Shin rikicin Fubara da Wike zai bari a yi zaɓen ƙananan hukumomi a Rivers?

Asalin hoton, Rivers State Government Press
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
Rikicin siyasa da ya ƙi, ya ƙi cinyewa a tsakanin gwamnan jihar Rivers Sim Fubara da tsohon ubangidansa, ministan Abuja Nyesom Wike ya ɗauki sabon salo a sanadiyar zaɓen ƙananan hukumomin jihar, wanda za a yi gobe Asabar.
Tun a shekarar 2023 ce shugabannin biyu suke takun-saƙa a kan jan ragamar jihar, lamarin da ya sa siyasar jihar ta ɗauki zafi, har ta zama abar kallo da magana a faɗin ƙasar.
Tuni ɓangaren Wike suka ce ba za a yi zaɓen ba, su kuma ɓangaren gwamna Fubara suka ce babu gudu, ba ja da baya sai an yi.
Tun a farko-farkon mulkin Fubara aka fara rikici a game da shugabannin ƙananan hukumomi, inda bayan wa’adin waɗanda Fubara ya gada daga Wike ya ƙare, ya buƙaci su tafi, su kuma suka ce allambaran suna da sauran lokaci, ana cikin wannan ne ya sanar da naɗa shugabannin riƙon ƙwarya domin su maye gurbin waɗancan, lamarin da ya tayar da tashin hankali a jihar.
Tun a lokacin da aka gudanar da zaɓen shugabannin PDP na jihar Rivers ne aka fara hango wannan rikicin na zaɓen ƙananan hukumomi.
A zaɓen, tsagin Wike na PDP ya samu a nasara a kan tsagin Fubara, lamarin da ya haifar da saɓani mai girma tsakanin Wike da ƙungiyar gwamnoni, har Wiken ya yi barazanar kunna wutar siyasa a duk jihar da ta sa baki a jiharsa.
Me ya sa PDP ba ta so a yi zaɓen?
Wani abu da ya ɗauki hankali a game da zaɓen shi ne yadda jam’iyyar PDP mai mulki a jihar ta gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da gudanar da zaɓen.
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Chukwuemeka Aaron ya bayyana a lokacin zanga-zangar cewa gwamna Fubara yana yi wa doka karar tsaye, sannan ya buƙaci ƴansanda da sauran jami’an tsaro su ƙaurace wa zaɓen.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shi ma Tonu Okocha, shugaban riƙon ƙwarya na tsagin APC da suke tare Wike ya ce ba za a yi zaɓe ba saboda kotu ta hana hukumar INEC da jami’an tsaro shiga zaɓen.
A nasa ɓangaren kuma, gwamna Fubara ya ce babu gudu ba ja da baya, inda ya ce ai Kotun Ƙoli ta yi hukuncin cewa dole kowace jiha a Najeriya ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.
A gefe guda, wasu daga cikin ƴan jam’iyyar PDP, ciki har da waɗanda gwamna Fubara ya naɗa shugabannin riƙon ƙwarya a ƙananan hukumomin jihar bayan wa’adin mutanen Wike ya ƙare sun koma jam’iyyar APP.
Komawarsu APP ke da wuya suka samu tikitin takarar shugabancin ƙananan hukumomi a zaɓen wanda za a yi gobe, wanda hakan ya sa ake tunanin wataƙila gwamna Fubara ne ya tura su can, kasancewar PDP ba a hannunsa take ba.
Wannan ne ya sa ita kuma jam'iyyar PDP, waɗanda shugabanninta na jihar ke tare da Wike suka dage kai da fata cewa ba za a yi zaɓen ba.
Sanannen abu ne dai a siyasar Najeriya cewa a lokuta da dama, jam'iyyar da gwamna yake so, ita ce ke yin cinye-du a zaɓen ƙananan hukumomi.

Asalin hoton, Bariuku Felix/Facebook
Hukunce-hukuncen kotuna daban-daban
A ranar 6 ga Satumba, Mai shari’a I.P.C Igwe na babbar kotun jihar Rivers ya ba hukumar RSIEC umarnin ta gudanar da zaɓen, sannan ya buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki a zaɓen su bayar da goyon baya domin tabbatar da zaɓen ya tafi da kyau.
Sai dai a wani hukunci daban da mai shari’a Peter Lifu na babbar kotun tarayya ya yanke a ranar Litinin da ta gabata wato 30 ga Satumba ya buƙaci Sufeto Janar na ƴansanda da hukumar tsaron SSS da su umarci jami'ansu su ƙaurace wa zaɓen bayan lauyoyin APC, ƙarƙashin Joseph Daudu SAN sun buƙaci hakan.
A ɓangaren INEC, babban kwamishinan INEC a jihar Rivers, Johnson Alalibo ya ce sun samu oda daga babbar kotun tarayya da ke Abuja da ke hana su bayar da rajistar masu kaɗa zaɓe.
Ya ce RSIEC ta aiko da buƙatar a ba su rajistar, amma kafin su miƙa mata ne kotun tarayyar ta yanke hukunci.
Mun shirya gudanar da zaɓe – Hukumar RSIEC
A nata ɓangaren, hukumar zaɓen jihar Rivers mai zaman kanta RSIEC ta ce a shirye take ta gudanar da zaɓen na gobe, inda ta ce za ta gudanar da zaɓen kamar yadda dokokinta suka tanada.
Shugaban RSIEC Adolphus Enebeli ya ce suna la’akari ne da hukuncin Kotun Ƙoli, wanda ya ce dole a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a a dukkan jihohin Najeriya, sannan ya ƙaryata batun cewa ba su fitar da rajistar masu kaɗa ƙuri’a ba.
Shin zaɓen zai yiwu kuwa?
Tuni dai rundunar ƴansandan jihar Rivers ta fitar da sanarwar cewa ba za ta bayar da tsaro ba a zaɓen na gobe Asabar.
A wata sanarwa da kakakin rundunar SP Grace Iringe-Koko ta fitar, ta ce rundunar ta samu hukunci daga kotu, wanda ya hana ƴansandan bayar da tsaron.
Wannan ya sa ake fargabar ko zaɓen zai iya yiwuwa, lamarin da masanin siyasa a Najeriya, Farfesa Kamilu Sani Fage na jami'ar Bayero da ke Kano ya kwatanta da kamar mace mai ciki.
A cewarsa, "Wannan abun da yake faruwa a Rivers a siysance yana da hatsari saboda shi tsohon gwamna yana neman ya mayar da jihar kamar yankinsa ne, sai yadda yake za a yi. Shi ya sa zaɓen ya ja hankalin Najeriya saboda cike yake da rigingimu tsakanin sabon gwamna da tsohon gwamna. Wannan ya sa shi sabon gwamna ya umarci mutanensa su koma wata jam'iyya su tsaya takara saboda shi tsohon gwamna ya riƙe PDP a hannunsa."
Farfesa Fage ya ce za a iya yin zaɓen, amma ko da an yi, za a cigaba da fuskantar matsaloli har zuwa kotunan gaba.
"Amma da tsari ake bi, to da umarnin kotun da ta fara hukunci za a bi, tunda darajarsu ɗaya ne, sai a cigaba da gudanar da zaɓen. Amma hukuncin wata kotun daga baya sai ya kawo tsaiko musamman ganin shi Wike yana da ƙarfi a sama."
Farfesan ya ƙara da cewa ƴansanda za su iya hana zaɓen baki ɗaya saboda hukuncin kotun da suka ce ya iso gare su.
"Matsalar ita ce ƴan siyasarmu suna fakewa ne a bayan shari’a suna mata fassarar da suke so. Shi sa wannan zaɓen na gobe babu wanda zai iya cewa za a yi ko ba za a yi ba, sai an ga yadda ta kaya domin kowane ɓangare ya smu goyon bayan shari’a."










