Me zai faru bayan komawar Fubara kan mulkin jihar Rivers?

Gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara

Asalin hoton, RSGH Media

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara ya koma kan mulki bayan dakatarwa ta wata shida
Lokacin karatu: Minti 6

Wa'adin dokar ta-ɓaci da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ayyana wa jihar Rivers ya cika a ranar Laraba, kuma yau Alhamis 18 ga watan Mayu ne gwamnan jihar ya koma bakin aiki bayan dakatarwa ta tsawon wata shida.

Tun a jiya Laraba ne shugaban na Najeriya Bola Tinubu ya sanar da kawo ƙarshen dokar ta-ɓacin, inda ya ce "daga Alhamis 18 ga watan Satumba, Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Nma Odu, da mambobin majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagoracin kakakin majalisar jihar, Martins Amaewhule, za su koma aikinsu''.

Hakan ya kawo ƙarshen dokar da ta shafe tsawon wata shida a jihar tun bayan da shugaban ya sanar da ita ranar 18 ga watan Maris ɗin 2025.

Tinubu ya ayyana dokar ne sakamakon saɓanin siyasa da aka riƙa samu tsakanin gwamnan jihar Siminalayi Fubara da tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike.

Rikicin ya samo asali ne sakamakon saɓani tsakanin gwamnan Fubara da Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.

Siminalayi Fubara tare da Nyesom Wike

Asalin hoton, Siminalayi Fubara

Bayanan hoto, Ana ganin cewa sulhun da aka yi tsakanin Fubara da Wike zai kawo ƙarshen rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar Rivers

Matsalolin da aka samu a jihar gabanin ayyana dokar ta-ɓaci

  • Yunƙurin tsige Gwamnan Fubara da majalisar dokokin jihar ta yi cikin watan Oktoban 2023, lamarin da ya raba kan ƴan majalisar, inda ƙalilan daga cikinsu ke goyon bayan Fubara, yayin da mafiya rinjayensu ke goyon bayan Wike.
  • Batun ƙona majalisar dokokin jihar da kuma rusa ginin majalisar ga kuma batun ficewar wasu ƴanmajalisar daga PDP zuwa APC, kodayake daga baya sun musanta ficewar.
  • Ga kuma batun shari'o'in kotu daban-daban, ciki har da hukuncin Kotun Ƙolin ƙasar na tabbatar da Martin Amaewhule a matsayin halastaccen kakakin majalisar dokokin jihar, tare da rusa sakamakon zaɓukan ƙananan hukumomin jihar da aka gudanar ƙarƙashin gwamnatin Fubara.
  • Haka ma Ƙotun Ƙolin Ƙasar ta buƙaci gwamnan ya sake gabatar da kasafin kuɗin ƙasar na 2025 a gaban majalisar dokokin jihar ƙarƙashin Amaewhule, to sai dai ba a kai ga saka ranar da za a sake gabatar da kasafin ba, har Shugaba Tinubu ya sanar da dokar-ta-ɓacin.

A lokacin sanar da dokar ta-ɓacin ranar 18 ga watan Maris, Tinubu ya dokar da gwamnan jihar da mataimakinsa da kuma duka mambobin majalisar dokokin jihar.

Abubuwan da suka faru bayan ayyana dokar

  • A Maris: Shugaba Tinubu ya naɗa Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas mai ritaya, a matsayin shugaban gwamnatin jihar tsawon wata shida na lokacin dokar ta-ɓacin. Ya kasance mai jagorantar duka ayyukan hukumomin jihar.
  • A Afrilu: Shugaban gwamnatin jihar ya naɗa kantomomin riƙo a ƙananan hukumomin jihar 23.
  • A Mayun: Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar dokokin ƙasar kasafin kuɗin jihar Rivers domin amincewa da shi.
  • A watan Yunin majalisar dokokin ta amince da kasafin kuɗin jihar na naira tiriliyan 1.485.
  • Haka ma a watan na Yuni, Ministan Abuja Nyesom Wike da Gwamna Fubara suka sasanta tare da alƙawarin yin aiki tare. ''Ba sauran rikici. Zaman lafiya ya dawo a jihar'', kamar yadda ƴansiyar biyu suka bayyana bayan ganawa da Tinubu a ranar 27 ga watan Yunin 2025.
  • A lokacin ganawar, Wike ya ce sun amince su yi aiki tare da gwamnan, hka shi ma Fubara ya amince da matakin.
  • Sun ce dukkansu ƴan mambobin jam'iyya guda ne, wadanda a baya suka samu saɓani, ama a yanzu shun shirya, don haka ne suka je domin shaida wa shugaba Tinubu.
  • Sannan a cikin watan na Yuni aka naɗa wanda ba ɗan jihar ba, Dr. Michael Odey a matsayin shugaban hukumar hukumar zaɓen jihar, lamarin da bai yi wa wasu ƴan jihar daɗi ba.
  • To sai dai duk da haka majalisar dattawan ƙasar ta amince da naɗin Dakta Odey - wanda ɗan asalin jihar Cross River ne - tare da sauran mambobin hukumar bayan rahoton kwamitin da ya sanya ido kan dokar ta-ɓacin, da shugaban kwamitin, Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar.
  • A watan Yuli: Dakta Odey ya fara aiki, inda ya sanar da ranar gudanar a zaɓukan ƙananan hukumomin jihar, da ya ce za a yi ranar 30 ga watan Agusta, aɓanin ranar 9 ga watan na Agusta da tsohon shugaban hukumar Adolphus Enebeli ya sanar tun da farko.
  • A dai watan na Yuli aka rantsar da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin, sannan kuma kantoman riƙo na jihar ya naɗa shugabannin wasu hukumomin jihar, to sai dai hakan ya fuskanci suka daga wasu masu ruwa da tsaki na jihar, da ke ganin cewa wannan hurumin zaɓaɓɓen gwamnan ne.

Na sauke nauyin da Tinubu ya ɗora min - Ibas

Babban kantoman riƙo na jihar, Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas, Mai ritaya, ya ce ya kammala sauke nauyin da Tinubu ya ɗora masa, sakamakon nasarar maido da gwamnatin dimokradiyya a matakin ƙananan hukumomi.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da hukumar zaɓen jihar ta gabatar masa da cikakken rahoton yadda ta gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomin jihar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Vice Admiral Ibas gudanar da zaɓukan cikin lumana da rantsar da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a faɗin ƙananan hukumomi 23 ya nuna cika umarnin da shugaban ƙasa ya bayar ranar 18 ga watan Maris ɗin 2018.

"Shugaba Tinubu ya ɗora min nauyin: Daidata al'amuran jihar, domin samar da kyayyawan yanayin inguwar lamurra, da nufin maido da cikakken tsarin dimokraɗiyya a jihar,'' in ji babban kantoman.

"Bayan da rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli, na yi imanin cewa mun kammala sauke nauyin da aka ɗora mana."

Dangane da batun tilasta dokar ta-ɓacin jihar, kontomar ya ce, ''dokar ta zama dole ne babu makawa sai an ayyanata, to amma ya yaba wa dokar, musamman saboda dawowar zaman lafiya a jihar.

Ya kuma yi kira ga al'ummar jihar su ajiye batun zazzafar hamayyar siyasa tsakaninsu, da son kai su rungumi zaman lafiya da haɗin kai domin ciyar da jihar gaba.

Yayin da gwamnan da ƴanmajalisar dokokin za su koma bakin aiki, wasu mutane na kiran a bincike kantoman riƙon jihar, to amma wasu na kira ga gwamnan ya mayar da hankali wajen gudanar da gwamnati don ciyar da jihar gaba.

Me zai faru bayan komawar gwamna Fubara?

Al'umma na sa ran ganin sauyawar al'amura sosai yayin da Fubara da majalisar dokokin jihar za su koma aiki domin dorawa daga inda aka tsaya.

Wasu bangarorin, kamar Cibiyar kare hakkin bil'adama da tabbatar da adalci, wato Human Rights and Accountability Network na son gwamna Fubara ya kafa wani kwamiti wanda zai binciki yadda aka kashe kudaden gwamnatin jihar a tsawon watanni shida da aka dakatar da shi, lokacin da jihar ke karkashin jagorancin Vice Admiral Ibokette Ibas, mai murabus.

Shugaban cibiyar, Otueking Franklyn Isong na ganin cewa matakin da shugaban kasa ya dauka na ayyana dokar ta baci a jihar ya saba wa doka, domin a cewarsa sashe na 35 na kundin tsarin mulkin Najeriya bai bai wa shugaban kasa ikon dakatar da gwamnan jiha da kuma 'yan majalisar dokokin jiha ba.

Ya kara da cewa matakin da Tinubu ya dauka na dakatar da gwamnan tsawon wata shida na nufin za a kara wata shida a kan wa'adin mulkinsa, kuma ya bukaci kotun kolin Najeriya ta tabbatar da haka domin hana ci gaba da irin wadannan abubuwa.

Wani mai sharhi kan siyasa a Najeriya Olalekan Ige ya shaida wa BBC cewa abin da ya kamaci Fubara shi ne ya kama aiki kan jiki kan karfi saboda babu sauran lokaci mai tsawo da ya rage masa.

Ya ce akwai ayyuka da yawa da suka kamata gwamnan ya aiwatar musamman batun karasa ayyukan gwamnatin jihar da aka dakatar sanadiyyar dokar ta baci da aka kafa da kuma kawo sabbin ayyukan ci gaban jihar.

Ige ya ce yanzu 'yan watanni suka rage kafin shekarar 2025 ta kare, sannan 2026 za ta kasance shekarar da hankula za su koma kan zaben 2027.

A cewarsa gwamnan bai da wani lokaci da zai tsaya yin bincike-binciken abubuwan da suka faru, babban abin da ya fi kamata ya mayar da hankali a kai shi ne kawo manufofi da ayyukan da za su bunkasa rayuwar al'ummar jihar Rivers.

Shi kuwa tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya O.C.J Okocha cewa ya yi "abin da zan fada wa duk wanda wannan lamarinya shafa, musamman gwamna Fubara da kuma shugaban majalisar dokokin jihar Rivers, Martin Amaewhule shi ne su kalli abin da ya faru a matsayin wata matashiya. Ya kamata su koma aiki da niyyar yin jagoranci na gari. Zan kuma shawarce su, su zauna su yi karatun ta-natsu, su sani cewa ya kamata bangarorin gwamnati su taimaka wa juna ne, ba su rika fada da juna ba."