Me tsarin mulki ya ce kan tsige gwamna a Najeriya?

Asalin hoton, Martin Amaewhule/ Sir Siminalayi Fubara/ Facebook
Tun bayan zaman tankiyar da ya ɓarke a jihar Rivers, wanda ya kai ga cewa shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ƙaƙaba dokar ta-ɓaci yan Najeriya ke ta neman sanin tanade-tanaden kundin tsarin mulkin ƙasar dangane da hanyoyi da kuma laifukan da ke janyo a tsige gwamna mai ci.
Kafin ƙaƙaba dokar, ƴanmajalisar sun fara bin matakin farko na ƙoƙarin tsige gwamnan, ta hanyar aika masa da takarda ƙunshe da jerin laifukan da suke tuhumarsa da aikatawa.
Ƴan majalisa 26 na jihar ta Rivers, wadanda yanzu haka an riga an dakatar da su sun yi waɗannan zarge-zarge ne a wasu takardun koke biyu da suka tura wa shugabansu, Martin Amaewhue.
Sun ce sun ɗauki matakin nasu ne "bisa dogaro da sashe na 188 na kudnin tsarin mulkin Najeriya na 1999", wanda ya tanadi cewa dole ne a samu kashi ɗaya cikin uku na ƴan majalisa su goyi bayan koken sannan kuma a tantance ainahin laifukan.
Takardun koken biyu waɗanda suka samu sa hannun ƴan majalisa 26, an gabatar da su ne ga shugaban majalisar a zaman da ta yi ranar Litinin, bisa dogaro da sashe na 188 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.
Yanzu abin tambaya shi ne shin me tsarin mulkin Najeriya ya ce kan tsige gwamna sannan waɗanne laifuka ne gwamnan zai aikata ya cancanci tsigewa?
Abin da tsarin mulkin Najeriya ya ce kan tsige gwamnan
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi bayanin yadda ake aiwatar da tsige gwamna a ƙasar daga mataki zuwa mataki, kamar yadda Barista Audu Bulama ya tabbatarwa BBC.
Ya ce ''Matakai guda shida ne kundin tsarin mulki ya gindaya cewa sai an bi su kafin gwamna ko mataimakinsa ya tsigu a Najeriya,''
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masanin shari'ar ya yi bayanin matakan kamar haka:
Rubutacciyar sanarwa.
Kundin mulkin Najeriya ya ce dole a samu sa hannun aƙalla ɗaya bisa uku na ƴan majalisar dokokin jihar da suka rubuta takardar sanarwa cewa suna da zarge-zarge a kan gwamna, kuma su rubuta dalla-dalla cewa ga irin abubuwan da suke zargin gwamnan. Za su rubuta asikar tasu ne ga shugaban majalisar dokokin jihar, wanda shi kuma a cikin kwana bakwai doka ta yi tanadin lallai ya sanar da gwamna sammacin.
Zaɓe a majalisa.
Mataki na biyu shi ne inda majalisar za ta yi zama kuma dole sai an samu kashi byu bisa uku na jimillar ƴan majalisa da suka amince cewa sun yarda a binciki gwamna game da zargin da ake masa.
Rubutawa alƙalin alƙalai na jihar
Shugaban majalisa zai rubutawa alƙalin alƙalai na jihar cewa kashi biyu bisa uku na ƴan majalisa sun buƙaci a binciki gwamna kan wasu zarge-zarge domin haka yana neman alƙalin ya kafa abinda ake kira ''kwamitin mutum bakwai''. Kundin mulki ya fayyace cewa alƙalin alƙalan ne kawai zai iya kafa wannan kwamiti na mutum bakwai kuma kundin mulkin ya ƙayyade cewa lallai sai sun zamo nagartattun mutane, ba ƴan siyasa ba, ba ma'aikatan gwamnati ba kuma waɗanda basu goyon bayan kowanne ɓangare na dambarwar.
Bincken ƙwamiti.
Kundn mulki ya bai wa wannan kwamitin mutum bakwai wa'adin wata uku ya gudanar da bincikensa. Kuma a cikin binciken nasu dole ne a bai wa gwamna cikakkiyar dama ya kare kanshi.
Rubutawa majalisa.
Idan kwamitin ya gama aikin binciken, sai ya rubutawa majalisa cewa kodai ya samu gwamna da laifin da ake zarginsa da aikatawa ko kuma akasin hakan.
Zabe tsakanin ƴan majalisa.
Mataki na shida shi ne inda majalisa za ta kaɗa ƙuri'a domin amincewa da tsige gwamnan. Wannan kuma yana faruwa ne bayan kwamitin mutum bakwai ya tabbatar cewa ya samu gwamnan da laifi. Duk da haka majalisar za ta zaɓe domin samun rinjayen kashi biyu bisa uku kafin amincewa da tsige gwamnan. Idan kuma kwamitin mutum bakwai ya rubuto cewa bai samu gwamna da laifi ba, to majalisar ba zata kaɗa ƙuri'ar ƙarshe ta shige gwamnan ba.
Laifukan da ke janyo a tsige gwamna mai ci
Dangane da abubuwan da za su iya sanya majalisa ta tsige gwamna kuwa, Barista Aminu Abdulrashid, lauya mai zaman kansa a jihar Kadunan Najeriya ya ce kundin mulkin Najeriya ya gindaya sharuɗɗan yin hakan.
''Sashi na 188 na kundin mulkin 1999 ya bayar da damar cewa ƴan majalisa za su iya tsige gwamna idan aka same shi da aikata wasu manyan laifuka da ake kira "gross misconduct" wanda ke nufin aikata babban laifin da ya ci karo da tanadin doka, ko yi wa doka katsalandan ko kuma karya dokar jihar kai tsaye''
Gwamnonin da aka taɓa tsigewa a Najeriya
A baya dai an samu lokuta daban-daban da aka tsige gwamnonin jihohi a Najeriya kamar haka:
- Abdulkadir Balarabe Musa (Jihar Kaduna, 1981)
- Rashidi Ladoja (Jihar Oyo, 2006)
- Joshua Dariye (Jihar Plateau, 2006)
- Diepreye Alamieyeseigha (Bayelsa State, 2005)
- Ayo Fayose (Jihar Ekiti, 2006)
- Peter Obi (Jihar Anambra, 2006)
- Murtala Nyako (Jihar Adamawa, 2014)
Akwai kuma wasu gwamnonin da aka yi yunƙurin tsige su amma ba a cimma nasara ba kamar haka:
- Darius Ishaku (Taraba State, 2015)
- Samuel Ortom (Jihar Benue, 2018)










