Laifukan da ƴanmajalisar dokokin Rivers ke zargin Gwamna Fubara da aikatawa

Ƴan majalisar dokokin jihar Rivers na zargin Fubara da tafka laifuka a ayyukansa

Asalin hoton, X/@SimFubara

Bayanan hoto, Ƴan majalisar dokokin jihar Rivers na zargin Fubara da tafka laifuka a ayyukansa
Lokacin karatu: Minti 3

An shiga wani sabon mataki a rikicin siyasa da ya turnuƙe a jihar Rivers, bayan da ƴan majalisar dokokin jihar suka zargi gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Odu da saɓa wa ƙa'idar aiki.

Ƴan majalisa 26 na jihar ta Rivers sun yi waɗannan zarge-zarge ne a wasu takardun koke biyu da suka tura wa shugaban majalisar, Martin Amaewhue.

Sun ce sun ɗauki matakin nasu ne "bisa dogaro da sashe na 188 na kudnin tsarin mulkin Najeriya na 1999", wanda ya tanadi cewa dole ne a samu kashi ɗaya cikin uku na ƴan majalisa su goyi bayan koken sannan kuma a tantance ainahin laifukan.

Takardun koken biyu waɗanda suka samu sa hannun ƴan majalisa 26, an gabatar da su ne ga shugaban majalisar a zaman da ta yi ranar Ltinin, bisa dogaro da sashe na 188 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Shugaban majalisar zai tabbatar an isar da takardar ga wanda ake ƙorafi a kansa, da kuma ga dukkanin ƴan majalisar jihar, cikin kwana bakwai da karɓar ta.

Ya zuwa yanzu dai gwamna Siminalayi Fubara bai ce komai ba kan lamarin.

Martin Amaewhule and Governor Fubara

Kashe kuɗi ba bisa ƙa'ida ba da sauran zarge-zargen da ake yi wa Fubara

Letter of Gross Misconduct Rivers Assembly members send to Governor Fubara
Bayanan hoto, Wasiƙar da ƴan majalisar dokokin jihar Rivers suka aika wa gwamnan jihar Siminalayi Fubara

Takardar ƙorafin ta bayar da lokuta biyar takaimai da ake zargin gwamnan da mataimakiyarsa da da aikata laifi.

Cikin abubuwan da ƴan majalisar suka zargi Fubara da aikatawa sun haɗa da:

  • Kashe kuɗin gwamnati babu tsari kuma ba bisa ƙa'ida ba
  • Kawo cikas ga ayyukan majalisar dokokin jihar, wadda wani ɓangare ne gwamnati
  • Naɗa mutane kan muƙaman gwamnati ba tare da an tantance su kamar yadda doka ta tanada ba
  • Riƙe albashi da alawus-alawus ɗin ƴan majalisar dokokin jihar Rivers
  • Riƙe albashin magatakardan majalisar dokokin jihar Rivers, Emeka Amad

Zarge-zargen da ake yi wa mataimakiyar gwamna, Ngozi Odu

Zarge-zargen da majalisar dokokin jihar ta Rivers ke yi wa mataimakiyar gwamnan jihar Rivers, Farfesa Ngozi Odu su ne:

  • Zargin mataimakiyar gwamna, Ngozi Odu da "haɗa baki da kuma goyon bayan naɗa mutane muƙaman gwamnati ba bisa ƙa'ida ba

Ƴan majalisa na jiran amsa daga Fubara

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan samun takardar ƙorafin, shugaban majalisar dokokin jihar ta Rivers ya mmiƙa ta ga ofishin gwamnan jihar, tare da bayyana cewa sama da kashi ɗaya cikin uku na ƴan majalisar ne suka amince da ƙorafin.

Shugaban majalisar ya buƙaci gwamna Fubara da ya amsa waɗannan tuhume-tuhume da aka yi masa na aikata laifukan da suka saɓa wa doka.

"Ina janyo hankalinka ga sashe na 188(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, wanda ya tanadi cewa:

"A cikin kwana 14 bayan gabatar da wannan bayani ga shugaban majalisar dokoki (ko da kuwa babu martani daga ofishin da ake tuhuma a wannan takarda) Majalisar Dokoki za ta yanke hukunci kan za ta ci gaba da yin bincike game da waɗannan zarge-zarge." In ji takardar da shugaban majalisar ya tura wa Gwamna Fubara.

Babu tabbas kan irin martanin da Gwamna Fubara da mataimakiyarsa za su yi kan zarge-zargen, balle kuma hanyar da za su bi wajen rage zaman tankiyar da ke tsakaninsu da ɓangaren majalisar dokokin jihar.

Haka nan kuma majalisar dokokin jihar ta yanke shawarar gayyatar hukumar yaƙi da rashawa ta Najeriya (EFCC) domin ta gudanar da bincike kan sakataren gwamnatin jihar, Tammy Danagogo bisa zargin wadaƙa da kuɗin gwamnati.