Mece ce makomar Gwamnan Rivers, Simi Fubara a siyasa?

Asalin hoton, Rivers state Government House Media
Kallo ya fara komawa sama a siyasar jihar Rivers, wadda dambarwarta ta karaɗe batun siyasar ƙasar na tsawon lokacin tun bayan da aka fara takun-saƙa tsakanin Gwamnan Jihar, Siminilayi Fubara, da tsohon mai gidansa, Ministan Abuja, Nyesome Wike.
A kwanakin baya ne Kotun Ƙoli ta soke zaɓen ƙananan hukumomin jihar, sannan ta umarci babban akanta da babban bankin Najeriya CBN da su daina ba jihar kasonta na tarayya na wata-wata, har sai gwamnan ya sake gabatar da kasafin kuɗi a gaban halastattun shugabanninin majalisar dokokin jihar.
Tuni gwamnan ya amince da hukuncin kotun, inda ya umarci shugabannn ƙananan hukumomin jihar su sauka, sannan ya sanar da cewa za a sake zaɓen nan da wani lokaci.
Sai dai har yanzu ana ta kwan-gaba-kwan-baya tsakaninsa da ƴan majalisar, waɗanda ake tunanin mafi yawansu mutanen Wike ne.
Da farko majalisar, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Martin Amaewhule, ta buƙaci gwamnan ya bayyana a gabanta domin gabatar da kasafin kuɗin, inda ta ba shi awa 44, inda har wa'adin ya ƙare gwamnan bai je ba, kuma bai ce komai kan gayyatar ba.
Daga bisani ya gayyace su gidan gwamnati, inda suma suka ƙi amsa gayyatar. Sannan a ranar 12 ga watan Maris, gwamnan ya je majalisar domin gabatar da kasafin, amma ya tarar da majalisar a kulle.
Makomar gwamnan a siyasance
Ganin yadda takun-saƙar ke ƙara ruruwa tsakanin gwamnan da ƴan majalisar ne ya sa ake tambayar ko yaushe za a gama wannan rigimar? da kuma ko gwamnan zai tsallake rijiyar da ake haƙawa?
Ko a ranar Talata, Nyesom Wike, ya ce babu abin da zai faru idan majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin Amaewhule ɗin ta tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce ƴanmajalisar ba su yi laifi ba idan suka yanke shawarar tsige Fubara, saboda ya aikata laifukan da suka cancanci a tsige shi, ciki kuwa har da riƙe musu albashi na tsawon watanni.
Domin jin yaya makomar gwamnan za ta kasance da kuma irin matakai ko zaɓin da suke rage masa, BBC ta tuntuɓi Farfesa Farfesa Tukur Abdulkadir na Jami'ar Jihar Kaduna da Malam Kabiru Sufi masanin kimiyyar siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano, inda suka ce zaɓin kaɗan ne suka rage wa gwamnan.
A game da makomar gwamnan, Farfesa Tukur ya ce maganar komawa, "wannan sai Allah," inda ya ƙara da cewa "amma akwai abubuwa da suke nuna akwai matsaloli."
"Ko jiya ka ga an samu taƙaddama a lokacin da gwamna ya je gabatar da kasafin kuɗi, kakakin majalisa ya ce bai sani ba, shi kuma gwamna ya ce sun yi magana da shi. Saboda haka ina ganin har yanzu akwai sauran rina a kaba domin alamu na nuna cewa ɓangarorin biyu ba su shirya yin sulhu da juna ba," in ji shi.
Farfesan ya ce rashin sulhun ba zai yi wa dukkan ɓangarorin daɗi ba domin a cewarsa akwai alama duk sun lashi takobin ganin bayan juna, inda ya ce, "akwai buƙatar dai su koyi darussa na irin matsaloli da suka dabaibaye jam'iyyun baya, wannan kuma kukan kuciya ne."
Malamin jami'ar ya ce a halin yanzu idan gwamnan bai nemi sulhu ba, "kusan shi ne za a ce ba zai kai ga gaci ba tunda ba shi da goyon bayan ƴan majalisa mafiya yawa. Saboda haka dole shi ne zai nemi sulhu, tunda an ce durƙusawa wada ba gajiya ba ne, don haka duk da cewa akwai wahala, amma shi ne ya kamata ya yi hakuri maimakon ya ɗauka matakin fito na fito wanda nake ganin ba zai taimaki siyasarsa ba da zaman lafiyar jihar ba."
A nasa ɓangaren, Malam Kabiru Sufi ya ce abubuwa biyu ne suka rage wa gwamnan, "ya yi ga hukuncin kotun ƙoli cikin hikima, sannan ya yi ƙoƙari ya sasanta da ƴanmajalisar, kada ya bari su tunzura shi, shi ma kada ya tunzura su, ya yi ƙoƙarin samun daidaito da su ta fuskantar maslaha, idan ba ka haka ba mulkin yana iya gagararsa cikin daɗi, yana iya gaza aikata abubuwan da yake so."
Shi ma Malam Sufi ya ce gwamnan zai iya samun sauƙi ta hanyar shigo da ƴansiyasar jihar a cikin maganar, "sannan shugaban ƙasa ya ba shi shawara, wanda hakan ke nufin akwai wata ƙofa ta samun maslaha, don haka zai iya komawa wajen shugaban ƙasa ya nemi shawara a kan yadda za a samu daidaito."
Ya ce tunda ana zargin duk abin da ke faruwa ba za a rasa hannun tsohon gwamnan jihar ba, "shi Wike ka ga babu wanda zai iya masa magana sai shugaban ƙasar kasancewar duk manyan siyasar jihar ana ganin sun riga sun samu saɓani da shi domin goya wa Fubara baya."
A game da batun ko sauya sheƙa za ta amfani gwamnan, Farfesa Abdulƙadir ya ce ya danganta da yadda siyasar ta kasance da kuma wataƙila wata tattaunawa da ake yi ta bayan fage.
A nasa ɓangaren, Sufi sauya sheka za ta danganci da irin ƙarfin siyasarsa, "idan yana ƙarfin siyasa a jihar, sai ya koma wata jam'iyyar ya gwada ƙwanjinsa."
Mene ne asalin takun-saƙar?
Rikicin siyasa dai ya ƙi, ya ƙi cinyewa a tsakanin gwamnan jihar Rivers Sim Fubara da tsohon ubangidansa, ministan Abuja Nyesom Wike tun a shekarar 2023, inda suka rigima a kan jan ragamar jihar, lamarin da ya sa siyasar jihar ta ɗauki zafi, har ta zama abar kallo.
Lamarin ya ɗauki sabon salo ne lokacin da za a yi zaɓen ƙananan hukumon jihar, inda ɓangaren Wike suka ce ba za a yi zaɓen ba, shi kuma ɓangaren gwamna Fubara suka ce babu gudu, ba ja da baya sai an yi, inda aka yi zaɓen, jam'iyyar APP wadda ake tunanin gwamna Fubara ya goyawa baya, ta lashe kujera 22 daga cikin ƙananan hukumomin jihar guda 23.
Ana tunanin gwamnan ya tsayar da ƴantakara ne a APP kasancewar tun a lokacin da aka gudanar da zaɓen shugabannin PDP na jihar Rivers an samu ɓaraka, inda tsagin Wike na PDP ya samu a nasara a kan tsagin Fubara.
Haka kuma rikici ya ɓarke a majalisar dokokin jihar, inda mafiya yawan majalisar, su 27 suke tare da da Wike, sauran kuma guda uku suke tare da gwamna.
A lokacin ne ƴanmajalisar na hannun damar Wike suka sanar da komawa APC, inda sauran ukun na gefen Fubara suka sanar da cewa guda 27 sun rasa kujerarsu, lamarin da aka je kotu har aka kotun ƙoli, wadda ta dawo musu da kujerarsu, sannan ta soke zaɓen ƙananan hukumomin jihar.











