Majalisar dokokin Ribas ta kuduri aniyar binciken kantoman riko Ibok-Ete Ibas

Vice Admiral (Rtd) Ibok-Ete Ekwe Ibas

Asalin hoton, RSGH Press

Lokacin karatu: Minti 3

Wani sabon rikici na neman kunno kai a jihar Ribas da ke Kudu maso Kudancin Najeriya, bayan da 'yan majalisar dokokin jihar suka kuduri aniyar gudanar da bincike kan harkokin kudi na gwamnatin a tsawon watanni shida karkashin jagorancin Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), da ya jagoranci jihar bayan shugaba Tinubu ya kafa dokar ta baci a jihar.

Ana ganin cewa matakin da 'yan majalisar suka dauka zai iya janyo takun saka tsakaninsu da tsohon kantoman riko na jihar, wanda a halin yanzu ake bin bahasin aikin sa.

Majalisar ta jaddada cewa huruminta ne ta gudanar da bincike kan harkokin kudaden jihar, wanda Ibok-Ete-Ibas ya ce ba huruminsu ba ne.

Sanarwar da Majalisar Dokokin jihar Ribas din ta fitar game da shirin binciken tsohon kantoman rikon na neman sake tayar da wata rikita-rikitar siyasa inda wasu 'yan jihar suka ce dama suna jiran wannan rana ta zo.

A na sa ran binciken zai bi bahasin yadda Ibas ya tafiyar da harkokin kudaden jihar a lokacin dokar ta-baci da aka sanya a jihar.

Binciken da 'yan majalisar suka ayyana gudanarwa kan Ibas, ya samo asali ne

daga zarge-zargen rashawa da kuma gurgunta kananan hukumomin jihar a lokacin

da ya ke rikon kwarya ciki har da bijirewa umarnin kotu da ta hana shi nada shugabannin kananan hukumomi 23 na riko a jihar.

Kungiyoyin farar hula daga shiyyar Naija Delta sun nemi a gudanar da bincike kan Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, bisa zargin yin amfani da karfin mulki da kuma karkatar da kudaden jama'a.

Matakin da suka dauka na binciken Ibas dai na ci gaba da haifar da cece-ku-ce, inda wasu kungiyoyi farar hula ke yabawa gwamnatinsa kan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, yayin da wasu kuma ke sukar gwamnatinsa bisa zargin kin aiki da abin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Alhaji Yahaya Wunti, me bibiyar dambarwar siyasar jihar ta Ribas ne da ma yankin Naija Delta, ya shaida wa BBC cewa, majalisar dokokin jihar ta Ribas ta ce ta dauki wannan mataki ne domin jin bahasin abin da aka yi da makudan kudin da jihar ta samu a tsawon watanni shida na mulkin Ibas.

Ya ce," Kudin da jihar ta samu sun kai kusan naira biliyan dari biyu da hamsin da wani abu, kuma a yadda al'ummar jihar da ma 'yan majalisar dokokin jihar ke fada manyan ayyuka na raya kasa da dama sun tsaya ba wanda aka ci gaba tun barin gwamna Fubara mulki."

Alhaji Yahaya Wunti, ya ce," Akwai ma wadanda ke cewa albashin watan Agusta Daya gabata ma sai da gwamna Fubara ya dawo kan mulki ya bayar da umarnin a biya, sannan kuma akwai masu maganar cewa an yi almubazzaranci da kudi wajen yin wasu ayyuka kamar misali sanya kyamarori na tsaro a gidan gwamnati sai da aka ware naira biliyan 22."

Yanzu haka dai tsohon kantoman rikon jihar ta Ribas, Ibok-Ete Ibas, ya yi watsi da

binciken, inda ya bayyana shi a matsayin wani aiki na wauta, sannan kuma ya cewa 'yan majalisar ba su da hurumin bincikensa, bisa la'akari da cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ne ya nada shi.

Masana harkokin siyasa dai na cewa ba a bin mamaki ba ne idan sakamakon binciken ya yi matukar tasiri ga siyasar jihar Ribas da kuma sahihancin gwamnati mai ci kan binciken gwamnatin rikon kwaryar.

Ana sa ran binciken zai yi karin haske kan yadda ake tafiyar da harkokin kudaden jihar a zamanin Ibas.

Matakin da majalisar ta dauka na binciki Ibas ya sanya ayar tambaya kan yadda ake gudanar da ayyukan gwamnati.

Dokar ta baci, da aka sanya a jihar wani yunkuri ne na dakile tabarbarewar harkokin siyasa da tsaro, inda wa'adin dokar ya kare a ranar 17 ga Satumba, 2025.

Masana na cewa wannan barazanar ka iya sake dawo da rashin zaman

lafiya tun bayan kafa dokar ta baci a jihar.