Ko Jonathan zai iya sasanta rikicin Wike da Fubara?

Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Goodluck Jonathan ya mulki Najeriya tsakanin 2010 zuwa 2015 a jam'iyyar PDP mai adawa a yanzu kuma mai mulkin jihar Ribas

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya fara wani yunƙuri na sasanta rikicin siyasar da ke ƙara kamari tsakanin Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara da mai gidansa Ministan Abuja Nyesome Wike yayin ƙaddamar da wani aiki da Jonathan ya je yi a jihar.

Rikicin dai ya yi ƙamari a baya-baya nan har ta kai ga ya janyo wa wasu kwamishinonin gwamnatin Fubara sauka daga muƙamansu.

Ɗan lokaci bayan rantsar da Gwamnan Fubara ne suka soma samun tsamin dangantaka tsakaninsa da Wike, abin da ya kai har wasu daga cikin ƴan majalisar dokokin jihar da ake zargin na goyon bayan ɓangaren Wike suka ɗauki matakin tsige gwamnan - kodayake ba su yi nasara ba.

Jonathan ya ce dole ne jagororin biyu su ajiye bambance-bambacen da ke tsakaninsu saboda su yi aiki tare domin ciyar da jihar gaba.

Muna maraba da yunƙurin - PDP

....

Asalin hoton, RIVERS STATE GOVERNMENT PRESS

Ibrahim Abdullahi, muƙaddashin mai magana da yawun jam'iyyar PDP a Najeriya ya shaida wa BBC cewa jam'iyyar na farin ciki da wannan yunƙuri na tsohon shugaban ƙasar na sasanta rikicin siyasa tsakanin Fubara da Wike.

Abdullahi ya ce Najeriya na cikin wani hali da bai kamata shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi sulhu a jam'iyyar da ba tasa ba.

"Ai bai yiwuwa a ce mutum ya yi ƙoƙarin sulhu a jam'iyyar da ba tasa ba, kamar abin da Tinubu ya yi ƙoƙarin yi." in ji shi.

"Yunƙurin Jonathan na sassanta rikici tsakanin Fubara da Wike zai yi tasiri idan har shi minista Wike akwai gaskiya a manufarsa."

Ko Jonathan zai iya sasanta rikicin?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dr Kole Shettima, masanin kimiyyar siyasa ne a Najeriya kuma ya shaida wa BBC cewa matakin da Jonathan ya ɗauka na sasanta Fubara da Wike na da alfanu.

Sai dai ya ce duk da amfanin hakan ba laile ne ya iya sasantasu ba.

"Na yi maraba da matakin da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ɗauka na shiga maganar rikicin Wike da Fubara. Ko a wanne lokaci, ya kamata idan irin waɗannan abubuwan suka taso a samu dattawa da za su iya shiga tsakani, wataƙila a samu masalaha," in ji Shettima.

"Da yake Jonathan ɗan yankinsu ne kuma ya yi aiki tare da su, wataƙila ya samu nasara wajen sasanta su."

Masanin kimiyyar siyasar ya ce zai yi wuya a cimma wannan masalahar da ake so saboda alaƙar tsakanin Fubara da Wike ta yi matuƙar lalacewa.

"Maganganun da ke fita daga bakin ɓangarorin biyu ba maganganu ne na dattawa ba shicyacsa nake ganin cewa zai yi wuya a samu masalaha." a cewarsa.

"Saboda waɗansu da suka bar gwamnati, wataƙila za su so su ga cewa su ne har yanzu ke ba da umarni a kan abubuwa."

Yunƙurin tsohon shugaban ƙasar ya zo ne bayan yunƙurin da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taba yi a baya na sasanta su, duk da cewa ba ɗan jam'iyyarsu.

A baya dai, Gwamna Fubara ya ɗauki matakin korar ƴan majalisar dokokin jihar 25 bayan da 'yan majalisa masu goyon bayansa suka ayyana kujerunsu a matsayin babu kowa a kai.