Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers

Asalin hoton, X/Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers bayan rikita-rikitar siyasa da jihar ta daɗe tana fama da shi tare da kuma da naɗa wanda zai riƙe muƙamin gwamnan jihar na tsawon wata shida.
Tinubu ya sanar da matakin ne a wani jawabi da ya yi ta kafafen talabijin na ƙasar da yammacin ranar Talata.
A cikin jawabin nasa, Tinubu ya yi nuni da yadda aka rushe ginin majalisar dokokin jihar watanni 18 da suka gabata, wadda aka kasa sake gina ta har zuwa wannan lokaci.
"Jihar ta tsaya cik tun bayan ɓarkewar rikicin siyasar inda aka tauye wa al'ummar jihar hakkinsu na cin moriyar mulkin dimokuraɗiyya.
''Na yi iyakar bakin kokarina wajen ganin yadda za a magance matsalar to amma duka ɓangarorin sun yi watsi da yunkurin.''
Tinubu ya bayyana cewa babu wani shugaban ƙasa nagari da zai zura ido yana kallon abin da ke faruwa ba tare da bin matakan da kundin tsarin mulki ya tanada ba wajen ganin an shawo kan matsalar ta jihar Rivers.
A cikin jawabin da ya gabatar ta kafafen talabijin na ƙasar, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce: ''Bayan nazari kan halin da ake ciki a jihar Rivers, ya zama wajibi na yi amfani da sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.
"A kan haka, na ayyana dokar ta-ɓaci daga yau 18 ga watan Maris, 2025."
"Da wannan bayani, gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Mrs Ngozi Odu da kuma dukkanin zaɓaɓbun ƴanmajalisar dokokin jihar Rivers, an dakatar da su na wata shida, a matakin farko."
Gwamnan jihar Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar sun kasa samun fahimtar juna kusan tun bayan hawansa kan mulki, duk kuwa da hukunce-hukunce da kotu ta zartar.
Haka nan shugaban ƙasar ya bayyana cewa wasu mutane daga ɓangarori daban-daban su ma sun yi nasu kokarin amma an kasa samun mafita.
''A yanzu ta tabbata babu wata sahihiyar gwamnati a jihar Rivers.'' in ji shugaba Tinubu.
Wane ne zai jagoranci jihar?
A cikin jawabin da ya gabatar, shugaban na Najeriya Bola Tinubu ya bayyana sunan Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas, mai ritaya a matsayin wanda zai jagorancin al'amuran jihar tsawon lokacin da dokar za ta yi aiki.
"A halin yanzu, na naɗa Vice Admiran Ibokette Ibas a matsayin wanda zai gudanar da lamurran jihar, domin amfanin al'ummar jihar," in ji Tinubu.
Sai dai a cikin jawabin nasa, Tinubu ya bayyana cewa wannan doka da ya ƙaƙaba ba ta shafi ɓangaren shari'a na jihar ba.
Tinubu ya ce a tsawon lokacin da Ibas zai jagoranci jihar, ba zai samar da wata doka ba, sai dai zai iya samar da wasu ƙa'idoji waɗanda za su buƙaci amincewar Majalisar Zartarwar Tarayya.











