KAI TSAYE, Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 05/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 5 ga watan Maris 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Iran ta kai wa jirgin dakon man Amurka hari

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya ce dakarun jiragen ruwan yaƙin ƙasar ta harbi wani jirgin ɗakon man Amurka a safiyar yau a arewacin Bahar Rum.

    Dakarun juyin juya halin Iran IRGC sun ce jirgin ya “sha harbi da makami mai linzami a arewacin Bahar Rum” kuma “har yanzu yana ci da wuta”, a wata sanarwa da aka karanta a talabijin na gwamnatin.

    IRGC ta ce tana da “cikakken iko” da Kogin Hormuz, wanda ke haɗa Bahar Rum da Tekun Indiya.

    Majiyoyi masu zaman kansu ba dai basu tabbatar da lamarin ba amma kuma ƙungiyar Kasuwancin Jiragen Ruwa ta Biritaniya MTO ta tabbatar da harin.

  2. Hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniyar Tehran

    Ga wasu hotuna da ke nuna yadda Hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniyar Tehran, babban birnin Iran.

    ...

    Asalin hoton, Wana / Reuters

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    ....

    Asalin hoton, AFP via Getty images

  3. Amurka ta bayyana sojojinta na biyar da na shida da Iran ta kashe

    ....

    Asalin hoton, US Army Reserve Command

    Bayanan hoto, Manjo Jeffrey O’Brien, soja na biyar da ya mutu a harin Iran

    Ma’aikatar tsaron Amurka, Pentagon, ta bayyana sunayen sojojinta na biyar da na shida da suka mutu a harin da Iran ta kai a ƙasar Kuwait a farkon rikicin da ke gudana.

    Ma'aikatar ta ce soja na biyar da aka tabbatar da mutuwarsa shi ne Manjo Jeffrey O’Brien, wanda ya fito daga garin Waukee wanda aka tura aiki a Kuwait a shekarar 2019.

    Soja na shida da ya mutu a harin shi ne Robert M Marzan mai shekaru 54, wanda ya fito daga Sacramento.

    Sojojin Amurka sun mutu ne bayan wani harin jirgi mara matuki da aka kai a wani cibiyar umarni ta sojoji a yankin Port Shuaiba a ranar Lahadi.

    Tun da farko rundunar sojin Amurka ta bayyana cewa sojojinta uku ne suka mutu a harin. Sai dai daga baya jami’ai suka tabbatar a ranar Litinin cewa adadin ya ƙaru, bayan wani soja ya mutu sakamakon raunukan da ya samu, sannan aka sake gano gawarwaki biyu a cikin ɓaraguzan ginin.

    A cewar Amurka, jimillar sojojinta shida ne suka mutu a wannan harin da ake zargin Iran ta kai.

  4. Majalisar dattijan Amurka ta goyi bayan Trump kan yaƙin Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar dattawan Amurka ta kada kuriar bayar da goyon baya ga matakin sojin da Shugaba Trump ya dauka kan Iran, inda kan 'yan majalisar ya rabu tsakanin 'yan jam'iyyarsa ta Republican da kuma 'yan hamayya na Democrat.

    Majalisar ta yi watsi da bukatar ƴan Democrat ta cewa lalle sai shugaban ya samu amincewar majalisun dokokin kasar kafin, kai duk wani hari.

    Yanzu hankali ya karkata zuwa ga majalisar wakilan kasar wadda ita ma za ta yi kuria a kan kudurin dokar a yau Alhamis.

    Masu goyon bayan shugaban sun kafe cewa yana yakin ne bisa ikon da doka ta ba shi. Da yake magana a fadarsa ta White House Shugaba Trump ya ce zuwa yanzu matakin sojin a kan Iran na nasara.

  5. Iran ta yi yunƙurin kashe Trump - Ma'aikatar tsaron Amurka

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma’aikatar tsaron Amurka ta ce Iran ta yi yunkurin kashe shugaban Amurka Donald Trump, inda ta kara da cewa sojojin Amurka sun kashe wani jami’in Iran ɗin da ake zargi da jagorantar shirya wannan yunkuri.

    Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ne ya sanar da hakan a yayin da yake magana da ‘yan jarida a hedkwatar ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon,

    Ya ce, “Iran ta so ta kashe Shugaba Trump, amma daga karshe Trump ne ya yi nasara.”

    A shekarar 2024 kuwa, gwamnatin Amurka ta gurfanar da wani dan asalin Afghanistan bisa zargin hannu a wani shiri da ake zargin Iran ta shirya na kashe Trump kafin ya fara aiki bayan nasararsa a zaɓen waccan shekarar.

    Tsohon babban lauyan gwamnatin Amurka Merrick Garland shima ya ce ma’aikatar shari’a ta tuhumi “wani mutum da ke aiki wa gwamnatin Iran wanda aka ɗora wa alhakin jagorantar masu aikata laifi domin aiwatar da shirin kashe wasu mutane, ciki har da Donald Trump.”

    Sai dai Iran ta musanta wadannan zarge-zargen.

    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya ce an taɓa irin wadannan zarge-zarge kan ƙoƙarin kashe shugabannin Amurka a baya, amma Iran ta ƙaryata su, yana mai cewa daga baya an gano cewa ba gaskiya ba ne.

  6. An ji ƙarar fashe-fashe a Doha bayan fara kwashe mutane kusa da ofishin Amurka

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni sun ce an ji ƙarar wasu fashe-fashe a birnin Doha, babban birnin ƙasar Qatar, kamar yadda wani ɗan jarida na kamfanin dillancin labaran AFP ya bayyana.

    Hakan na zuwa ne bayan hukumomin Qatar sun fara kwashe mutanen da ke zaune kusa da ofishin jakadancin Amurka da ke Doha a matsayin matakin kariya.

    Ma’aikatar cikin gida ta Qatar ta ce ana ɗaukar matakin ne na wucin gadi domin kare lafiyar jama’a, inda aka tanadi wuraren zama ga wadanda aka kwashe daga yankin.

    Rahotanni sun kuma ce a baya an ji ƙarar fashe-fashe a Doha yayin da Iran ke kai hare-hare a sassa daban-daban na yankin domin mayar da martani ga hare-haren da Isra'ila da Amurka suka kai mata.

    Wani makami mai linzami da Iran ta harba ya kuma faɗa a sansanin sojin Amurka na Al Udeid Air Base, wanda yake kimanin kilomita 40 daga Doha.

    Rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila da Amurka ya ci gaba da tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya, inda kowace ƙasa ke kai hare-hare ko mayar da martani, lamarin da ya kara dagula tsaro a ƙasashe da dama na yankin.

  7. Iran ta kai hari da makamai masu linzami kan Isra’ila - Sojoji

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Isra’ila sun ce ƙasar Iran ta harba wasu makamai masu linzami zuwa Isra’ila a safiyar yau, Alhamis.

    Rahotanni sun nuna cewa an ga hasken wutar makaman a sararin samaniyar birnin Tel Aviv a lokacin da Iran ta kai harin.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa babu rahoton mutuwa ko waɗanda suka jikkata nan take, kamar yadda hukumar agajin gaggawa ta Isra’ila ta bayyana.

    An kuma fitar da gargaɗi sau uku cikin awanni biyu, inda ‘yan jarida na AFP suka ce sun ji ƙarar fashewa a birnin Birnin Ƙudus.

    Sojojin Isra’ila sun sanar da cewa mutane na iya barin wuraren mafaka da aka tanada domin kariya.

  8. Ko hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan Iran sun halasta?

    ....

    Asalin hoton, Amirhossein Khorgooei/ISNA/West Asia News Agency via Reuters

    Hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai kan Iran, da kuma martanin da Iran ta mayar sum yi sanadin mutuwar fararen hula.

    Majalisar Dinkin Duniya, ta bakin shugabanta António Guterres ta yi Allah-wadai da hare-haren, tare da kiran a tsagaita wuta da kuma mutunta dokokin ƙasa da ƙasa.

    Dukkanin ɓangarorin biyu na iƙirarin cewa a kan daidai suke, amma kuma ba za a iya tabbatar da hakan ba sai an bincika dokokin da kasashen duniya suka amince da su bayan yaƙin duniya na biyu.

    Jin kaɗan bayan da Amurka da Isra'ila suka harba bama-bamai a Iran a ranar 28 ga watan Fabaraiu, shugaba Donald Trump ya zargi Tehran da yunkurin ƙera makaman nukiliya, wanda hakan barazana ce ga ƙawayenta.

    Sai dai sakataren Amurka Marco Rubio ya ce ya zama wajibi Amurka ta ragargaji Iran saboda tana da masaniyar cewa Isra'ila za ta kai hari ƙasar.

  9. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.