Real Madrid da Liverpool za su yi musayar Rodrygo da Szoboszlai, Man U na son dawo da McTominay

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na tunanin sake sayen dan wasan tsakiya na Scotland Scott McTominay kan Yuro miliyan 80 (£70m) a lokacin bazara, inda Napoli ke shirin karbar kudin dan wasan mai shekaru 29 shekaru biyu kacal bayan ya koma kungiyar ta Italiya daga Old Trafford. (Fichajes)
Real Madrid na sa ido sosai kan dan wasan tsakiya na Tottenham Micky van de Ven mai shekaru 24, yayin da ake ganin babu alamar cewa dan wasan Netherlands zai rabata hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da kungiyar ta Premier League. (Teamtalk)
Brighton na fatan kammala yarjejeniyar sayen dan wasan gefe na Cologne mai shekaru 19 Said El Mala ta hanyar sayen dan uwansa, dan wasan gaba mai shekaru 20 Malek. (Times)
Manchester United na duba yiwuwar daukar ɗan wasan tsakiya na Ivory Coast na Nottingham Forest, Ibrahim Sangare, mai shekaru 28, a ƙoƙarinta na neman wanda zai maye gurbin ɗan wasan Brazil, Casemiro, mai shekaru 34. (GiveMeSport)
Casemiro zai sami damar komawa Amurka lokacin da kwantaraginsa a Manchester United zai kare, inda ɗan wasan tsakiyar zai iya komawa wata babbar kungiya a kasar ta Amurka (Telegraph)
Liverpool na iya duba bukatar yin musaya da Real Madrid, da za ta kai ta ga daukar ɗan wasan gefen Brazil, Rodrygo, mai shekaru 25, yayin da ita kuma za ta ba wa Madrid din ɗan wasan tsakiya na Hungary, Dominik Szoboszlai, mai shekaru 25. (Fichajes)
Kocin Chelsea, Liam Rosenior, ba ya son barin ɗan wasan gaba na Ingila mai shekara 23, Liam Delap ya tafi a wannan bazarar, a dai-dai lokacin da Everton ke sha'awarsa. (Football Insider)
Crystal Palace za ta ba wa kocin Austrian Oliver Glasner damar ci gaba da jagorantar ƙungiyar har zuwa ƙarshen kakar wasa. (Football Insider)
Aston Villa, da Crystal Palace da Wolves suna cikin kungiyoyin da ke sha'awar sayen dan wasan baya na hagu na Scotland Andy Robertson, idan dan wasan mai shekaru 31 ya bar Liverpool a wannan bazarar. (Cough Offside)
Nottingham Forest na iya karɓar tayi daga kungiyoyi kan dan wasan gaban Brazil Igor Jesus, mai shekaru 24, a ƙarshen kakar wasa. (Football Insider)











