya wajen tabbatar da Fubara ya zama gwamnan jihar domin ya gaje shi bayan ya kammala wa'adinsa na biyu na mulki.

Tun a shekarar 2023 bayan samun nasara a zaɓen ne shugabannin biyu suke takun-saƙa a kan jan ragamar jihar, lamarin da ya sa siyasar jihar ta ɗauki zafi, har ta zama abar kallo da magana a faɗin ƙasar.

Tun a farko-farkon mulkin Fubara aka fara rikici a game da shugabannin ƙananan hukumomi, inda bayan wa'adin waɗanda Fubara ya gada daga Wike ya ƙare, ya buƙaci su tafi, su kuma suka ce allambaran suna da sauran lokaci.

Ana cikin wannan ne ya sanar da naɗa shugabannin riƙon ƙwarya domin su maye gurbin waɗancan, lamarin da ya tayar da tashin hankali a jihar.

Kafin nan, an yi rigima wajen zaɓen shugabannin PDP na jihar Rivers, inda tsagin Wike na PDP ya samu a nasara a kan tsagin Fubara, lamarin da ya haifar da saɓani mai girma tsakanin Wike da ƙungiyar gwamnoni, har Wiken ya yi barazanar kunna wutar siyasa a duk jihar da ta sa baki a jiharsa.

Daga baya ƴan majalisar jihar da ke tare da Fubara sun sanar da tsige mafi yawan ƴan majalisar da ke tare da Wike, lamarin da ya ƙara ta'azzara rikicin siyasar jihar, sannan Fubara ya gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi, inda mutanensa suka lashe.

Daga bisani kotun ƙoli ta ta soke zaɓen, sannan ta soke cire ƴan majalisun, tare da umartar Fubara ya je gabansu ya gabatar da kasafin kuɗi.

Ana cikin haka ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da gwamnan, tare da naɗa gwamnan riƙon-ƙwarya na wata shida, sannan ya jagoranci sulhunta Wike da Fubara.

Bayan sulhun ne aka yi sabon zaɓen ƙananan hukumomi, inda mafi yawansu suka kasance na kusa da Wike.

Sai tun bayan da Fubara ya sanar da komawa APC ne rikici ya ƙara komawa ɗanye, inda aka fara rikici kan waye ya kamata ya jagoranci tallata Tinubu.