Mece ce dokar ta-ɓaci kuma me kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce a kan ta?

Bola Tinubu da Siminalayi Fubara
Bayanan hoto, Bola Tinubu da Siminalayi Fubara
Lokacin karatu: Minti 3

A baya-bayan nan ne Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers da rikicin siyasa ya yi wa katutu tsawon lokaci.

Matakin na shugaba Tinubu dai ya yamutsa hazo a faɗin Najeriya lamarin da ya sa mutane da dama bayyana mabambantan ra'ayoyi a shafukan sada zumunta.

Yayin da wasu kuma ke neman sanin manufar dokar ta-ɓaci da kuma abin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce game da ayyana irin wannan doka da ma hurumin da shugaban ƙasa yake da shi na ɗaukar irin wannan mataki.

Hakan ya sa muka tuntuɓi Barista Abba Hikima, wani lauya mai zaman kansa a Kano wanda kuma ya yi mana taza da tsifa kan haka.

Ma'anar dokar ta-ɓaci

A cewar Barista Abba Hikima, dokar ta-ɓaci wani yanayi ne da tsarin mulkin Najeriya ya tanada wanda kuma yake bai wa gwamnatin ƙasar damar a ayyana shi a ƙasa baki ɗaya ko a ayyana shi a wani ɓangare na ƙasar kamar ilimi ko tsaro ko tattalin arziki.

Ya ce ana ɗaukan irin wannan mataki ne idan aka tsinci kai cikin "yanayin yaƙi ko akwai tsoron za a kawo wa Najeriya yaƙi ko akwai afkuwar bala'i kamar ɓallewar ruwa ko faɗawa cikin ruɗani babu bin doka da oda ko wata cuta da ke buƙatar a ɗauki irin wannan mataki."

Barista Abba Hikima ya ƙara da cewa bayan ayyana dokar, matakin na bai wa gwamnati dama ta ɗauki wasu matakai na kawo sauƙi ga abin da ke faruwa kasancewar "akwai tsarin ƴancin cin gashin kai na jihohi da gwamnatin tarayya."

"Idan aka ayyana dokar ta-ɓaci, hakan na bayar da dama ga gwamnatin tarayya ta ɗauki wani mataki wanda zai ɗauke wasu daga cikin ikon da jihohi suka da shi saboda ana ganin sun gaza." in ji lauyan.

Ko Tinubu ya saɓa wa doka?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Barista Abba Hikima ya bayyana cewa madogarar Shugaba Tinubu na ɗaukan matakin ƙaƙaba dokar ta-ɓaci a jihar Rivers wato sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya bai yi maganar zaɓaɓɓen gwamna da zaɓaɓɓun ƴanmajalisa a ce gaba ɗaya a jingine su a kuma ɗauko tsohon soja a saka a matsayin wanda zai tafiyar da al'amuran jihar Rivers.

Lauyan ya bayyana cewa matakin ya saɓa da dokoki da dama da hukunce-hukuncen kotu da aka yi kafin yanzu sannan kuma ya ci karo da tsarin tafiyar da ƙasa a ƙarƙashin dimokraɗiyya.

Ya kuma ce matakin ba sabon abu ba ne a Najeriya kasancewar a baya ma an samu tsoohon shugaban ƙasar, Olusegun Obasanjo da ya ayyana irin wannan doka kuma "an je kotu kuma an tabbatar da abin da Obasanjo ya yi ya saɓa wa doka - idan ka saka dokar ta-ɓaci, hakan ba ya bai wa shugaban ƙasa damar ya dakatar da zaɓaɓɓun shugabanni."

Barista Abba Hikima ya ce sashen da ya yi magana game da dokar ta-ɓaci ya faɗi cewa "idan an ayyana wannan doka, majalisar dokokin Najeriya tana da kwana biyu -musamman idan ba a lokacin hutu suke ba, idan kuma suna hutu suna da kwana 10 - su koma zama su yi nazari kan dokar ta-ɓacin sannan su tafka muhawara a kai, kuma sai an samu kashi biyu bisa uku na amincewar ƴanmajalisar sannan za a iya cewa wannan doka ta kafu kuma ta fara aiki.

Abin da ya dace

A ganin Barista Abba Hikima, ya kamata a ce an bai wa ƴanmajalisar jihar dama - idan za su tsige gwamnan su tsige shi idan suna ganin ya yi abubuwan da bai kamata.

Ya ce babu wata hanya da ake bi a dakatar da ƴanmajalisa idan ba kiranye za a yi masu ba bisa tanadin sashe na 110 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Sai dai ya ce matakin na Tinubu bai tsaya iya gwamna da mataimakinsa ba, har da ƴanmajalisa masu tsara doka.