Me ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers ke nufi?

…

Asalin hoton, FB/Siminalayi Fubara

Lokacin karatu: Minti 1

A ranar Talata ne rikicin siyasa da ake fama da shi a jihar Rivers - wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa - ya kai magaryar tuƙewa, bayan da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar.

Wannan ya biyo bayan duk wasu matakan da aka ɗauka a baya domin sasanta rikicin, kamar yadda shugaban na Najeriya ya bayyana.

Siyasar jihar ta Rivers ta damalmale ne tun bayan da rashin jituwa ya ɓulla tsakanin gwamnan jihar Siminalayi Fubara da magabacinsa, ministan birnin tarayyar Najeriya, Nyesom Wike.

Lamarin ya kai ga cewa ƴan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike sun yi barazanar tsige gwamna Fubara.

Sai dai al'amarin ya ƙara dagulewa bayan da rikicin ya kai ga rushe ginin majalisar dokokin jihar, wanda har a halin yanzu yake a rushe.

Lamarin ya kai ga cewa ƴanmajalisar na ɓangaren Wike sun bayyana ficewarsu daga jam'iyyar PDP zuwa APC, sai dai daga baya sun janye batun nasu, kuma an riƙa tafka shari'a har zuwa kotun ƙoli.

Ko me ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers ke nufi?

Tuni masana fannin kimiyyar siayasa da masu sharhi kan al'amura suka fara tofa albarkacin baki. Farfesa Abubakar Umar Kari na jami'ar Abuja ya shaidawa BBC cewa matakin ya zo da bazata

''Abin ya zo da bazata a haka, kuma abu ne mai daure kai, tun da ina ganin babban abinda ya sa aka dauki wannan mataki shi ne a nemi maslaha. To amma akwai shakku ko masalahan za ta samu''

''Saboda maganar gaskiya wannan jawabi na Tinubu, idan aka karanc shi aka yi la'akari sai a ga ya yi ta ba wa dakataccen gwamna Similayi Fubara laifi a wurare da dama'' in ji shi.

Masanin ya ce akwai bangarori uku a wannan rigima da suka hada da sashin gwamna da majalisa da kuma Ministan babban birnin taraya Abuja kuma tsohon gwamnan jihar ta Ribas, Nyesom Wike kuna kamata ya yi a ce matakin ya shafi dukkanin bangarorin da ke wannan rigima.