Sukar da Tinubu ke sha bayan ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers

Bola Tinubu

Asalin hoton, State House

Lokacin karatu: Minti 5

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bai wa 'yan Najeriya mamaki lokacin da ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers a makon da ya gabata sakamakon rikicin siyasar da ya mamaye jihar.

A matakin da ya ɗauka, Tinubu ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da kuma majalisar dokokin jihar tsawon wata shida, sannan ya naɗa kantoman riƙo wanda tsohon sojan ruwa ne Vice Admiral Ibok-Ete Ibas a matsayi gwamna.

Har yanzu wannan matakin na jawo cecekuce a ƙasar, inda wasu manyan mutane ke sukar matakin tare da matsa wa shugaban ƙasar da ya sauya shawara.

A gefe guda kuma wasu na goyon bayan matakin na Tinubu.

Ga wasu muhimman abubuwa biyar da suka faru tun bayan ayyana matakin.

Gwamnonin PDP da 'yan gwagwarmaya sun tafi kotu

Wasu daga cikin gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyyar adawa ta PDP sun garzaya Kotun Ƙolin Najeriya domin neman fatawa game da abin da sashe na 305 na kundin mulkin ƙasar ke nufi.

Gwamonin da ke kan gaba a shigar da ƙarar su ne na jihohin Adamawa, Bauchi, Bayelsa, Enugu, Osun, Filato, Zamfara.

Daga cikin abubuwan da suke nema akwai neman kotun ta ɗauki matsaya kan ko sashen na 305 na kudin mulkin Najeriya na 1999 ya bai wa shugaban ƙasa dama ya dakatar da zaɓaɓɓen gwamna da mataimakinsa da majalisar dokoki ta jiha, kuma ya naɗa wani gwamnan riƙo a ƙarƙashin dokar ta-ɓaci.

Matakin na zuwa bayan huɗu cikin shida na gwamnonin yankin kudu maso kudu sun yi tir da dokar da Tinubu ya ayyana a Rivers.

Gwamnan Bayelsa Duoye Diri, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin, ya ce "rikicin siyasar na Rivers bai kai abin da za a ayyana dokar ta-ɓaci a kai ba kamar yadda sashe na 305(3) ya tanada".

Sai dai kuma, gwamnonin Edo da na Cross River sun goyi bayan matakin na Shugaba Tinubu.

A gefe guda kuma, ƙungiyar neman shugabanci na gari ta Socio-Economic Rights and Accountability Project (Serap) ta ce ta shigar da Tinubu ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja game da dakatar da gwamnan Rivers da mataimakinsa da majalisar dokoki "wanda ya saɓa wa doka".

Sukar majalisar tarayya kan goyon bayan matakin

Godswill Akpabio ne shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

Asalin hoton, Nigeria Senate

Bayanan hoto, Godswill Akpabio ne shugaban Majalisar Dattawan Najeriya
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani abin da ya ƙara jan hankalin 'yan Najeriya shi ne yadda majalisun tarayya na dattawa da ta wakilai suka amince da matakin dokar da shugaban ƙasar ya ayyana.

A cewar kundin mulkin Najeriya, shugaban ƙasa na buƙatar amincewar biyu cikin uku na 'yanmajalisar tarayya kafin dokar ta fara aiki.

Duka majalisar dattawa da ta wakilai sun kaɗa ƙuri'un amincewa, amma maimakon su kaɗa ƙuri'a ɗaya bayan ɗaya, sai suka yi amfani da ƙuri'ar baki kawai - inda masu goyon baya suka yi ihun "eh" waɗanda ke adawa suka yi ihun "a'a", kuma a ƙarshe aka ce masu "eh" sun fi yawa.

Afam Osigwe babban lauya ne kuma shugaban ƙungiyar lauyoyi ta Nigerian Bar Association (NBA), kuma ya ce ba irin wannan salon kaɗa ƙuri'ar kundin mulki ya ce a yi ba.

"Idan kana so ka tabbatar ka samu rinjayen biyu cikin uku, dole ne ka nuna ƙarara adadin mutanen da suka halarci zaman, da mutanen da suka kaɗa ƙuri'ar amincewa ko akasin haka, da mutanend suka ƙaurace, kuma ba zai yiwu ka samu hakan a ƙuri'ar baki ba," kamar yadda ya bayyana.

"Saboda haka, amfani da ƙuri'ar baki a majalisa shi ma ya saɓa wa kundin mulki."

Adadin 'yanmajalisar wakilai 360 ne, majalisar dattawa kuma 109. Saboda haka dole sai an samu 240 da kuma 73 a majalisun da suka amince.

Aminu Tambuwal, tsohon gwamnan Sokoto kuma sanata a yanzu, ya ce yana da tabbas adadin sanatocin da suka halarci zaman majalisar ma domin kaɗa ƙuri'a ba su kai 73 ba.

"Ban sani ba ko ku 'yanjarida kun duba rajista domin sanin yawan sanatocin da suka halarci zaman, ni dai ban ga mutanen da suka kai 73 ba a majalisa," kamar yadda ya faɗa wa jaridar Sun ranar Lahadi.

An ci mutuncin doka - Jonathan

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana ayyana dokar a matsayin "cin mutuncin doka da aiki da alfarmomin" da kundin mulkin Najeriya ya bai wa shugabanni.

Tsohon shugaban wanda shi me ya saka irin wannan doka a jihohin Borno da Yobe a 2013 - amma bai dakatar da gwamnoni da majalisa ba - ya ce mutanen da ke tafiyar da wannan lamari sun abin da ya dace "amma sai suka yi kamar suna barci kuma abu ne mai wuya ka iya tashin mutumin da ya fake cewa barci yake yi".

Ya ƙara da cewa irin wannan matsalar ce ke jawo fasfon Najeriya ya daina daraja a idon ƙasashen duniya kuma "ya hana masu zuba jari kawo kuɗinsu cikin ƙasa".

Soyinka, mai goyon bayan Tinubu, ya soki matakin

Mai riƙe da lambar yabo ta Nobel, Farfesa Wole Soyinka, wanda aka sani da goyon bayan Shugaba Tinubu, ya soki matakin shugaban yana mai cewa "abin ya yi yawa".

"Ina ganin sare ƙafar dimokudraɗiyya gaba ɗaya irin haka a Rivers ya yi yawa. Ina ganin ya kamata a ce shugaban ya tunkari abin ta fuskar tattalin arziki," a cewarsa.

Soyinka ya ce yana fatan waɗanda abin ya shafa za su je kotun ƙoli domin "mu samu cikakken bayani kan komai ta yadda za mu san ko hakan yana kan doka ko kuma a'a".

Fubara ya bayyana a bainar jama'a bayan dakatar da shi

Yayin da wannan ke faruwa, gwamnan da aka dakatar Siminalayi Fubara ya fito bainar jama'a karon farko bayan dakatar da shi domin halartar addu'o'i a cocin Salvation Ministries da birnin Fatakwal ranar Lahadi.

Bai ce wa 'yanjarida komai ba, amma hakan ya kore raɗe-raɗin da ake yi cewa gwamnan ya fice daga jihar.