Wane ne Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, sabon gwamnan riƙon ƙwarya na jihar Rivers?

Asalin hoton, Ibok-Ete Ekwe Ibas
A ranar Talatar nan ne dai shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya naɗa Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas a matsayin kantoman jihar Rivers bayan da ya sanar da ƙaƙaba wa jihar dokar ta-baci.
Shugaba Tinubu ya yi amfani da sashen kundin tsarin mulkin Najeriya na 305(5) na 1999 wajen ayyana dokar ta-ɓacin.
Bola Tinubu ya dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu tare da ƴan majalisar dokokin jihar har na tsawon watanni shida.
Wane Ibok-Ete Ekwe Ibas?
Ibok-Ete Ekwe Ibas tsohon sojan ruwa mai muƙamin Vice Admiral wanda ya kasance babban hafsan sojojin ruwa na 22 a Najeriya daga shekarar 2015 zuwa 2021.
An haifi Ibok-Ete a shekarar 1960 a garin Nko da ke jihar Cross River a kudu maso kudancin Najeriya.
Ibok ya shiga makarantar koyon aikin soji ta NDA, a shekarar 1979 inda ya fito a matsayin ƙaramin laftanar a 1983.
Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe ya riƙe muƙamai da dama a rundunar sojin ruwan Najeriya sannan kuma ya jagoranci rundunar sojoji mai yaƙi a wurare da dama a Najeriya da suka haɗa da NNS Ruwan Yaro da NNS Obuma da kuma NNS Aradu.
Tsohon sojan ya kuma halarci kwasa-kwasai masu yawa a ciki da wajen Najeriya.










