Dalilin da ya sa gwamnoni ke ɓatawa da iyayen gidansu

- Marubuci, Daga Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
Ɗaya daga cikin abin da ya fi shahara a siyasar Najeriya shi ne yaro ya gaji ubangidansa na siyasa a matsayin gwamna. Wani abu da kuma ke biyo bayan haka shi ne yaro ya ɓata da ubangidan nasa.
Irin haka ta daɗe tana faruwa a jihohi masu yawa, yayin da siyasar ubangida ke ci gaba da mamaye tunanin ƴan siyasar Najeriya tun daga sama har ƙasa a ƙasar da ta zarta kowacce yawan al'umma a nahiyar Afirka.
Abin da ke faruwa yanzu haka a jihar Rivers da ke kudancin ƙasar ya isa misali, inda tsohon Gwamna Nyesom Wike ke fafata rikici da gwamna mai-ci Siminalayi Fubara.
Masu sharhi kan ce tasirin siyasar ubandiga na da girma a siyasar Najeriya ta yadda babu abin da zai iya sauya ta sai dai masu jefa ƙuri'a da kansu.
Daga cikin jihohin da siyasarsu ta shahara da irin wannan balahira akwai Sokoto, da Zamfara, da Katsina, da Legas, da Kano.
Yayin da duk wannan ke faruwa, ko mene ne talakawa - waɗanda su ne ƙashin bayan dimokuraɗiyyar - amfana da rikici tsakanin shugabanni da iyayen gidansu? Mene ne ke jawo rikicin tun da farko?
Girman kujerar gwamna
Bisa tsarin siyasar Najeriya, gwamna ne mutum mafi ƙarfin iko a jiharsa - ban da ƴan wasu lokuta da dokar ta bai wa shugaban ƙasa damar ɗaukar mataki bisa wasu dalilai.
Irin wannan ƙarfin iko da kujerar gwamna ke da shi, shi ne dalili mafi girma da ke jawo rikici tsakanin tsofaffin gwamnoni da yaransu a siyasa, in ji masaninin kimiyyar siyasa, Kabiru Sufi.
"Duk wanda ya hau mulki kuma ya ji ƙarfin ikon da kujerar [gwamna] ke da shi, sannan da yawan mutanen da za su koma su kewaye shi, sai ya ji cewa shi fa yanzu ba yaron wani ba ne," a cewar malamin da ke koyar da kimiyyar siyasa a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano.
"Sannan za ta saka mutum ya ji cewa da ma ƙila ubangidan nasa kujerar da ya riƙe ce ta sa ya ji shi wani ne, saboda haka shi ma yanzu ya kawo ƙarfi."
Sauka daga kan manufa
Ita ma Suwaiba Muhammad Dankabo ta jaddada irin ƙarfin ikon kujerar gwamna a matsayin babban abu da ke lalata alaƙa tsakanin abokan aiki.
Sai dai ta nuna cewa wani zubin sauka daga kan wata manufa da tsohon gwamna yake kai tun da farko kan haddasa rikicin.
"Idan gwamna mai-ci ya yi yunƙurin sauka daga kan wani tsari ko kuma ya lura da wani abu da bai fahimta ba, to za a samu matsala," a cewar mai sharhin kuma mataimakiyar shugaban ƙungiyar Action Aid a Najeriya - mai rajin inganta hakkin ɗan'adam da yaƙi da talauci.
Sai dai Malam Sufi na ganin duk da cewa wannan na cikin dalilai amma ya zama makunnar rikicin, ba wai ainahin dalilin faruwar sa ba.
__________________________________________________
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A kwanan nan majalisar jihar Kaduna ta ƙaddamar da bincike kan gwamnatin tsohon Gwamna Nasir EL-Rufai, tana mai cewa saboda an ciyo basuka masu yawa amma ba a aiwatar da ayyuka yadda ya kamata ba.
Lokaci na ƙarshe da majalisar ta yi muharawara kan lamarin ta nemi a kawo mata bayanan asusun ajiya na abubuwan da gwamnatin El-Rufai ta yi da kuɗin da ta ranto.
Idan ba a manta ba, Nasir El-Rufai ne ya yi uwa ya yi makarɓiya wajen tabbatar da Gwamna Uba Sani mai-ci ya yi nasarar zama sanata daga Kaduna ta tsakiya saboda rikicin siyasarsu da Shehu Sani, sanata mai riƙe da kujerar a lokacin, sannan kuma ya taimaka masa wajen ganin ya gaje shi a matsayin gwamna a zaɓen 2023.
A jihar Rivers kuma, Gwamna Siminalayi Fubara ne ke ƙoƙarin faɗaɗa ikonsa a rikici da tsohon ubangidansa Nyesom Wike.
Rikcin nasu ya kai ga tarwatsa kan majalisar dokokin jihar tsakanin magoya bayansu. inda har aka samu kakakin majalisa biyu kafin daga baya a sasanta.
Bugu da ƙari, irin wannan yanayin aka shiga lokacin da Wike ya gaji Rotimi Amaechi a matsayin gwamnan Rivers, inda Wiken ya koma PDP daga APC mai mulkin Najeriya.
A jihar Edo kuma alaƙa ta yi matuƙar lalacewa tsakanin Gwamna Godwin Obaseki da mataimakinsa Philip Shaibu, wanda ya sa jawo tsige mataimakin a watan Afrilun da ya gabata.
Rikice-rikicen yaro da ubangida daga 1999:
- Aliyu Magatakarda Wamakko da Aminu Waziri Tambuwal - jihar Sokoto
- Rochas Okorocha da Hope Uzodimma - jihar Imo
- Mamuda Shinkafi da Ahmad Sani Yarima - jihar Zamfara
- Rabiu Musa Kwankwaso da Umar Ganduje - jihar Kano
- Nasiru El-Rufai da Uba Sani - jihar Kaduna
- Bola Tinubu da Akinwunmi Ambode - jihar Legas
- Rotimi Amaechi da Nyesom Wike - jihar Rivers
- Nyesom Wike da Siminalayi Fubara - jihar Rivers
- Danjuma Goje da Ibrahim Hassan Dankwambo - jihar Gombe
- Inuwa Yahaya da Danjuma Goje - jihar Gombe
Gaba kura baya sayaki...
Shakka babu, mutane da dama na ganin irin wannan rikici a matsayin koma-baya ga dimokuraɗiyya.
Sai dai kuma masana na cewa ba haka abin yake ba.
"Ba za a ce hakan yana taimakon dimokuraɗiyya ba, amma dai yana cikin hanyoyin da ake bi wajen ƙara gyara tsarin," in ji Kabiru Sufi.
"Dole ne a ci gaba da ganin irin waɗannan matsalolin ana gyara su. Misali, matsalolin da aka fuskanta a farkon 1999 ba su ake fama da su ba a yanzu. Wannan ta sa ma za ka ji wasu na cewa za mu tabbatar matsalolin da muka shiga ba za mu sake shigarsu ba."
A wani hannun kuma, ko mene ne tasirin irin wannan rikici a kan masu zaɓe? Da yake amsa wannan tambaya, Sufi ya ce lamarin fa gaba kura ne baya kuma sayaki.
"Kullum dai su ne a ƙasa, su za a ci gaba da cuta. Misali, idan ana yin rikicin sai hankali ya sauka daga kan harkokin jagoranci da mulki."
Ganin cewa siyasar ubangida ta samu gindin zama sosai a Najeriya, akwai yiwuwar a samu ƙarin gwamnonin da za su ɓata da iyayen gidansu kafin zaɓen 2027.










